Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي بُرْدَةَ الْأَنْصَارِيِّ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «لَا يُجْلَدُ أَحَدٌ فَوْقَ عَشَرَةِ أَسْوَاطٍ إِلَّا فِي حَدٍّ مِنْ حُدُودِ اللهِ».
Fassara
Daga Abu Burda - al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Ba'a yi wa wani mutum bulala sama da goma sai a haddi daga cikin haddodin Allah"
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani a yi wa wani bulala sama da bulala goma sai dai a cikin saɓo, ba wai ana nufin cewa abinda ya zo a cikinsa na iyakance adadi daga mai shara'antawa na bulala ko duka ko uƙuba keɓantacciya ba, abin nufi ba'a yin ƙari a cikin bulalar ladabtarwa akan bulala goma, kamar yi wa mata bulala ko ɗa.
Fa'idoji
- Dokokin Allah - Maɗaukakin sarki - waɗanda Ya yi umarni da su ko kuma ya yi hani daga barinsu suna da uƙubobi waɗanda suke tsawatarwa daga gare su, kodai ababen ƙaddarawa ne daga mai shara'antawa, ko kuma a koma zuwa ga maslahar da shugaba yake ganin ta dace a cikin ƙaddarawarsu.
- Ladabtarwa tana kasancewa mai sauƙi gwargwadan fadakarwa da kuma tsoratarwa, saboda haka ba'a ƙari a cikinsa akan bulala goma idan an buƙatu ga hakan, abinda ya fi ladabtar da su ba tare da duka ba, kai da nusarwa, da kuma koyarwa, da shiryarwa, da kwaɗaitarwa, to ya fi sa karɓuwa da kuma sassautawa a cikin koyarwa, halaye a wannan matsayar suna saɓawa da yawa, to yana kamata a aikata abinda ya fi maslaha.
Sharhi: العربية
نهى النبيُّ صلى الله عليه وسلم أن يجلد أحد أكثر من عشرة أسواط إلا في المعاصي، وليس المراد ما ورد فيه من الشارع عدد محدد من الجلد أو الضرب أو العقوبة المخصوصة، والمراد لا يُزاد في ضرب التأديب على عشرة أسواط، كجلد الزوجة والابن.
- حدود الله تعالى التي أمر بها أو نهى عنها لها عقوبات تردع عنها، إما مقدرة من الشارع، أو راجعة في تقديرها إلى المصلحة التي يراها الحاكم.
- التأديب يكون خفيفًا بقدر التوجيه والتخويف، فلا يزاد فيه على عشرة أسواط إن احتيج لذلك، والأولى تأديبهم بدون الضرب، بل بالتوجيه، والتعليم، والإرشاد، والتشويق، فهو أدعى للقبول واللطف في التعليم، والأحوال في هذا المقام تختلف كثيرًا، فينبغي فعل الأصلح.