Hadisai

Jinin mutum musulmi ba ya halatta sai da ɗaya daga cikin abubuwa uku

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ ابنِ مَسعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا يَحِلُّ دَمُ امْرِئٍ مُسْلِمٍ إِلَّا بِإِحْدَى ثَلَاثٍ: الثَّيِّبُ الزَّانِي، وَالنَّفْسُ بِالنَّفْسِ، وَالتَّارِكُ لِدِينِهِ المُفَارِقُ لِلْجَمَاعَةِ».

Fassara

Daga Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Jinin mutum musulmi ba ya halatta sai da ɗaya daga cikin abubuwa uku, bazawarin da ya yi zina, da ran (da ya kashe) rai, da wanda ya bar addininsa wanda ya bar jama'a».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa jinin musulmi haramun ne, sai dai idan ya aikata ɗaya daga cikin ɗabi'un nan uku: Na farko: Wanda ya faɗa cikin alfashar zina, alhali ya riga ya yi aure da ƙulla ingantaccen ɗaurin aure, to sai kashe shi ta hanyar jifa ya halatta. Na biyu: Wanda ya kashe tsararren rai da aka hana kashewa ba tare da wani haƙƙi ba, to sai a kashe shi da sharuɗɗansa. Na uku: Wanda ya fita daga cikin jama'ar muslmai; ko dai ta hanyar barin addininsa gabaɗayansa ta hanyar yin ridda, ko wanda ya bari ba tare da ridda ba ta hanyar barin sashinsa kamar 'yan tawaye, da 'yan fashi, da mayaƙa cikin Khwarij da wasunsu.

Fa'idoji

  • Haramcin aikata waɗannan ɗabi'un uku, kuma wanda ya aikata ɗaya daga cikinsu ya cancanci uƙubar kisa; ko dai kafirci, shi ne yin ridda daga Musulunci, ko kuma haddi, sune: Bazawarin da ya yi zina, da wanda ya yi kisa da gangan.
  • Wajabcin kiyaye mutunci da kuma tsarkake shi .
  • Wajabcin girmama musulmi, kuma jininsa a tsare yake.
  • Kwaɗaitarwa akan lazimtar jama'ar musulmai da kuma rashin rabuwa da su.
  • Kyakkyawan koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda wani lokaci zancensa yake zuwa da rarrabewa; domin rarrabewar tana taƙaita mas'aloli kuma tana tattarosu, kuma shi ne mafi saurin haddacewa.
  • Allah Ya shara'anta haddodi; dan tsawatar da masu laifi, da kuma kare zamantakewa da kiyayewa daga manyan laifuka.
  • zartar da waɗannan hukunce hukuncen ya rataya ne akan shugaba ne kadai.
  • Dalilan dake sa a yi kisa sun fi uku, sai dai basa fita daga wadannan ukun, Ibnul Arabi al-Maliki ya ce: Ba sa fita daga waɗanannan ukun ta kowane irin hali, domin duk wanda ya yi asiri, ko ya zagi Annabin Allah to ya kafirta, shi ya shiga cikin wanda ya bar addininsa.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ دمَ المسلم حرام، إلا إنْ فعل واحدة من خصال ثلاث: الأولى: مَن وقع في فاحشة الزنا، وقد تزوج بعقد صحيح؛ فيحل قتله بالرجم. الثانية: من قَتل نفسًا معصومة عمدًا بغير حق، قُتل بشروطه. الثالثة: الخارج عن جماعة المسلمين؛ إما بترك دينه الإسلام كله بالردة، أو المفارق بغير ردة بترك بعضه كأهل البغي، وقطاع الطريق، والمحاربين من الخوارج وغيرهم.

  • تحريم فعل هذه الخصال الثلاث، وأن من فعل واحدة منها استحق عقوبة القتل: إما كفرًا، وهو المرتد عن الإسلام، وإما حدًّا، وهما: الثيب الزاني، والقاتل عمدًا.
  • وجوب حفظ الأعراض ونقائها.
  • وجوب احترام المسلم، وأنه معصوم الدم.
  • الحث على التزام جماعة المسلمين وعدم مفارقتهم.
  • حسن تعليم النبي صلى الله عليه وسلم حيث يَرِدُ كلامُه أحيانًا بالتقسيم؛ لأن التقسيم يحصر المسائل ويجمعها وهو أسرع حفظًا.
  • شرع الله الحدودَ؛ لردع الجناة، ولحماية المجتمع ووقايتِه من الجرائم.
  • تطبيق هذه الحدود هو من اختصاص ولي الأمر.
  • أسباب القتل أكثر من ثلاثة، ولكنها لا تخرج عنها، قال ابن العربي المالكي: ولا تخرج عن هذه الثلاثة بحال، فإنَّ مَن سَحَرَ أو سب نبيَّ الله كفر، فهو داخل في التارك لدينه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari