Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بن مسعودٍ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إِنَّ مِنْ شِرَارِ النَّاسِ مَنْ تُدْرِكُهُ السَّاعَةُ وَهُمْ أَحْيَاءٌ، وَمَنْ يَتَّخِذُ الْقُبُورَ مَسَاجِدَ».
Fassara
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Lallai cewa yana daga mafi sharrin mutane wadanda alkiyama zata riske su alhali suna raye, da wanda yake rikon kaburbura masallatai".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da mafi sharrin mutane, cewa sune wadanda alkiyama zata tsaya akansu alhali su suna raye, da wadanda suke daukar kaburbura masallatai, suna sallah a wurinsu suna kuma kallonsu..
Fa'idoji
- Haramcin gina masallatai akan kaburbura; domin hakan hanyace zuwa ga shirka.
- Haramcin sallah a wurin kaburbura koda ba tare da gini ba; domin masallaci suna ne ga abinda ake sujjada a cikinsa koda babu gini a wurin.
- Wanda ya riki kaburburan salihai masallatai dan yin sallah a wurin to shi yana daga mafi sharrin mutane, koda ya yi ikirarin cewa manufarsa neman kusanci zuwa ga Allah - Madaukakin sarki -.
Sharhi: العربية
يُخْبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم عن شِرَار الناس، وأنهم مَن تقومُ الساعةُ عليهم وهم أحياءٌ، والذين يتَّخذون القبور مساجد، يُصَلُّون عندها وإليها.
- تحريم بناء المساجد على القبور؛ لأنه وسيلةٌ إلى الشرك.
- تحريم الصلاة عند القبور ولو بدون بناء؛ لأن المسجد اسم لما يسجد فيه ولو لم يكن فيه بناء.
- مَن اتخذ قبورَ الصالحين مساجدَ للصلاة فيها فهو من شرار الخلق، وإنْ زعم أنَّ قصدَه التقرُّبُ إلى الله تعالى.