Hadisai

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsinewa mai karɓar rashawa da mai ba da ita a hukunci

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neTirmizi da Ahmad sun rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: لَعَنَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الرَّاشِيَ وَالْمُرْتَشِيَ فِي الْحُكْمِ.

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsinewa mai karɓar rashawa da mai ba da ita a hukunci.

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mummnar addu'a da korewa da nisantarwa daga rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - a kan mai ba da rashawa da mai karɓarta. Daga hakan akwai abin da ake ba wa alƙalai don su yi zalunci a hukuncin da suke jiɓintarsa; don mai bayarwa ya kai ga manufarsa ba tare da wani haƙƙi ba.

Fa'idoji

  • Ba da rashawa yana haramta, da karɓarta da yin hanya zuwa gareta, da taimako a kanta; don abin da ke cikinta na taimakekeniya a kan ƙarya (ɓarna).
  • Rashawa tana daga manyan zunubai; domin cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsinewa mai karɓarta da mai ba da ita.
  • Rashawa a shari'a (Alƙalanci) da hukunci ita ce mafi girman laifi, kuma mafi tsanani; don abin da ke cikinta na zalunci da hukunci ba tare da abin da Allah Ya saukar ba.
Sharhi: العربية

دعا النبيُّ صلى الله عليه وسلم بالطرد والإبعاد من رحمة الله عز وجل لدافع الرشوة وآخذها وقابضها. ومن ذلك ما يُدفع للقُضاة ليَحِيْفُوا في الحُكْم الذي يَتَولونه؛ ليتوصل به المُعطي إلى مراده بغير حق.

  • يَحْرُمُ بذل الرشوة، وأخذُهَا، والتوسُّطُ فيها، والإعانةُ عليها؛ لما فيها من التعاون على الباطل.
  • الرشوة من كبائر الذنوب؛ لأنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلم لعن آخذَها ومعطيَها.
  • الرشوة في باب القضاء والحُكْم أعظم جُرْمًا، وأشد إثمًا؛ لما فيها من الظلم والحكم بغير ما أنزل الله.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari