Hadisai

Na haneku da shiga wurin mata" sai wani mutum daga mutanen Madina ya ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin ƙanin miji fa? ya ce: "Ƙanin miji (shi ne) mutuwa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عُقْبَةَ بْنِ عَامِرٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِيَّاكُمْ وَالدُّخُولَ عَلَى النِّسَاءِ» فَقَالَ رَجُلٌ مِنَ الأَنْصَارِ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَفَرَأَيْتَ الحَمْوَ؟ قَالَ: «الحَمْوُ المَوْتُ».

Fassara

Daga Uƙubah ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Na haneku da shiga wurin mata" sai wani mutum daga mutanen Madina ya ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin ƙanin miji fa? ya ce: "Ƙanin miji (shi ne) mutuwa".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar daga cakuɗuwa da mata ajanibai (waɗanda ba muharramai ba), ya ce: Ku kiyaye kawunanku da ku shiga gurin mata, mata kuma su shiga gurinku. Sai wani mutum daga mutanen Madina ya ce: Shin kana ganin makusantan miji fa; kamar ɗan uwan miji da ɗan ɗan uwansa, da baffansa da ɗan baffansa, da ɗan 'yar uwarsa, da makamancinsu daga waɗanda aure da su yake halatta gare shi da a ce ba mai aure ba ce? Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ku kiyaye shi kamar yadda kuke kiyayar mutuwa! domin kaɗaitaka da 'yan uwan miji mai kaiwa ne zuwa ga fitina da halaka a cikin Addini, makusantan miji banda iyayensa da 'ya'yansa sune mafi cancanta da hani cikin ajnabi; domin kaɗaitaka da makusancin miji tafi yawa daga kaɗaitaka da waninsa, kuma sharri ana tinanin afkuwarsa ne daga gare shi sama da waninsa ba tare da wani inakri akansa ba, kuma domin cewa shi babu makawa daga gare shi , kuma tsare shi ba ya yiwuwa daga gareta, yayin da al'ada ta gudana da sassauci a cikinsa sai namiji ya keɓanta da matar dan uwansa; to shi yana kama da mutuwa a muni da barna, sabanin namiji ajnabi cewa shi ana kulawa daga gare shi.

Fa'idoji

  • Hani daga shiga gun ajanibai da kaɗaitaka da su, dan toshe kafar afkawa cikin alfasha.
  • Wannan mai gamewa ne a duk wani da ba mararrami ba na ɗan uwan miji da makusantansa, waɗanda su ba muharraman matar ba ne, kuma babu makawa da izina ta shigar ta zama mai kaiwa ce zuwa ga kaɗaitakarsu.
  • Nisanta daga wuraren zamiya mai gamewane, dan tsoron afkawa cikin sharri.
  • Al-Nawawi ya ce: Ma'abota ilimi na luga sun haɗu akan cewa al-Ahma'u (su ne) 'yan uwan mijin mace kamar babansa da baffansa, da ɗan uwansa da ɗan ɗan uwansa, da ɗan baffansa da makamancinsu, kuma al-Aktan (su ne) 'yan uwan matar mutum, surukai kuma sun haɗa nau'i biyun.
  • Ya kamanta (ɗan uwan miji) da mutuwa, Ibnu Hajar ya ce; Larabawa suna siffanta abinda ake ƙi da mutuwa, ta fuskar kamanceceniyar cewa ita mutuwa ce a Addini idan saɓo ya afku, kuma mutuwar wacce aka keɓanta da ita ce idan saɓo ya afku kuma jifa ya wajaba, kuma halakar mace da rabuwar mijinta idan kishi ya ɗaike shi akan sakinta.
Sharhi: العربية

حَذَّرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم مِن الاختلاط بالنساء الأجنبيات، وقال: اتقوا أنفسَكم أنْ تدخلوا على النساء، والنساء أنْ يَدخلْنَ عليكم. فقال رجل من الأنصار: أفرأيتَ أقارب الزوج؛ كأخِ الزوج وابن أخيه، وعمه وابن عمه، وابن أخته، ونحوهم ممن يَحِلُّ لها تزويجُه لو لم تكن مُتزوجة؟ فقال صلى الله عليه وسلم: احذروه كما تَحذَروا الموت! لأنَّ الخَلْوَة بالأَحْمَاء مُؤدِّيَة إلى الفتنة والهلاك في الدِّين، فأقارب الزَّوج غير آبائه وأبنائه أولى بالمنع من الأجنبي؛ لأن الخَلْوَة بقريب الزوج أكثر من الخلوة بغيره، والشر يُتَوَقّع منه أكثر من غيره، والفتنة به أَمْكَنُ؛ لِتَمَكُّنه من الوصول إلى المرأة والخلوة بها من غير نكير عليه، ولأنه لا بُدّ منه، ولا يمكن حَجْبُه عنها، حيث جرت العادة بالتساهل فيه فيخلو الرجل بامرأة أخيه؛ فهو يُشْبِه الموتَ في الاستقباح والمفسدة، بخلاف الرجل الأجنبي فإنه يُحْذَرُ منه.

  • النهيُ عن الدخول على الأجنبيات والخلوة بهن، سَدًّا لذريعة وقوع الفاحشة.
  • هذا عامٌّ في الأجانب من أخي الزوج وأقاربه، الذين ليسوا محارم للمرأة، ولا بد من اعتبار أن يكون الدخول مقتضيًا للخلوة.
  • الابتعاد عن مواطن الزَّلَل عامة، خشية الوقوع في الشر.
  • قال النووي: اتفق أهل العلم باللغة على أنَّ الأحْمَاءَ أقاربُ زوج المرأة كأبيه وعمه، وأخيه وابن أخيه، وابن عمه ونحوهم، وأن الأَخْتَانَ أقاربُ زوجة الرجل، وأنَّ الأصْهارَ تقعُ على النوعين.
  • شَبَّهَ (الحَمْوَ) بالموت، قال ابن حجر: والعرب تَصف الشيء المكروه بالموت، وجْهُ الشَّبَهِ أنه موتُ الدِّين إنْ وقعت المعصية، وموتُ المُختلي إن وقعت المعصية ووجب الرَّجْم، وهلاك المرأة بفراق زوجها إذا حَمَلَتْه الغَيْرَة على تَطلِيقِها.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari