Hadisai

Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - har sai ya sanya kiyayewarSa, sai Ya tabbatar masa da zunubansa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ صَفْوَانَ بْنِ مُحْرِزٍ قَالَ: قَالَ رَجُلٌ لِابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما كَيْفَ سَمِعْتَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ: فِي النَّجْوَى؟ قَالَ: سَمِعْتُهُ يَقُولُ: «يُدْنَى الْمُؤْمِنُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مِنْ رَبِّهِ عَزَّ وَجَلَّ، حَتَّى يَضَعَ عَلَيْهِ كَنَفَهُ، فَيُقَرِّرُهُ بِذُنُوبِهِ، فَيَقُولُ: هَلْ تَعْرِفُ؟ فَيَقُولُ: أَيْ رَبِّ أَعْرِفُ، قَالَ: فَإِنِّي قَدْ سَتَرْتُهَا عَلَيْكَ فِي الدُّنْيَا، وَإِنِّي أَغْفِرُهَا لَكَ الْيَوْمَ، فَيُعْطَى صَحِيفَةَ حَسَنَاتِهِ، وَأَمَّا الْكُفَّارُ وَالْمُنَافِقُونَ، فَيُنَادَى بِهِمْ عَلَى رؤُوسِ الْخَلَائِقِ هَؤُلَاءِ الَّذِينَ كَذَبُوا عَلَى اللهِ».

Fassara

Daga Safwan ɗan Muhriz ya ce: Wani mutum ya ce wa Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - yaya ka ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: A (sha'anin) sirri? ya ce: Na ji shi yana cewa: "Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - har sai ya sanya kiyayewarSa, sai Ya tabbatar masa da zunubansa, sai Ya ce: Shin kana sane ? sai ya ce: Eh ya Ubangiji ina sani, ya ce: Lallai cewa Ni haƙiƙa Na suturtasu gareka a duniya, kuma cewa lallai Ni Zan gafarta maka su a yau, sai a ba shi takardar kyawawan ayyukansa, amma kafirai da munafukai, sai a kirasu akan kawunan halittu waɗannan sune waɗanda suka yi wa Allah ƙarya".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da ganawar Allah ga bawanSa mumini ranar alƙiyama, sai ya ce: Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa sai Ya sanya suturarSa daga ma'abota wurin tsayuwa har ya zama waninsa ba zai yi tsinkaye akan sirrinsa ba, sai ya ce masa: Shin kana sanin zunubi kaza da kaza... Zai tabbatar masa da zunuban da suke tsakanin bawa da UbangijinSa. Sai ya ce: Na'am Eh, ya Ubangiji. Har idan mumini ya firgita ya ji tsoro, sai Tsarki ya tabbatar maSa Ya ce masa: Lallai cewa Ni na suturta su gareka a duniya, kuma cewa Ni na gafartasu gareka a yau, sai a ba shi takardar kyawawan ayyukansa. Amma kafiri da munafuki sai a yi kira a gabn mahalarta: Waɗannan sune waɗanda suka yi wa Ubangijinsu ƙarya, ku saurara tsinuwar Allah ta tabbata akan azzalumai.

Fa'idoji

  • Falalar Allah da rahamarSa ga muminai saboda rufa musu asiri a duniya da lahira.
  • Kwaɗaitarwa akan rufawa mumini asiri gwargwadan iko.
  • Ayyukan bayi gaba ɗayansu Ubangijin bayi Zai kiyayesu, wanda ya samu alheri to ya godewa Allah, wanda ya samu wanin haka to kada ya zargi kowa sai kansa, kuma shi yana ƙarƙashin Mashi'ar Allah.
  • Ibnu Hajar ya ce: Dukkan hadisan sun yi nuni akan cewa masu saɓo cikin muminai a alƙiyama sun kasu gida biyu: Na ɗayansu: Wanda saɓonsa tsakaninsa da Ubanginjinsa ne, sai hadisin Ibnu Umar ya yi nuni akan cewa wannan ɓangaren ya kasu gida biyu: Wani ɓangaren: Saɓonsu zai zama abin suturtawa a duniya, to wannan wanda Allah Zai yi masa sutura ne a alƙiyama shi a mafurtar (hadisn). Wani ɓangaren kuma: Saɓonsu zai zama a bayyane, sai mafhum ɗin sa ya yi nuni akan cewa shi saɓanin haka ne. Bangare na biyu: Wanda saɓonsa tsakanin sa da bayi ne to su sun kasu kashi biyu kuma: Wani ɓangaren: Mummunan ayyukansu sun rinjayi kyawan ayyukansu, to wadannan zasu fada cikin wuta sannan su fita da ceto, wani bangaren kuma: Munanan ayyukansu zasu yi daidai da kyawawan ayyukansu, to wadannan ba zasu shiga aljanna ba har sai sakayya ta faru tsakaninsu.
Sharhi: العربية

أَخْبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم عن مناجاة الله لعبدِه المؤمن يوم القيامة، فقال: يُدْنَى المؤمنُ يوم القيامة من ربه فيضع عليه سِتْرَه عن أهل الموقف حتى لا يَطَّلع على سرِّه غيرُه، فيقول له: أتعرف ذنب كذا وكذا... يُقرِّرُه بالذنوب التي بين العبد وربه. فيقول: نعم أي رب. حتى إذا فَزِع المؤمن وخاف، قال له سبحانه: إني سترتها عليك في الدنيا، وأنا أغفرها لك اليوم، فيُعطى صحيفة حسناته. وأما الكافر والمنافق فيُنادى على رؤوس الأشهاد: هؤلاء الذين كذبوا على ربهم، ألا لعنة الله على الظالمين.

  • فضل الله ورحمته للمؤمنين بسترهم في الدنيا والآخرة.
  • الحث على ستر المؤمن ما أمكن.
  • أعمال العباد كلها يُحصيها رب العباد، فمن وجد خيرًا فليحمد الله، ومن وجد غير ذلك فلا يلومنَّ إلا نفسه وهو تحت مشيئة الله.
  • قال ابن حجر: دلَّ مجموع الأحاديث على أن العصاة من المؤمنين في القيامة على قسمين: أحدهما: من معصيته بينه وبين ربه، فدل حديث ابن عمر على أن هذا القسم على قسمين: قسم: تكون معصيته مستورة في الدنيا، فهذا الذي يسترها الله عليه في القيامة وهو بالمنطوق، وقسم: تكون معصيته مجاهرة، فدل مفهومه على أنه بخلاف ذلك، والقسم الثاني: من تكون معصيته بينه وبين العباد فهم على قسمين أيضا: قسم: ترجح سيئاتهم على حسناتهم، فهؤلاء يقعون في النار ثم يخرجون بالشفاعة، وقسم: تتساوى سيئاتهم وحسناتهم، فهؤلاء لا يدخلون الجنة حتى يقع بينهم التَّقَاصُّ.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari