Hadisai

‌Duk wanda ya zama yana da wani abin da ya zalinci ɗan uwansa da shi na mutuncinsa ne ko wani abu to ya yi ƙoƙarin warwarewa daga gare shi a yau, tun kafin lokacin da babu dinari ko dirhami

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ كَانَتْ لَهُ مَظْلَمَةٌ لِأَخِيهِ مِنْ عِرْضِهِ أَوْ شَيْءٍ فَلْيَتَحَلَّلْهُ مِنْهُ اليَوْمَ، قَبْلَ أَلا يَكُونَ دِينَارٌ وَلاَ دِرْهَمٌ، إِنْ كَانَ لَهُ عَمَلٌ صَالِحٌ أُخِذَ مِنْهُ بِقَدْرِ مَظْلَمَتِهِ، وَإِلَمْ تَكُنْ لَهُ حَسَنَاتٌ أُخِذَ مِنْ سَيِّئَاتِ صَاحِبِهِ فَحُمِلَ عَلَيْهِ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Duk wanda ya zama yana da wani abin da ya zalinci ɗan uwansa da shi na mutuncinsa ne ko wani abu to ya yi ƙoƙarin warwarewa daga gare shi a yau, tun kafin lokacin da babu dinari ko dirhami, idan yana da wani aiki na gari za'a ɗauka daga cikin shi gwargwadan zalincinsa, idan ba shi da wasu kyawawan ayyuka za'a ɗauka daga munanan ayyukan ɗan'uwansa (da ya zalinta) sai a jibga masa su».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci dukkan wanda ya aikata wani zalinci ga ɗan'uwansa musulmi a mutunci ne, ko dukiya, ko jini ya nemi wanda ya zalinta ya yafe masa tunda yana duniya, tun kafin ranar lahira ta zo, inda dinari ko dirhami ba za su yi amfani ba ga wanda ya baiwa wanda ya zalinta ba, dan ya fanshi kansa da shi ba; domin sakayya a wannan ranar da kyawawan ayyuka ne da kuma munana. Inda wanda aka zalinta zai kwasa daga kyawawan ayyukan azzalimin gwargwdan zalincinsa, idan azzalimin ba shi da wasu kyawawan ayyuka sai a labtawa azzalimin munanan ayyukan wanda aka zalinta gwargwadan zalincin da ya yi.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa akan nisantar zalinci da kuma ta'addanci.
  • Kwaɗaitarwa akan yin gaggawa dan kuɓutar da kawuna daga abinda suka rataya da shi na haƙƙoƙi.
  • Ayyuka na gari zalintar mutane da cutar da su yana ɓata su kuma yana tafiyar da amfaninsu.
  • Haƙƙoƙin bayi Allah ba Ya gafarta su, sai ta hanyar mai da su ga masu su.
  • Dinari da dirhami sune tsani na jawo abubuwan amfani a duniya, amma a ranar Lahira to sai dai kyawawan ayyuka da munana kawai.
  • Wasu daga cikin malamai sun faɗa a cikin mas'alar Irbad: Idan wanda aka zalinta bai sani ba to babu buƙatuwar ya sanar masa, misali a ce ya zage shi a wani wuri daga cikin wurare kuma ya tuba, to a nan shi babu wata buƙatuwa ya sanar da shi, saidai babu bukatar ya sanar da shi , saidai ya nema masa gafara, kuma ya yi masa addu'a, ya yabi alherinsa a wuraran da ya zage shi a cikinsu, da haka ne zai warware daga gare shi .
Sharhi: العربية

أمر النبي صلى الله عليه وسلم كل من وقع منه ظلم لأخيه المسلم في عرض، أو مال، أو دم أن يطلب ممن ظلم أن يسامحه ما دام في الدنيا، قبل أن يأتي يوم القيامة حيث لا ينفع دينار من ذهب ولا درهم من فضة يدفعه لمن ظلمه ليفدي به نفسه؛ إذ القصاص يومها بالحسنات والسيئات؛ حيث يأخذ المظلوم من حسنات الظالم بقدر مظلمته التي ظُلِمها، فإن لم يكن للظالم حسنات وُضِع من سيئات المظلوم على الظالم بقدر المظلمة.

  • الحرص على البُعد عن الظلم والاعتداء.
  • الحث على المبادرة لاستبراء الذمة مما عَلِق بها من حقوق.
  • الأعمال الصالحة يفسدها ويذهب ثمرتها ظلمُ الناس وإيذاؤهم.
  • حقوق العباد لا يغفرها الله إلا بإرجاعها إلى أهلها.
  • الدينار والدرهم هما وسيلة لجلب المنافع في الدنيا، أما في يوم القيامة فالحسنات والسيئات.
  • قال بعض العلماء في مسألة العِرْض: إن كان المظلوم لم يَعلَمْ فلا حاجة أن يُعلِمَه، مثل أن يكون قد سبَّه في مجلس من المجالس وتاب، فإنه لا حاجة أن يُعلِمَه، ولكن يستغفر له ويدعو له، ويُثني عليه بالخير في المجالس التي كان يسُبُّه فيها، وبذلك يَتَحلَّل منه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari