Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا يَنْظُرُ اللهُ إِلَى رَجُلٍ أَتَى رَجُلًا أَوِ امْرَأَةً فِي دُبُرٍ».
Fassara
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa ga namijin da ya zo wa wani namiji ko wata mace ta dubura".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana narko mai tsanani da cewa Allah ba Ya duba duban rahama zuwa namijin da ya zo wa namiji ta duburarsa ko mace ta duburarta, kuma hakan laifi ne babba daga cikin manyan laifuka.
Fa'idoji
- Zakkewa namiji ga namiji - shi ne liwaɗi - yana daga manyan zunubai.
- Zakkewa mace ta duburarta yana daga manyan zunubai.
- (Allah ba Ya duba) wato duba na rahama da tausayi, ba ana nufi da shi cewa: Duba gamamme ba; domin Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - wani abu ba ya ɓoyuwa gare Shi kuma wani abu ba ya fakuwa daga ganinSa.
- Waɗannan ayyukan suna daga manyan (ayyukan) alfasha kuma mafi haɗarinsu akan mutuntaka; dan abinda ke cikinsu na saɓawa nagartacciyar ɗabi'a ta mutuntaka, da ƙarancin zuriya, da ɓa ta rayuwar auratayya, da dasa ƙiyayya da gaba, da afkawa a wuraren ƙazanta.
Sharhi: العربية
بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم الوعيدَ الشديدَ بأنَّ الله لا ينظر نظرةَ رحمةٍ إلى رجلٍ أتى رجلًا في دُبُرِهِ أو امرأة في دُبُرها، وأنه كبيرة من كبائر الذنوب.
- إتيان الرجلِ الرجلَ -وهو اللواط- من كبائر الذنوب.
- إتيان المرأة في دبرها من كبائر الذنوب.
- (لا ينظر الله) أي نظر رحمة ورأفة، وليس المراد به: النظر العام؛ لأن الله سبحانه وتعالى لا يخفى عليه شيء ولا يغيب عن بصره شيء.
- هذه الأعمال من أعظم الفواحش وأخطرها على البشرية؛ لما فيها من مخالفة الفطرة البشرية السليمة، وقلة النسل، وإفساد الحياة الزوجية، وغرس العداوة والبغضاء، والوقوع في الأماكن المستقذرة.