Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ الدِّينَ يُسْرٌ، وَلَنْ يُشَادَّ الدِّينَ أَحَدٌ إِلَّا غَلَبَهُ، فَسَدِّدُوا وَقَارِبُوا، وَأَبْشِرُوا، وَاسْتَعِينُوا بِالْغَدْوَةِ وَالرَّوْحَةِ وَشَيْءٍ مِنَ الدُّلْجَةِ».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Addini mai sauƙi ne, babu wanda zai tsananta cikinsa face sai ya rinjaye shi, saboda haka ku daidaita ku kusanto, ku yi bushara, ku nemi taimakon Allah da jijjifi da kuma yammaci da wani abu na duhun dare".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa Addinin Musulunci an gina shi akan sauƙaƙawa da sauƙi a dukkan sha’aninsa, sauƙi yana ƙarfafa a lokacin samun gajiyawa da buƙata, kuma domin cewa tsanantawa a ayyuka na Addini da barin sauƙi ƙarshensa shi ne gajiyawa da yankewa daga barin aiki gabaɗayansa ko wani daga ciki. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan tsakatsakiya ba tare da zirfafawa ba; kada bawa ya taƙaita a cikin abinda aka umarce shi da shi, kuma kada ya ɗorawa kansa abinda ba zai iya ba, idan ya gajiya daga cikakken aiki to ya yi aiki akan abinda yake kusa da hakan. Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi bushara da sakamako mai yawa akan dawwamammen aiki koda kadan ne ga wanda ya gajiya daga aiki cikakke; domin kasawa idan bata kasance daga aikinsa ba to bata lazimtar tauye ladansa. Yayin da cewa duniya a haƙiƙa gidan tafiya ce da tashi zuwa lahira sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi umarni da neman taimako akan dawwama akan ibada ta hanyar yinta a cikin lokuta uku masu sa nishaɗantarwa: Na farko: Jijjifi: Da tafiya a farkon yini; tsakanin sallar Asuba da hudowar rana. Na biyu: Yammaci: Da tafiya bayan karkacewar rana. Na uku: Duhun dare: Da tafiyar dare gabaɗayansa ko sashinsa, domin cewa aikin dare yafi wahala akan aikin rana sai aka yi umarni da sashinsa da faɗinsa: Da wani abu daga duhun dare.
Fa'idoji
- Sauƙi da afuwar shari'ar Musulunci da tsakatsakiyarta tsakanin wuce gona da iri da kuma sakaci.
- Ya wajaba akan bawa ya aikata umarni gwargwadan ikonsa, ba tare da sakaci ko tsanantawa ba.
- Ya wajaba akan bawa ya zaɓi lokutan nishaɗi a cikin ibada, waɗannan lokuta ukun a keɓancesu sune mafi hutawar jiki dan yin ibada a cikinsu.
- Ibnu Hajar Al’Asƙalani ya ce: Kamar cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa matafiyi magana ne zuwa manufa, waɗannan lokuta ukun sune mafi daɗin lokutan matafiyi, sai ya faɗakar da shi akan lokutan kazar-kazar; domin matafiyi idan ya yi tafiyar dare da rana gaba ɗaya zai gajiya ya yanke, idan ya kintaci tafiya a cikin waɗannan lokuta masu nishaɗantarwa sai ya samu damar dawwama ba tare da wahala ba.
- Ibnu Hajar ya ce: Nuni a cikin wannan hadisin zuwa riƙo da sauƙi na shari'a, domin riƙo da azima a lokacin sauƙi zirfafawa ne, kamar wanda ya bar Taimama a lokacin gajiyawa daga anfani da ruwa sai anfani da shi ya kai shi zuwa faruwar wata cuta.
- Ibnul Munir ya ce; A cikin wannan Hadisin akwai alama daga alamomin Annabci, haƙiƙa mun ga mutane a gabaninmu sun ga cewa dukkan mai zirfafawa a Addini zai yanke, bawai ana nufin hana neman mafi cika a ibada ba cewa shi yana daga al'amura ababen yabo, kai hana wuce gona da iri mai kaiwa ne zuwa ƙosawa, kai zirfafawa a aikin nafila mai kaiwa ne zuwa ga barin abin da ya fi, ko fitar da farilla daga lokacinta kamar wanda ya kwana yana sallar dare gaba ɗayansa sai ya yi bacci daga sallar Asuba a cikin jam’i, ko zuwa lokacin hudowar rana sai lokacin farillar ya fita.
Sharhi: العربية
بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ دينَ الإسلامِ مبنيٌّ على التيسير والسهولة في كل شؤونه، ويتأكد التيسير عند وجود سبب العجز والحاجة، ولأنَّ التعمُّقَ في الأعمال الدينية وترك الرفق عاقبتُه العجز والانقطاع عن العمل كله أو بعضه، ثم حث صلى الله عليه وسلم على التوسط من غير مبالغة؛ فلا يُقصِّر العبد فيما أُمر به، ولا يتحمل ما لا يطيقه، فإن عجز عن العمل بالأكمل؛ فالعمل على ما يَقْرُبُ منه. وبشَّر صلى الله عليه وسلم بالثواب الجزيل على العمل الدائم وإن قلَّ لمَن عجز عن العمل بالأكمل؛ لأن العجز إذا لم يكن من صنيعه فلا يستلزم نقص أجره. وحيث أن الدنيا في الحقيقة دار سفر ونُقْلة إلى الآخرة أمر صلى الله عليه وسلم بالاستعانة على مداومة العبادة بإيقاعها في الأوقات الثلاثية المنشطة: الأول: الغَدوة: بسير أول النهار؛ ما بين صلاة الفجر وطلوع الشمس. الثاني: الرَّوحة: بالسير بعد الزوال. الثالث: الدُّلْجة: بسير الليل كله أو بعضه، ولأن عمل الليل أشق من عمل النهار أمر ببعضه بقوله: وشيءٍ من الدلجة.
- يُسر وسماحة الشريعة الإسلامية وتوسُّطها بين الإفراط والتفريط.
- على العبد أن يأتي بالأمر بقدر استطاعته، من دون تساهل أو تشديد.
- على العبد أن يختار أوقات النشاط في العبادة، وهذه الأوقات الثلاثة بخصوصها هي أروح ما يكون فيها البدن للعبادة.
- قال ابن حجر العسقلاني: كأنه صلى الله عليه وسلم خاطب مسافرًا إلى مقصدٍ، وهذه الأوقات الثلاثة أطيب أوقات المسافر، فنبهه على أوقات نشاطه؛ لأن المسافر إذا سافر الليل والنهار جميعًا عجز وانقطع، وإذا تحرَّى السير في هذه الأوقات المنشطة أمكنته المداومة من غير مشقة.
- قال ابن حجر: الإشارة في هذا الحديث إلى الأخذ بالرخصة الشرعية، فإنّ الأخذ بالعزيمة في موضع الرخصة تَنَطُّعٌ، كمن يترك التيمم عند العجز عن استعمال الماء فيفضي به استعماله إلى حصول الضرر.
- قال ابن المنير: في هذا الحديث عَلَمٌ من أعلام النبوة، فقد رأينا ورأى الناس قبلنا أن كل متنطع في الدين ينقطع، وليس المراد مَنْعِ طلب الأكمل في العبادة فإنه من الأمور المحمودة، بل منع الإفراط المؤدّي إلى الملال، أو المبالغة في التطوع المفضي إلى ترك الأفضل، أو إخراج الفرض عن وقته كمَن بات يصلي الليل كلَّه فنام عن صلاة الصبح في الجماعة، أو إلى أن طلعت الشمس فخرج وقت الفريضة.