Hadisai

Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAhmad ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ ابْنِ أَبِي مُلَيْكَةَ: عَنْ بَعْضِ أَزْوَاجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -قَالَ: أَبُو عَامِرٍ، قَالَ نَافِعٌ: أُرَاهَا حَفْصَةَ- أَنَّهَا سُئِلَتْ عَنْ قِرَاءَةِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَتْ: إِنَّكُمْ لَا تَسْتَطِيعُونَهَا قَالَ: فَقِيلَ لَهَا أَخْبِرِينَا بِهَا. قَالَ: فَقَرَأَتْ قِرَاءَةً تَرَسَّلَتْ فِيهَا قَالَ أَبُو عَامِرٍ: قَالَ نَافِعٌ: فَحَكَى لَنَا ابْنُ أَبِي مُلَيْكَةَ {الحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ} [الفاتحة: 2] ثُمَّ قَطَّعَ {الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ} [الفاتحة: 1] ثُمَّ قَطَّعَ {مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ}.

Fassara

Daga Ibnu Abi Mulaikah: Daga wata daga cikin matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Abu Amir ya ce: Nafi'u Ya ce: Ina zatan Nana Hafsa ce - Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Lallai ku ba zaku iya ba, ya ce: Sai aka ce mata bamu labarin yadda karatun yake. Ya ce: Sai ta yi karatun da ta yi a sake, Abu Amir ya ce: Nafi'u ya ce: Sai Ibnu Abi Mulaikah ya hakaito mana {Alhamdu lillahi rabbil Aalamin} [al-Fatiha: 2]. sannan ya yanyanke {Al-rahmanur Rahim} [al-Fatiha: 1] sannan ya yanyanke {Maliki yaumud din}.

Sharhi

An tambayi Nana Hafsa uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -: Yaya Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake karanra Alƙur'ani? Sai ta ce: Lallai ku ba zaku iya irin nasa ba, sai aka ce mata; Faɗa mana. Nafi'u ya ce sai Ibnu Abi Mulaikah ya karanta karatun da yayi shi a hankali; dan ta hakaito kuma ta kusanto musu da yadda karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ke, sai ya karanta: {Alhamdu lillhi rabbil Aalamin} sannan ya yanyanke karatun, {Arrahmanur rahim}, sannan ya yanyanke karatun, {Maliki yaumid din}.

Fa'idoji

  • Bayanin shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin karatun Alƙur'ani.
  • Ɗabbaƙawa na ilimi na bayanin kaifiyyar karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Halaccin yin karatu a hankali kuma hakan ya fi kusanto da Tadabburin ma'anoninsa.
  • Himmatuwar magabata na gari da Alƙur'ani mai girma da kuma aikin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Muhimmancin sanin Tajwidi da kuma Ulumul Ƙur'an.
Sharhi: العربية

سئلت حفصة أم المؤمنين رضي الله عنها: كيف كانت قراءة النبي صلى الله عليه وسلم للقرآن؟ فقالت: إنكم لا تقدرون على مثلها، فقيل لها: أخبرينا. قال نافع فقرأ لنا ابن أبي مليكة قراءة تمهل فيها؛ لتحكي وتقرب لهم كيفية قراءة النبي صلى الله عليه وسلم، فقرأ: {الحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ} ثم قطع القراءة، {الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ}، ثم قطع القراءة، {مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ}.

  • بيان هدي النبي صلى الله عليه وسلم في قراءة القرآن.
  • التطبيق العملي لبيان كيفية قراءة النبي صلى الله عليه وسلم.
  • مشروعية الترسُّل في قراءة القرآن فهو أدعى إلى تدبره.
  • اهتمام السلف الصالح بالقرآن الكريم وبعمل النبي صلى الله عليه وسلم.
  • أهمية معرفة التجويد وعلوم القرآن.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari