Hadisai

Ku dinga aikata aikin da zaku iya, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa har sai kun ƙosa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنين رَضيَ اللهُ عنها زَوْجَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَنَّ الْحَوْلَاءَ بِنْتَ تُوَيْتِ بْنِ حَبِيبِ بْنِ أَسَدِ بْنِ عَبْدِ الْعُزَّى مَرَّتْ بِهَا وَعِنْدَهَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقُلْتُ: هَذِهِ الْحَوْلَاءُ بِنْتُ تُوَيْتٍ، وَزَعَمُوا أَنَّهَا لَا تَنَامُ اللَّيْلَ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَنَامُ اللَّيْلَ! خُذُوا مِنَ الْعَمَلِ مَا تُطِيقُونَ، فَوَاللهِ لَا يَسْأَمُ اللهُ حَتَّى تَسْأَمُوا».

Fassara

Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Lallai cewa Haula'a Bint Tuwait Ibnu Habib Ibnu Asad Ibnu Abdul'uzza ta wuceta alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana wurinta, sai na ce: Wannan Haula'u ce Bnit Tuwait, kuma sun yi da'awar cewa bata baccin dare, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Bata baccin dare! Ku dinga aikata aikin da zaku iya, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa har sai kun ƙosa».

Sharhi

Haula'u Bnt Tuwait - Allah Ya yarda da ita - ta kasance a wurin uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -, lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo gurinta (Nana A'isha), sai (Haula'u) ta fita ta barta Sai Nana A'isha ta ce masa: Wannan matar bata baccin dare, kai tana raya shi da sallah. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce yana mai tsananin yi mata inkari: Bata baccin dare! ku shagalta da aiki na gari wanda zaku iya dawwama a kansa, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa akan baiwa bayinSa salihai masu biyayya lada da sakamako akan biyayyarsu da kuma kyawawan ayyukansu da kuma ayyukansu na gari har sai sun ƙosa sun bar aikin.

Fa'idoji

  • Yawaita ibada sama da yadda jiki zai iya, yana kaiwa zuwa ga ƙosawa da kuma yankewa sai zuciya ta daina yin aikin.
  • Daidaituwa da tsakatsaki a cikin yin ibada hakan yana sawa a ci gaba da ibadar da kuma tabbata a kanta.
  • Kanƙanin aiki da aka dawwama ana yi ya fi alheri akan aiki mai yawa mai sa a yanke aikin.
  • Nawawi ya ce: Ta hanyar dawwama da aiki kaɗan ɗa'a tana zarcewa da zikiri da muraƙaba da ikhlasi da kuma fuskanta ga Allah, saɓanin aiki mai yawa mai wahalarwa har aiki ɗan kaɗan ya ƙaru ta inda zai fi mai yawa wanda aka daina da lada mai yawa.
Sharhi: العربية

كانت عند أم المؤمنين عائشة رضي الله عنها الحولاء بنت تويت رضي الله عنها، فخرجت منها مع دخول النبي صلى الله عليه وسلم عليها. فقالت عائشة له: هذه المرأة لا تنام الليل بل تحييه بالصلاة. فقال صلى الله عليه وسلم مستنكرًا تشديدها على نفسها: لا تنام الليل! اشتغلوا من الأعمال الصالحة بما تستطيعون المداومة عليه، فوالله لا يسأم الله من إعطاء عباده الصالحين المطيعين الثواب والجزاء على طاعاتهم وحسناتهم وأعمالهم الصالحة حتى يسأموا ويتركوا من العمل.

  • الإكثار من العبادة فوق ما يطيق الجسد يؤدي إلى الملل والفتور فتترك النفس.
  • الاعتدال والتوسط في أداء العبادة مدعاة لاستمرارها والثبات عليها.
  • العمل القليل الدائم خير من الكثير المنقطع.
  • قال النووي: بدوام القليل تستمر الطاعة بالذكر والمراقبة والإخلاص والإقبال على الله، بخلاف الكثير الشاق حتى ينمو القليل الدائم بحيث يزيد على الكثير المنقطع أضعافًا كثيرة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari