Hadisai

Wani mutum ya kasance nesa da masallaci sama da kowa a iya sanina, kuma ya kasance ba wata sallah da take wuce shi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أُبَيِّ بْنِ كَعْبٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: كَانَ رَجُلٌ لَا أَعْلَمُ رَجُلًا أَبْعَدَ مِنَ الْمَسْجِدِ مِنْهُ، وَكَانَ لَا تُخْطِئُهُ صَلَاةٌ، قَالَ: فَقِيلَ لَهُ: أَوْ قُلْتُ لَهُ: لَوْ اشْتَرَيْتَ حِمَارًا تَرْكَبُهُ فِي الظَّلْمَاءِ، وَفِي الرَّمْضَاءِ، قَالَ: مَا يَسُرُّنِي أَنَّ مَنْزِلِي إِلَى جَنْبِ الْمَسْجِدِ، إِنِّي أُرِيدُ أَنْ يُكْتَبَ لِي مَمْشَايَ إِلَى الْمَسْجِدِ، وَرُجُوعِي إِذَا رَجَعْتُ إِلَى أَهْلِي، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «قَدْ جَمَعَ اللهُ لَكَ ذَلِكَ كُلَّهُ».

Fassara

Daga Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya kasance nesa da masallaci sama da kowa a iya sanina, kuma ya kasance ba wata sallah da take wuce shi, ya ce: Sai aka ce masa: Ko nace masa: Ai da za ka sayi jakin da zaka dinga hawan shi cikin duhu, da zafin rana, sai ya ce; Ba na son gidana ya kasance a gefen masallaci, lallai ni ina son a rubuta mini tafiya ta zuwa masallaci, da dawowa ta idan na dawo zuwa iyalaina, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: «‌Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka wadannan gaba ɗayan su».

Sharhi

Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa wani mutum daga cikin mutanen Madina yana daga cikin mafi nisan gida daga masallacin Annabi, kuma ya kasance sallah bata wuce shi; kai yana halattar kowace sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai aka ce masa: Inama dai a ce zaka sayi jakin da zaka dinga hawansa a cikin duhun dare da kuma cikin zafin ƙasa a cikin rana, ya ce: Bana son a ce gidana yana gefen masallaci, lallai ni ina son Allah Ya rubuta mini tafiyata zuwa masallaci, da kuma dawowata idan na dawo zuwa ga iyalaina, sai maganarsa ta kai wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: «‌Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka hakan baki ɗayansu».

Fa'idoji

  • Tsananin kwaɗayin sahabbai akan alheri da neman ƙaruwar shi da kuma neman lada.
  • Nawawi ya ce: A cikinsa akwai tabbatar da lada a cikin takun dawowa daga sallah kamar yadda yake tabbata a tafiya.
  • Musulmi su yi wa junansu wasiyya da alheri da kuma nasiha da aikin alheri, wanda ya ga cewa ɗan'uwansa wata wahala tana riskarsa to ya gabatar masa da nasiha a gusar da ita.
  • Nisan gida daga masallaci ba uzuri ba ne a kan barin jam’i, muddin dai yana jin kiran sallah.
Sharhi: العربية

أخبر أبي بن كعب رضي الله عنه أن رجلًا من الأنصار من أبعد الناس دارًا من المسجد النبوي، وكان لا تفوته صلاة؛ بل يحضر كل صلاة مع النبي صلى الله عليه وسلم، فقيل له: لو اشتريت حمارًا تركبه في ظلماء الليل، وفي حر الأرض في النهار، قال: ما يسرني أن منزلي إلى جنب المسجد، إني أريد أن يكتب الله لي ممشاي إلى الصلاة في المسجد، ورجوعي إذا رجعت إلى أهلي، فوصل كلامه إلى النبي صلى الله عليه وسلم فقال: «قد جمع الله لك ذلك كله».

  • شدة حرص الصحابة على الخير والازدياد منه وكسب الأجر.
  • قال النووي: فيه إثبات الثواب في الخُطا في الرجوع من الصلاة كما يثبت في الذهاب.
  • تواصي المسلمين بالخير والتناصح بالبر، فمن رأى أن أخاه تلحقه مشقة فليقدم له النصح في إزالتها.
  • بُعد الدار عن المسجد ليس عذرًا في ترك الجماعة، ما دام يسمع النداء.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari