Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عِكْرِمَةَ: أَنَّ عَلِيًّا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ حَرَّقَ قَوْمًا، فَبَلَغَ ابْنَ عَبَّاسٍ فَقَالَ: لَوْ كُنْتُ أَنَا لَمْ أُحَرِّقْهُمْ لِأَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لاَ تُعَذِّبُوا بِعَذَابِ اللَّهِ»، وَلَقَتَلْتُهُمْ كَمَا قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ بَدَّلَ دِينَهُ فَاقْتُلُوهُ».
Fassara
Daga Ikramah: Cewa Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ƙona wasu mutane, sai labarin ya kaiwa Ibnu Abbas sai ya ce: Da ace ni ne ba zan ƙonasu ba; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kada Ku yi azaba da azabar Allah», da na kashe su kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Duk wanda ya canja Addininsa to ku kashe shi».
Sharhi
Aliyu ibnu Abi Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya yi ijtihadi sai ya ƙona wasu mutane daga cikin zindiƙai waɗanda suka yi ridda suka bar Musulunci (ya Kona su) da wuta, sai labarin hakan ya kai ga Abdullahi ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su -, sai ya ƙarfafe shi akan kisan su; sai dai ya yi inkarin ƙona su da wuta. Kuma ya ce: Da ace nine a matsayinsa da ban ƙonasu da wuta ba; domin shi Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa babu mai yin azaba da wuta sai Ubangijin wuta, saidai kashesu ya wadatar, inda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Duk wanda ya yi ridda daga Musulunci ya canja Addinisa zuwa wani Addinin daban to ku kashe shi.
Fa'idoji
- Wajabcin kashe wanda ya yi ridda ya bar Musulunci da ijma'in ma'abota ilimi, hakan da sharuɗɗansa, bamai aikata haka sai shugaba da alƙali.
- Faɗinsa: "Wanda ya canja Addininsa to ku kashe shi" wato: Wanda ya yi ridda daga Musulunci: Hukunci ne gamamme ga maza da mata.
- Wanda ya yi ridda ba'a barinsa akan riddarsa, kai za'a kira shi zuwa ga Musulunci, idan bai amsa ba sai a kashe shi.
- A cikin wannan hadisin akwai hani akan azabtarwa da wuta, kuma haddodi ba'a zartar da su da wuta.
- Falalar Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su -, da yalwar iliminsa da fahimtarsa da hadisan Annbi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- A cikin wannan akwai ladabin inkari akan wanda ya saɓa.
Sharhi: العربية
اجتهد علي بن أبي طالب رضي الله عنه فحرّق بالنار قومًا من الزنادقة المرتدين عن الإسلام، فبلغ عبدَ الله بن عباس رضي الله عنهما ذلك، فأيَّده على قتلهم؛ لكن أنكر تحريقَهم بالنار. وقال: لو كنت مكانه لما أحرقتهم بالنار؛ لأنه صلى الله عليه وسلم بين أنه لا يُعذِّب بالنار إلا الله رب النار، ولكن يكفي قتلهم حيث قال صلى الله عليه وسلم: من ارتد عن الإسلام وبدل دينه لدين آخر فاقتلوه.
- وجوب قتل المرتد عن دين الإسلام بإجماع أهل العلم، وذلك بشروطه، ولا يفعل ذلك إلا الإمام والحاكم.
- قوله: "من بدَّل دينه، فاقتلوه" أي: من ارتد عن الإسلام: حكمٌ عامٌّ للرجال والنساء.
- المرتد لا يُقرُّ على ردته بل يُدعى إلى الإسلام، فإن لم يجب قُتِلَ.
- في هذا الحديث النهي عن التعذيب بالنار، وأن الحدود لا تستوفى بالنار.
- فضل ابن عباس رضي الله عنهما، وسعة علمه وفقهه بأحاديث النبي صلى الله عليه وسلم.
- فيه أدب الإنكار على المخالف.