Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ صَخْرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْت رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم يَقُولُ: «مَا نَهَيْتُكُمْ عَنْهُ فَاجْتَنِبُوهُ، وَمَا أَمَرْتُكُمْ بِهِ فَافْعَلُوا مِنْهُ مَا اسْتَطَعْتُمْ، فَإِنَّمَا أَهْلَكَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ كَثْرَةُ مَسَائِلِهِمْ، وَاخْتِلَافُهُمْ عَلَى أَنْبِيَائِهِمْ».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «Duk abin da na haneku daga gare shi to ku nisance shi, kuma abinda na umarce ku da shi to ku zo da shi dai dai iyawarku, domin abin da ya halaka magabatanku (shi ne) yawan tambayoyinsu da kuma saɓawarsu ga Annabawansu».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana mana cewa shi idan ya hana mu wani abu to ya wajaba a kanmu mu nisance shi, ba tare da togaciya ba, idan kuma ya umarce mu da wani abu to wajibi ne a kanmu mu aikata abin da zamu iya daga gare shi. Sannan ya gargaɗemu dan kar mu zama kamar wasu daga cikin al'ummun da suka gabata lokacin da suka yawaita tambayoyi ga Annabawan su tare da saɓa wa annbawan, sai Allah Ya yi musu uƙuba da nau'ikan halaka da rusawa, to yana kamata kada mu zama irinsu dan kada mu halaka kamar yadda suka halaka.
Fa'idoji
- Hadisin ƙa'ida ne akan bayanin wajibi domin aikata abinda aka yi umarni da kuma nisantar abin da aka hana.
- Hani, ba’a yi rangwami akan aikata wani abu daga gare shi ba, umarni kuma an ƙayyade shi da gwargwadan iko; domin bari abin ƙaddarawa ne, aiki kuma yana buƙatuwa zuwa ga iko akan samar da aikin da aka yi umarni da shi.
- Hani akan yawan tambaya, haƙiƙa malamai sun raba tambaya gida biyu: Ta ɗayansu: Wadda take kasancewa ta fuskar koyarwa ga abinda ake buƙatuwa zuwa gare shi na al'amarin addini, to wannan an yi umarni da ita, daga wannan nau'in tambayoyin sahabbai suke. Na biyu: Wadda ta kasance ta fuskar ta'annuti da ɗorawa kai to wannan ita ce wacce aka hana.
- Gargaɗin wannan al'ummar daga saɓawa annabinta, kamar yadda ya afku a cikin al’ummun da suka gabata.
- Abin da aka hana yana ƙunsar kaɗan da mai yawa; domin nisantarsa ba ya yi wu wa sai da nisantar ƙanƙaninsa da mai yawansa, misali: Ya hanemu daga riba to hanin ya ƙunshi ƙanƙaninta da kuma mai yawanta.
- Barin sabubban da zasu iya kaiwa zuwa ga haram; domin hakan yana daga ma'anar nisanta.
- Ba ya kamata ga mutum idan ya ji umarnin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce ba: Shin wajibi ne ko mustahabbi ne, kawai ya wajaba a kansa ya yi gaggawa zuwa aikata shi; saboda faɗinsa: «Ku zo da shi gwargwadan iyawarku».
- Yawan tambayoyi sababi ne na halaka musamman ma a cikin al'amuran da ba zai yi wu akai zuwa garesu ba, misali mas'alolin gaibu, da siffar yanayin ranar alƙiyama, kada ka yawaita tambaya a cikinsu sai ka halaka, sai ka zama mai tsanantawa a cikin Addini mai zirfafawa.
Sharhi: العربية
بين لنا رسول الله صلى الله عليه وسلم أنه إذا نهانا عن شيء وجب علينا اجتنابه بدون استثناء، وإذا أمرنا بشيء فعلينا أن نفعل منه ما نطيق. ثم حذرنا حتى لا نكون كبعض الأمم السابقة حينما أكثروا من الأسئلة على أنبيائهم مع مخالفتهم لهم فعاقبهم الله بأنواع من الهلاك والدمار، فينبغي أن لا نكون مثلهم حتى لا نهلك كما هلكوا.
- الحديث قاعدة في بيان الواجب في إتيان المأمور واجتناب المحظور.
- النهي لم يرخص في ارتكاب شيء منه، والأمر قيد بالاستطاعة؛ لأن الترك مقدور والفعل يحتاج إلى قدرة على إيجاد الفعل المأمور به.
- النهي عن كثرة السؤال، قد قسم العلماء السؤال إلى قسمين: أحدهما: ما كان على وجه التعليم لما يحتاج إليه من أمر الدين، فهذا مأمور به ومن هذا النوع أسئلة الصحابة. والثاني: ما كان على وجه التعنت والتكلف وهذا هو المنهي عنه.
- تحذير هذه الأمة من مخالفة نبيها، كما وقع في الأمم التي قبلها.
- المنهي عنه يشمل القليل والكثير؛ لأنه لا يتأتّى اجتنابه إلا باجتناب قليله وكثيره، فمثلًا: نهانا عن الرِّبا فيشمل قليله وكثيره.
- ترك الأسباب المفضية إلى المحرم؛ لأن ذلك من معنى الاجتناب.
- لا ينبغي للإنسان إذا سمع أمر الرسول صلى الله عليه وسلم أن يقول: هل هو واجب أم مستحبّ، بل عليه بالمبادرة إلى الفعل؛ لقوله: «فَأْتُوا مِنْهُ مَا استَطَعْتُمْ».
- كثرة المسائل سبب للهلاك ولا سيّما في الأمور التي لا يمكن الوصول إليها مثل المسائل الغيبية، وكيفية أحوال يوم القيامة، لا تكثر السؤال فيها فتهلك، وتكون متنطّعًا متعمّقًا.