Hadisai
ƘARUWAR IMANI DA RAGUWARSA
Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
sakamako 9
- 3480
- 6468
Imani tsagi saba’in- ko Sittin- da wani abu ne, mafi falalarsu faɗin: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, mafi ƙasa kuma kawar da ƙazanta daga hanya
Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi - 10101
Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi
Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi - 65001
- 65002
Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe
Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi - 65011
- 65020
Lallai imani yana tsufa a zukatan dayanku kamar yadda tsohon tufafi yake tsufa, ku roki Allah Ya sabunta imani a cikin zukatanku
Ingantacce neHakim da Dabrani ne suka Rawaito shi - 65116
Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammadu a matsayin Manzo
Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi - 65218