Hadisai

Addini nasiha ne

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي رُقَيَّةَ تَمِيمِ بْنِ أَوْسٍ الدَّارِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «الدِّينُ النَّصِيحَةُ» قُلْنَا: لِمَنْ؟ قَالَ: «لِلهِ وَلِكِتَابِهِ وَلِرَسُولِهِ وَلِأَئِمَّةِ الْمُسْلِمِينَ وَعَامَّتِهِمْ».

Fassara

Daga Abu Ruƙayya Tamim ibnu Aws al-Dari - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Addini nasiha ne" Muka ce; ga wa? Ya ce; "Ga Allah da littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin musulmai da dukkaninsu".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa Addini a tsaye yake a kan ikhlasi da gaskiya, har sai an yi shi kamar yadda Allah Ya wajabta, cikakke ba tare da tawaya ko algus ba. Sai aka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Ga wa nasihar za ta kasance? sai ya ce: Na farko: Nasiha ga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -: ta hanyar tsarkake aiki gare shi, da rashin haɗa Shi da wani, kuma mu yi imani da RububiyyarSa da UluhiyyarSa da sunayenSa da siffofinSa, da girmama umarninSa, da kira zuwa ga imani da Shi. Na biyu: Nasiha ga littafinSa shi ne AlKur'ani mai girma: Shi ne mu ƙudirce cewa shi zancenSa ne, kuma ƙarshen littattafanSa, kuma shi mai shafewa ne ga dukkanin shari'o'in da suke kafinsa, kuma mu girmama shi, mu karanta shi haƙiƙanin karanta shi, mu yi aiki da muhkam ɗinsa, kuma mu miƙa wuya ga masu kamanceceniya daga gare shi, kuma mu kore tawilin masu karkace masa, mu wa'azantu da wa'azozinsa, da yaɗa ilimummukansa, mu yi kira zuwa gare shi. Na uku: Nasiha ga ManzonSa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Shi ne mu ƙudire cewa shi ne ƙarshen Manzanni, mu gasgata shi a cikin abin da ya zo da shi, mu yi riko da umarninsa, mu nisanci haninsa, kuma kada mu bautawa Allah da komai sai abin da ya zo da shi, mu girmama haƙƙinsa, mu girmama shi, mu yaɗa Da'awarsa, mu yaɗa shari'arsa, kuma mu kore tuhuma daga gare shi. Na huɗu: Nasiha ga shugabannin musulmai: Ta hanyar taimakonsu a kan gaskiya, da rashin jayayya da su a al'amari, da ji da biyayya garesu akan biyayya ga Allah. Na biyar: Nasiha ga musulami: Ta hanyar kyautatawa zuwa garesu da kiransu, da hana cutar da su, da son alheri garesu, da taimakekeniya tare da su a kan biyayya da tsoron Allah.

Fa'idoji

  • Umarni da nasiha ga kowa da kowa.
  • Girman matsayin nasiha a addini.
  • Addini ya ƙunshi ƙudirce-ƙudirce da maganganu da kuma ayyuka.
  • Yana daga cikin nasiha tsarkake zuciya daga algus ga wanda aka yi wa nasihar da kuma nufin alheri gareshi.
  • Kyakkyawar koyarwar Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da yake ambaton abu a dunkule sannan ya yi shi dalla-dalla.
  • Farawa da mafi muhimmanci sannan mai bi masa, yayin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fara da nasiha ga Allah, sannan littafinsa, sannan manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sannan ga shugabannin musulmai, sannan kowa da kowansu.
Sharhi: العربية

أَخبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم بأنَّ الدين قائمٌ على الإخلاص والصدق، حتى يؤدَّى كما أوجب الله، كاملًا دون تقصير أو غش. فقيل للنبي صلى الله عليه وسلم: لمن تكون النصيحة؟ فقال: أولًا: النصيحة لله سبحانه وتعالى: بإخلاص العمل له، وعدم الإشراك به، وأن نؤمن بربوبيته وألوهيته وأسمائه وصفاته، وتعظيم أمره، والدعوة إلى الإيمان به. ثانيًا: النصيحة لكتابه وهو القرآن الكريم: بأن نعتقد أنه كلامُه، وآخِرُ كتبِه، وأنه ناسخ لجميع الشرائع قبله، ونعظِّمه، ونتلوه حق تلاوته، ونعمل بمُحْكَمِه، ونسلم بمتشابهه، ونَذُبُّ عن تأويل المُحرِّفين له، ونعتبر بمواعظه، وننشر علومه، وندعو إليه. ثالثًا: النصيحة لرسوله محمد صلى الله عليه وسلم: بأن نعتقدَ أنه آخِرُ الرسل، ونصدِّقَه فيما جاء به، ونَمتَثِلَ أمرَه، ونجتنبَ نهيَه، وأن لا نتعبدَ لله إلا بما جاء به، ونُعظِّمَ حقَّه، ونوقرَه، ونَبُثَّ دعوته، ونَنشُرَ شريعتَه، ونَنفيَ التُّهَمَ عنه. رابعًا: النصيحة لأئمة المسلمين: بمعاونتهم على الحق، وعدم منازعتهم الأمر، والسمع والطاعة لهم في طاعة الله. خامسًا: النصيحة للمسلمين: بالإحسان إليهم ودعوتهم، وكَفِّ الأذى عنهم، ومحبة الخير لهم، والتعاون معهم على البر والتقوى.

  • الأمر بالنصيحة للجميع.
  • عِظَم منزلة النصيحة من الدين.
  • اشتمال الدين على الاعتقادات والأقوال والأعمال.
  • من النصيحة تصفية النفس من الغش للمنصوح له وإرادة الخير له.
  • حسن تعليم الرسول صلى الله عليه وسلم حيث يذكر الشيء مُجملًا ثم يُفصّله.
  • البداءة بالأهم فالأهم، حيث بدأ النبي صلى الله عليه وسلم بالنصيحة لله، ثم لكتابه، ثم لرسوله صلى الله عليه وسلم ثم لأئمة المسلمين، ثم عامتهم.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari