Hadisai

Tafkina tafiyar wata ne, ruwansa ya fi nono fari, kamshinsa ya fi almiski kanshi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي الله عنهما قَالَ: قالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «حَوْضِي مَسِيرَةُ شَهْرٍ، مَاؤُهُ أَبْيَضُ مِنَ اللَّبَنِ، وَرِيحُهُ أَطْيَبُ مِنَ المِسْكِ، وَكِيزَانُهُ كَنُجُومِ السَّمَاءِ، مَنْ شَرِبَ مِنْهَا فَلاَ يَظْمَأُ أَبَدًا».

Fassara

Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tafkina tafiyar wata ne, ruwansa ya fi nono fari, kamshinsa ya fi almiski kanshi, kofunansa kamar taurarin sama ne, wanda ya sha daga gare shi ba zai yi kishirwa ba har abada".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari cewa yana da wani tafki a ranar Alkiyama, tsawonsa tafiyar wata ne kuma fadinsama kamar haka ne. Kuma lallai cewa ruwansa ya fi nono tsananin fari. Kuma cewa kamshinsa mai dadi ne ya fi kamshin almiski. Kuma kofinansa tamkar taurarin sama ne a yawansu, Wanda ya sha daga tafkin da wadancan kofinan ba zai yi kishirwa ba har abada.

Fa'idoji

  • Tafkin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - matattarar ruwa ne mai girma, muminai za su zo masa daga al'ummarsa a ranar lahira.
  • Samuwar ni'ima ga wanda zai sha daga tafkin ba zai yi kishirwa ba har abada.
Sharhi: العربية

أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أنّ له حوضًا يوم القيامة، طوله مسيرة شهر وعرضه كذلك، وأنّ ماءَه أشدّ بياضًا مِن اللَّبن، وأنّ رائِحتَه زكيَّة أطيب من ريح المسك، وأباريقه مثل نجوم السماء في كثرتها، مَن شرب مِن الحوض بتلك الأباريق لا يعطش أبدًا.

  • حوض النبي صلى الله عليه وسلم مجمع ماء عظيم يرده المؤمنون من أمته يوم القيامة.
  • حصول النعيم لمن يشرب من الحوض فلا يظمأ أبدا.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari