Hadisai

Mafificin yinin da rana ta ɓullo a cikinsa yinin Juma'a

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «خَيْرُ يَوْمٍ طَلَعَتْ عَلَيْهِ الشَّمْسُ يَوْمُ الْجُمُعَةِ، فِيهِ خُلِقَ آدَمُ، وَفِيهِ أُدْخِلَ الْجَنَّةَ، وَفِيهِ أُخْرِجَ مِنْهَا، وَلَا تَقُومُ السَّاعَةُ إِلَّا فِي يَوْمِ الْجُمُعَةِ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafificin yinin da rana ta ɓullo a cikinsa yinin Juma'a, a cikinsa ne aka halicci (Annabi) Adam, kuma a cikinsa ne aka shigar da shi aljanna, kuma a cikinsa ne aka fitar da shi daga gareta, kuma AlKiyama ba za ta tsayaba sai a ranar Juma'a".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mafificin yinin da rana ta ɓullo a ciknsa shi ne yinin Juma'a. Daga abinda (ginin Juma’a) ya keɓa ta da shi: Allah Ya halicci (Annabi) Adam - aminci ya tabbata agare shi - a cikinsa, a cikinsa ne aka shigar da shi aljanna, a cikinsa ne aka fitar da shi daga aljannar, kuma aka sakko da shi ƙasa, Alkiyama ba za ta tashiba sai a yinin Juma'a.

Fa'idoji

  • Falalar ranar Juma'a akan sauran kwanukan mako.
  • Kwaɗaitarwa akan yawaita ayyuka na gari a cikin ranar Juma'a, da yin tanadi dan samun rahamar Allah - Maɗaukakin sarki -, da tunkuɗe azabarsa.
  • Waɗannan keɓantattun abubuwan na ranar Juma'a da aka ambace su a cikin Hadisin, wasu malam sun ce: Su ba dan ambatan falalar ranar Juma'a ba ne; domin fitar da (Annabi) Adam da tashin Alkiyama ba'a ɗaukarsu falala. Wasu malaman su ka ce: Kai dukkaninsu falala ce, kuma fitar (Annabi) Adam sababin samun zuriya ne kamar manzanni da annabawa da salihai, tsayuwar Alkiyama kuwa sababin gaggauto da sakamakon salihai ne da samun su ga abinda Allah Ya tanadar musu na karamomi.
  • An ambaci wasu keɓantattun abubuwa daban ga ranar Juma'a, banda abinda aka ambata a cikin wannan riwayar, daga cikinsu: A cikinta ne aka karɓi tuban (Annabi) Adam, kuma acikinta ne aka ɗauki ransa, kuma aciknta akwai wani (Takaitaccen) lokaci bawa mumini ba zai dace da shi ba yana sallah (Addu’a) yana roƙon Allah wani abu ba sai Ya amsa masa.
  • Mafificin yini a shekara ranar Arfa, (wasu malaman) suka ce: Ranar babbar sallah, kuma mafificin kwanukan mako ranar Juma'a, mafificin darare kuma daren Lailatul Kadr.
Sharhi: العربية

يُخبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ خيْرَ يومٍ طلعت عليه الشمس يومُ الجمعة، ومن خصائصه: أن الله خلق فيه آدم عليه السلام، وفيه أدخله الجنة، وفيه أخرجه منها وأهبطه إلى الأرض، ولا تقوم الساعة إلا في يوم الجمعة.

  • فضل يوم الجمعة على سائر أيام الأسبوع.
  • الحث والإكثار من الأعمال الصالحة في يوم الجمعة، والتأهب لنيل رحمة الله تعالى، ودفع نقمته.
  • هذه الخصائص ليوم الجمعة التي ذكرت في الحديث قيل: أنها ليست لذكر فضيلة يوم الجمعة؛ لأن إخراج آدم وقيام الساعة لا يعد فضيلة، وقيل: بل جميعها فضائل وخروج آدم سبب وجود الذرية من الرسل والأنبياء والصالحين، وقيام الساعة سبب تعجيل جزاء الصالحين ونيلهم ما أعد الله لهم من الكرامات.
  • ذُكِرَ ليوم الجمعة خصائص أخرى غير ما ذكر في هذه الرواية، ومنها: فيه تِيْبَ على آدم، وفيه قُبض، وفيه ساعة لا يصادفها عبد مؤمن وهو يصلي يسأل الله شيئًا إلا أعطاه إياه.
  • أفضل أيام السنة يوم عرفة، وقيل: يوم النحر، وأفضل أيام الأسبوع يوم الجمعة، وأفضل ليلة ليلة القدر.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari