Hadisai

Sai muka ce: Kai ne shugabanmu, sai ya ce: "Shugaba Shi ne Allah", muka ce: Mafificinmu a fifiko, kuma mafi girmanmu a kyauta, sai ya ce: "Ku fadi maganarku, ko wani bangare na maganarku, kada Shaidan ya yi amfani daku

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAbu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma Ahmad

Rubutun Larabci

عَن عَبدِ الله بنِ الشِّخِّير رضي الله عنه قَالَ: انْطَلَقْتُ في وَفدِ بَنِي عَامِرٍ إِلى رَسُولِ الله صلى الله عليه وسلم، فَقُلنا: أَنتَ سيّدُنَا، فقال: «السَّيدُ اللهُ»، قُلنا: وَأَفْضَلُنا فَضْلاً، وأعظَمُنا طَوْلاً، فقال: «قُولُوا بِقَولِكُم، أَو بَعضِ قولِكُم، وَلَا يَسْتَجْرِيَنَّكُم الشَّيطَانُ».

Fassara

Daga Abdullahi Dan Shikkhir - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Na tafi a cikin jama'ar Banu Amir zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Sai muka ce: Kai ne shugabanmu, sai ya ce: "Shugaba Shi ne Allah", muka ce: Mafificinmu a fifiko, kuma mafi girmanmu a kyauta, sai ya ce: "Ku fadi maganarku, ko wani bangare na maganarku, kada Shaidan ya yi amfani daku".

Sharhi

Wasu jama'a suka zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da suka iso wurinsa sai suka fadi - suna masu yabonsa - wasu daga cikin kalmomin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ki su, sai suka ce ; "Kai ne shugabanmu", sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Shugaba (Shi ne) Allah" Cikakken shugabanci nasa ne akan halittarSa su bayinSa ne. Suka ce : Kai ne "Mafificinmu a fifiko" kuma mafi daukakarmu a daraja da daukaka. kuma kaine "Mafi girmanmu a kyauta" mafi yawaitawarmu a kyauta da daukaka da daraja. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nuna musu su fadi maganarsu ta al'ada kada su kallafawa kansu lafazai, kuma kada Shaidan ya Ja su zuwa wuce gona da iri da kanbawar da zata afkar cikin abinda aka haramta na shirka da hanyoyinta.

Fa'idoji

  • Girman darajar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a rayukan sahabbansa da girmamawarsu gare shi .
  • Hani daga matsama kai a lafazi, da takaituwa a magana.
  • Kariya ga Tauhidi daga abinda zai bata shi na maganganu da ayyuka.
  • Hani daga wuce gona da iri a yabo, shi yana daga hanyoyin Shaidan,
  • Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne shugaban 'ya'yan Adam, abinda ya zo a hadisi shi yana babin kankar da kai ne, kuma a babin tsoro garesu kar su fada a wuce iyaka.
Sharhi: العربية

جاءَ جماعةٌ إلى النبيِّ صلى الله عليه وسلم، فلمّا وَصَلَوا إليه قالوا -مَادِحِين له- بعضَ الكلمات التي كَرِهَها صلى الله عليه وسلم، فقالوا: "أنت سيدُنا"، فقال لهم صلى الله عليه وسلم: "السيدُ الله" فله السُّؤْدَدُ التامُّ على خلقِهِ وهم عبيدُهُ. وقالوا: أنت "أَفْضَلُنا فَضْلًا" وأعلانا رُتبةً وشرفًا ومزيةً. وأنت "أعظَمُنا طَوْلًا" وأكثرنا عطاءً وعُلوًّا ورفعةً. ثم أرشدَهم النبيُّ صلى الله عليه وسلم أن يقولوا قولهم المعتاد ولا يتكلَّفوا الألفاظ، وألَّا يَجُرَّهم الشيطان إلى الغلو والإطراء الذي يُوقِع فيما حُرِّم من الشرك ووسائله.

  • عظم قدر النبي صلى الله عليه وسلم في نفوس أصحابه واحترامهم له.
  • النهي عن التكلّف في الألفاظ، والاقتصاد في المقال.
  • حماية التوحيد عما يُخِلُّ به من الأقوال والأعمال.
  • النهي عن الغلو في المدح، فهو من مداخل الشيطان.
  • النبي صلى الله عليه وسلم هو سيِّدُ ولد آدم، وما جاء في الحديث هو من باب التواضع، ومن باب الخوف عليهم أن يغلو فيه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari