Juzu'i 9

الأعراف

Al-A'araf

ayoyi 206MakkiyaJuzu'i 8
Saitunan karatu

Jagorar launukan tajwidi

Sunaye, misalai da layukan ƙasa iri-iri suna bayyana ƙa'idojin baya ga launi. An ɗauko misalan daga rubutun Alƙur'ani da aka wallafa.

Gunna
وَمِمَّا2:3
Nau'o'in Ikhfa'i
يُنفِقُونَ2:3
Nau'o'in Idgami
هُدًى لِّلْمُتَّقِينَ2:2
Iƙlabi
أَلِيمٌۢ بِمَا2:10
Ƙalƙala
رَزَقْنَـٰهُمْ2:3
Madda: harka 2
ٱلرَّحْمَـٰنِ1:1
Madda: harka 2, 4 ko 6
ٱلرَّحِيمِ1:1
Madda: harka 4 ko 5
بِمَآ2:4
Madda: harka 6
ٱلضَّآلِّينَ1:7
Hamzatul wasli
ٱللَّهِ1:1
Lam Shamsiyya
ٱلرَّحْمَـٰنِ1:1
Haruffan da ba a furtawa
ٱلصَّلَوٰةَ2:3

Alamomin tajwidi: cpfair/quran-tajweed (CC BY 4.0), an gina su daga ReciteQuran.com da mus'hafan tajwidi na Dar al-Maarifah; an daidaita wurarensu da rubutun Tanzil na yanzu.

Fassarar Hausa - Abubakar Gumi. Siga: 1.2.2. Sabuntawa ta ƙarshe: 2025-06-26. QuranEnc.com

  1. 88

    ۞ قَالَ ٱلْمَلَأُ ٱلَّذِينَ ٱسْتَكْبَرُوا۟ مِن قَوْمِهِۦ لَنُخْرِجَنَّكَ يَـٰشُعَيْبُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مَعَكَ مِن قَرْيَتِنَآ أَوْ لَتَعُودُنَّ فِى مِلَّتِنَا ۚ قَالَ أَوَلَوْ كُنَّا كَـٰرِهِينَ

    Mashawarta waɗanda suka kangare daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, Munã fitar da kai, Yã Shu'aibu, kai da waɗanda suka yi Ĩmãni tãre da kai, daga alƙaryarmu; kõ kuwa lalle ku kõmo a cikin addininmu." Ya ce: "Ashe! Kuma kõ dã mun kasance mãsu ƙĩ?"

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 88 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  2. 89

    قَدِ ٱفْتَرَيْنَا عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا إِنْ عُدْنَا فِى مِلَّتِكُم بَعْدَ إِذْ نَجَّىٰنَا ٱللَّهُ مِنْهَا ۚ وَمَا يَكُونُ لَنَآ أَن نَّعُودَ فِيهَآ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّنَا ۚ وَسِعَ رَبُّنَا كُلَّ شَىْءٍ عِلْمًا ۚ عَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلْنَا ۚ رَبَّنَا ٱفْتَحْ بَيْنَنَا وَبَيْنَ قَوْمِنَا بِٱلْحَقِّ وَأَنتَ خَيْرُ ٱلْفَـٰتِحِينَ

    "Lalle ne mun ƙirƙira ƙarya ga Allah idan mun kõma a cikin addininku a bãyan lõkacin da Allah ya tsĩrar da mu daga gare shi, kuma bã ya kasancewa a gare mu, mu kõma a cikinsa, fãce idan Alah, Ubangijinmu Ya so. Ubangijinmu Yã yalwaci dukan kõme ga ilmi. Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Ka yi hukunci a tsakãninmu da tsakanin mutãnenmu da gaskiya, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 89 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  3. 90

    وَقَالَ ٱلْمَلَأُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِن قَوْمِهِۦ لَئِنِ ٱتَّبَعْتُمْ شُعَيْبًا إِنَّكُمْ إِذًا لَّخَـٰسِرُونَ

    Kuma mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, idan kun bi Shu'aibu haƙĩƙa kũ, a lõkacin nan, mãsu hasãra ne."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 90 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  4. 91

    فَأَخَذَتْهُمُ ٱلرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا۟ فِى دَارِهِمْ جَـٰثِمِينَ

    Sai tsãwa ta kãma su, sabõda haka suka wãyi gari, a cikin gidan su, sunã guggurfãne.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 91 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  5. 92

    ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ شُعَيْبًا كَأَن لَّمْ يَغْنَوْا۟ فِيهَا ۚ ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ شُعَيْبًا كَانُوا۟ هُمُ ٱلْخَـٰسِرِينَ

    Waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu kamar ba su zauna ba a cikinta, waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu, sun kasance sũ nemãsu hasãra!

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 92 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  6. 93

    فَتَوَلَّىٰ عَنْهُمْ وَقَالَ يَـٰقَوْمِ لَقَدْ أَبْلَغْتُكُمْ رِسَـٰلَـٰتِ رَبِّى وَنَصَحْتُ لَكُمْ ۖ فَكَيْفَ ءَاسَىٰ عَلَىٰ قَوْمٍ كَـٰفِرِينَ

    Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Yã mutãnena! Haƙĩƙa, nã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nã yi muku nasĩha! To, yãya zan yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai?"

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 93 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  7. 94

    وَمَآ أَرْسَلْنَا فِى قَرْيَةٍ مِّن نَّبِىٍّ إِلَّآ أَخَذْنَآ أَهْلَهَا بِٱلْبَأْسَآءِ وَٱلضَّرَّآءِ لَعَلَّهُمْ يَضَّرَّعُونَ

    Kuma ba Mu aika wani Annabi[1] a cikin wata alƙarya ba, fãce Mun kãma mutãnenta da azãba da cũta, tsammãninsu sunã yin ƙasƙantar da kai.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Daga ãyã ta 94 zuwa ãyã ta l03 duka tãlĩƙi ne dõmin farkarwa ga muhimman manganganu waɗanda ƙissoshin Annabawan nan da mutãnensu suka ƙunsa, kuma aka ce haka dai sauran Annabawa da ba a faɗa ba suka zauna da mutãnensu a cikin faɗa a tsakanin gaskiya da ƙarya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 94 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  8. 95

    ثُمَّ بَدَّلْنَا مَكَانَ ٱلسَّيِّئَةِ ٱلْحَسَنَةَ حَتَّىٰ عَفَوا۟ وَّقَالُوا۟ قَدْ مَسَّ ءَابَآءَنَا ٱلضَّرَّآءُ وَٱلسَّرَّآءُ فَأَخَذْنَـٰهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ

    Sa'an nan kuma Muka musanya mai kyau a matsayin mummũna, har su yi yawa, kuma su ce: "Cũta da azãba sun shãfi ubanninmu." (sai su kõma wa kãfirci). Sai Mu kãmã su kwatsam! alhãli kuwa sũ, bã su sansancẽwa."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 95 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  9. 96

    وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ ٱلْقُرَىٰٓ ءَامَنُوا۟ وَٱتَّقَوْا۟ لَفَتَحْنَا عَلَيْهِم بَرَكَـٰتٍ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلْأَرْضِ وَلَـٰكِن كَذَّبُوا۟ فَأَخَذْنَـٰهُم بِمَا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ

    Kuma dã lalle mutãnen alƙaryu sun yi ĩmãni kuma suka yi taƙawa dã haƙĩƙa Mun bũɗe albarkõki a kansu daga sama da ƙasa, kuma amma sun ƙaryata, don haka Muka kãma su da abin da suka kasance sunã tãrãwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 96 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  10. 97

    أَفَأَمِنَ أَهْلُ ٱلْقُرَىٰٓ أَن يَأْتِيَهُم بَأْسُنَا بَيَـٰتًا وَهُمْ نَآئِمُونَ

    Shin, mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbar Mu ta jẽ musu da dare, alhãli kuwa sunã barci?

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 97 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  11. 98

    أَوَأَمِنَ أَهْلُ ٱلْقُرَىٰٓ أَن يَأْتِيَهُم بَأْسُنَا ضُحًى وَهُمْ يَلْعَبُونَ

    Kõ kuwa mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbarMu ta jẽ musu da hantsi, alhãli kuwa sunã wãsa?

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 98 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  12. 99

    أَفَأَمِنُوا۟ مَكْرَ ٱللَّهِ ۚ فَلَا يَأْمَنُ مَكْرَ ٱللَّهِ إِلَّا ٱلْقَوْمُ ٱلْخَـٰسِرُونَ

    Shin fa, sun amince wa makarun Allah? To, bãbu mai amince wa makarun Allah fãce mutãne mãsu hasãra!

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 99 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  13. 100

    أَوَلَمْ يَهْدِ لِلَّذِينَ يَرِثُونَ ٱلْأَرْضَ مِنۢ بَعْدِ أَهْلِهَآ أَن لَّوْ نَشَآءُ أَصَبْنَـٰهُم بِذُنُوبِهِمْ ۚ وَنَطْبَعُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لَا يَسْمَعُونَ

    Shin, kuma bai shiryar da waɗanda suke gãdon ƙasa ba daga bãyan mutãnenta cẽwa da Munã so, dã Mun sãme su da zunubansu, kuma Mu rufe a kan zukãtansu, sai su zama bã su ji?

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 100 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  14. 101

    تِلْكَ ٱلْقُرَىٰ نَقُصُّ عَلَيْكَ مِنْ أَنۢبَآئِهَا ۚ وَلَقَدْ جَآءَتْهُمْ رُسُلُهُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ فَمَا كَانُوا۟ لِيُؤْمِنُوا۟ بِمَا كَذَّبُوا۟ مِن قَبْلُ ۚ كَذَٰلِكَ يَطْبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِ ٱلْكَـٰفِرِينَ

    Waɗancan alƙaryu Munã gaya maka daga lãbãransu, kuma lalle ne, haƙĩƙa manzanninMu sun jẽ musu da hujjõji bayyanannnu; to, ba su kasance sunã yin ĩmãnida abin da suka ƙaryata daga gabãni ba. Kamar wancan ne Allah Yake rufẽwa a kan zukãtan kãfirai.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 101 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  15. 102

    وَمَا وَجَدْنَا لِأَكْثَرِهِم مِّنْ عَهْدٍ ۖ وَإِن وَجَدْنَآ أَكْثَرَهُمْ لَفَـٰسِقِينَ

    Kuma ba Mu sãmi wani alkawari ba ga mafi yawansu, kuma lalle ne, Mun sãmi mafi yawansu, haƙĩƙa, fãsiƙai.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 102 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  16. 103

    ثُمَّ بَعَثْنَا مِنۢ بَعْدِهِم مُّوسَىٰ بِـَٔايَـٰتِنَآ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَإِي۟هِۦ فَظَلَمُوا۟ بِهَا ۖ فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلْمُفْسِدِينَ

    Sa'an nan kuma Mun aika Musa,[1] daga bãyansu, da ãyõyinMu zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka yi zãlunci game da su. To, dũbi yadda ãƙibar maɓarnata take.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] An fitar da ƙissar Bani Isrã'ila dabam, dõmin tã ƙunsa abũbuwa mãsu yawa na faɗa a tsakãnin ƙarya da gaskiya, ta hanyõyi mãsu yawa, a bayyane da ɓõye a cikin Addini.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 103 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  17. 104

    وَقَالَ مُوسَىٰ يَـٰفِرْعَوْنُ إِنِّى رَسُولٌ مِّن رَّبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

    Kuma Musa ya ce: "Ya Fir'auna! Lalle ne nĩ, manzo ne daga Ubangijin halittu."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 104 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  18. 105

    حَقِيقٌ عَلَىٰٓ أَن لَّآ أَقُولَ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلْحَقَّ ۚ قَدْ جِئْتُكُم بِبَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ فَأَرْسِلْ مَعِىَ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ

    "Tabbatacce ne a kan kada in faɗi kõme ga Allah fãce gaskiya. Lalle ne, nã zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka saki Banĩ Isrã'ila tãreda ni."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 105 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  19. 106

    قَالَ إِن كُنتَ جِئْتَ بِـَٔايَةٍ فَأْتِ بِهَآ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

    Ya ce: "Idan kã kasance kã zo da wata ãyã, to, ka kãwõ ta, idan kã kasance daga mãsu gaskiya."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 106 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  20. 107

    فَأَلْقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِىَ ثُعْبَانٌ مُّبِينٌ

    Sai ya jẽfa sandarsa, sai gã ta kumurci bayyanan ne!

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 107 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  21. 108

    وَنَزَعَ يَدَهُۥ فَإِذَا هِىَ بَيْضَآءُ لِلنَّـٰظِرِينَ

    Kuma ya fizge hannun sa, sai ga shi fari ga mãsu dũbi!

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 108 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  22. 109

    قَالَ ٱلْمَلَأُ مِن قَوْمِ فِرْعَوْنَ إِنَّ هَـٰذَا لَسَـٰحِرٌ عَلِيمٌ

    Mashãwarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, matsafi ne mai ilmi."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 109 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  23. 110

    يُرِيدُ أَن يُخْرِجَكُم مِّنْ أَرْضِكُمْ ۖ فَمَاذَا تَأْمُرُونَ

    " Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku: To, mẽne ne kuke shawartawa?"

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 110 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  24. 111

    قَالُوٓا۟ أَرْجِهْ وَأَخَاهُ وَأَرْسِلْ فِى ٱلْمَدَآئِنِ حَـٰشِرِينَ

    Suka ce: "Ka jinkirtar da shĩ, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika da mãsu gayyar mutãne a cikin garũruwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 111 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  25. 112

    يَأْتُوكَ بِكُلِّ سَـٰحِرٍ عَلِيمٍ

    "Su zõ maka da duka matsafi, mai ilmi."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 112 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  26. 113

    وَجَآءَ ٱلسَّحَرَةُ فِرْعَوْنَ قَالُوٓا۟ إِنَّ لَنَا لَأَجْرًا إِن كُنَّا نَحْنُ ٱلْغَـٰلِبِينَ

    Kuma matsafa suka jẽ wa fir'aunã suka ce: "Lalle ne, shin, Munã da ijãra, idan mun kasance mũ ne marinjaya?"

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 113 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  27. 114

    قَالَ نَعَمْ وَإِنَّكُمْ لَمِنَ ٱلْمُقَرَّبِينَ

    Ya ce: "Na, am kuma lalle ne kunã a cikin makusanta."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 114 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  28. 115

    قَالُوا۟ يَـٰمُوسَىٰٓ إِمَّآ أَن تُلْقِىَ وَإِمَّآ أَن نَّكُونَ نَحْنُ ٱلْمُلْقِينَ

    Suka ce: "Ya Mũsã! Kõ dai ka jẽfa, kõ kuwa mu kasance, mũ ne, mãsu jẽfãwa?"

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 115 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  29. 116

    قَالَ أَلْقُوا۟ ۖ فَلَمَّآ أَلْقَوْا۟ سَحَرُوٓا۟ أَعْيُنَ ٱلنَّاسِ وَٱسْتَرْهَبُوهُمْ وَجَآءُو بِسِحْرٍ عَظِيمٍ

    Ya ce: "Ku jẽfa." To a õkacin da suka jẽfa, suka sihirce idãnun mutãne kuma suka tsõratar da su; Kuma suka jẽ da tsafi mai girma."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 116 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  30. 117

    ۞ وَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنْ أَلْقِ عَصَاكَ ۖ فَإِذَا هِىَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ

    Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa: "Ka jẽfa sandarka." Sai gã ta tanã lãƙumar abin da suke ƙarya da shi!

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 117 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  31. 118

    فَوَقَعَ ٱلْحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

    Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 118 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  32. 119

    فَغُلِبُوا۟ هُنَالِكَ وَٱنقَلَبُوا۟ صَـٰغِرِينَ

    Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 119 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  33. 120

    وَأُلْقِىَ ٱلسَّحَرَةُ سَـٰجِدِينَ

    Kuma aka jẽfar da matsafan, sunã mãsu sujada.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 120 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  34. 121

    قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

    Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halittu."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 121 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  35. 122

    رَبِّ مُوسَىٰ وَهَـٰرُونَ

    "Ubangijin Mũsã da Harũna."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 122 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  36. 123

    قَالَ فِرْعَوْنُ ءَامَنتُم بِهِۦ قَبْلَ أَنْ ءَاذَنَ لَكُمْ ۖ إِنَّ هَـٰذَا لَمَكْرٌ مَّكَرْتُمُوهُ فِى ٱلْمَدِينَةِ لِتُخْرِجُوا۟ مِنْهَآ أَهْلَهَا ۖ فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ

    Fir'auna ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni da shi a gabãnin inyi izni a gare ku? Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, mãkirci ne kuka mãkirta a cikin birni, dõmin ku fitar da mutãnensa daga gare shi; To, da sannu zã ku sani."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 123 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  37. 124

    لَأُقَطِّعَنَّ أَيْدِيَكُمْ وَأَرْجُلَكُم مِّنْ خِلَـٰفٍ ثُمَّ لَأُصَلِّبَنَّكُمْ أَجْمَعِينَ

    "Lalle ne, inã karkãtse hannãyenku da ƙafãfunku daga sãɓãni, sa'an nan kuma, haƙĩƙa, inã tsĩre, ku gabã ɗaya."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 124 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  38. 125

    قَالُوٓا۟ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ

    Suka ce: "Lalle ne mu, zuwa ga Ubangijinmu, mãsu jũyãwa ne."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 125 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  39. 126

    وَمَا تَنقِمُ مِنَّآ إِلَّآ أَنْ ءَامَنَّا بِـَٔايَـٰتِ رَبِّنَا لَمَّا جَآءَتْنَا ۚ رَبَّنَآ أَفْرِغْ عَلَيْنَا صَبْرًا وَتَوَفَّنَا مُسْلِمِينَ

    "Kuma bã ka zargin kõme daga gare mu fãce dõmin mun yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinmu a lõkacin da suka zõ mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana munã Musulmai![1] "

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Musulmi shi ne wanda ya sallama kansa ga hukunce-hukuncen Allah waɗanda wani Annabin Allah ya zõ da su, a cikin zãmaninsa. Sabõda haka ma'anar Musulmi shi ne mai sallamãwa ga hukuncin Allah, a kõwane zãmani, tun daga Ãdamu har zuwa Rãnar Ƙiyãma. Sai dai wannan al'umma ta Muhammadu tã keɓanta da sũnan Musulmi, addinin kuma da sũnan Musulunci.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 126 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  40. 127

    وَقَالَ ٱلْمَلَأُ مِن قَوْمِ فِرْعَوْنَ أَتَذَرُ مُوسَىٰ وَقَوْمَهُۥ لِيُفْسِدُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ وَيَذَرَكَ وَءَالِهَتَكَ ۚ قَالَ سَنُقَتِّلُ أَبْنَآءَهُمْ وَنَسْتَحْىِۦ نِسَآءَهُمْ وَإِنَّا فَوْقَهُمْ قَـٰهِرُونَ

    Kuma mashawarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Shin, zã ka bar Mũsã da mutãnensa dõmin su yi ɓarna a cikin ƙasa, kuma ya bar ka, kai da gumãkanka?" Ya ce: "Zã mu yayyanka ɗiyansu maza kuma mu rãya mãtansu; kuma lalle ne mũ, a bisa gare su, marinjãya ne."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 127 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  41. 128

    قَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِ ٱسْتَعِينُوا۟ بِٱللَّهِ وَٱصْبِرُوٓا۟ ۖ إِنَّ ٱلْأَرْضَ لِلَّهِ يُورِثُهَا مَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦ ۖ وَٱلْعَـٰقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ

    Mũsã ya ce wa mutãnensa:[1] "Ku nẽmi taimako da Allah, kuma ku yi haƙuri; Lalle ne ƙasa ta Allah ce, Yãna gãdar da ita ga wanda Yake so daga bãyinSa, kuma ãƙiba ta mãsu taƙawa ce."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Maganar Mũsã ga Banĩ Isrã'ila tã nũna cewa sun ga azãbar ta yi musu yawa, har sun fãra zargin Mũsã da cewa ya sabbaba musu tsananin fitinar, da zõwarsa. Shi kuma ya lallãshe su da cewa, "Kõme ya yi tsanani, to, sauƙin sa ya yi kusa.".

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 128 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  42. 129

    قَالُوٓا۟ أُوذِينَا مِن قَبْلِ أَن تَأْتِيَنَا وَمِنۢ بَعْدِ مَا جِئْتَنَا ۚ قَالَ عَسَىٰ رَبُّكُمْ أَن يُهْلِكَ عَدُوَّكُمْ وَيَسْتَخْلِفَكُمْ فِى ٱلْأَرْضِ فَيَنظُرَ كَيْفَ تَعْمَلُونَ

    Suka ce: "An cũtar da mu daga gabãnin ka zõ mana, kuma daga bãyan da kã zõ mana." Ya ce: "Akwai tsammãnin Ubangijinku, Ya halaka maƙiyanku, kuma Ya sanya ku, ku maye a cikin ƙasa, sa'an nan Ya dũba yadda kuke aikatãwa."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 129 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  43. 130

    وَلَقَدْ أَخَذْنَآ ءَالَ فِرْعَوْنَ بِٱلسِّنِينَ وَنَقْصٍ مِّنَ ٱلثَّمَرَٰتِ لَعَلَّهُمْ يَذَّكَّرُونَ

    Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun kãma mutãnen Fir'auna da tsananin shẽkaru (fari) da nakasa daga 'ya'yan itãce; Tsammãninsu sunã tunãwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 130 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  44. 131

    فَإِذَا جَآءَتْهُمُ ٱلْحَسَنَةُ قَالُوا۟ لَنَا هَـٰذِهِۦ ۖ وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌ يَطَّيَّرُوا۟ بِمُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓ ۗ أَلَآ إِنَّمَا طَـٰٓئِرُهُمْ عِندَ ٱللَّهِ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ

    Sa'an nan idan wani alhẽri ya jẽ musu, sai su ce: "Masĩfa ta sãme su, sai su yi shu'umci da Mũsã da wanda yake tãre da shi, To, shu'umcinsu a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawansu bã su sani!"

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 131 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  45. 132

    وَقَالُوا۟ مَهْمَا تَأْتِنَا بِهِۦ مِنْ ءَايَةٍ لِّتَسْحَرَنَا بِهَا فَمَا نَحْنُ لَكَ بِمُؤْمِنِينَ

    Kuma suka ce: "Kõ me ka zõ mana da shi daga ãyã, dõmin ka sihirce mu da ita, to, baza mu zama, sabõda kai, mãsu ĩmãni ba."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 132 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  46. 133

    فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمُ ٱلطُّوفَانَ وَٱلْجَرَادَ وَٱلْقُمَّلَ وَٱلضَّفَادِعَ وَٱلدَّمَ ءَايَـٰتٍ مُّفَصَّلَـٰتٍ فَٱسْتَكْبَرُوا۟ وَكَانُوا۟ قَوْمًا مُّجْرِمِينَ

    Sai Muka aika a kansu da cikõwa, da fãra, da ƙwarƙwata da kwãɗi, da jini; ãyõyi abũbuwan rarrabẽwa[1]; Sai suka kangare, kuma suka kasance mutãne mãsu laifi.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Ãyõyin da suka je musu a cikin lõkatai daban-daban dõmin a ja hankalinsu, kõ zã su yi ĩmãni. Kõwace ãyã tanã kwãna bakwai sunã wahala da ita, sa'an nan su rõƙi Mũsã ya yi addu'a a kuranye ta, sa'an nan a bãyan wani lõkaci sai su kõma wa kãfircinsu, kamar yadda ãyõyi mãsu biyar wannan suka bayyana.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 133 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  47. 134

    وَلَمَّا وَقَعَ عَلَيْهِمُ ٱلرِّجْزُ قَالُوا۟ يَـٰمُوسَى ٱدْعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَ ۖ لَئِن كَشَفْتَ عَنَّا ٱلرِّجْزَ لَنُؤْمِنَنَّ لَكَ وَلَنُرْسِلَنَّ مَعَكَ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ

    Kuma a lõkacin da masĩfa ta auku a kansu, sukan ce: "Yã Mũsã! Ka rõƙa mana Ubangijinka, sabõda abin da Ya yi alkwari a wurinka, lalle ne idan ka kau da azãbar daga barinmu, haƙĩƙa Munã ĩmãni sabõda kai, kuma munã sakin Banĩ Isrã'ila tĩre da kai."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 134 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  48. 135

    فَلَمَّا كَشَفْنَا عَنْهُمُ ٱلرِّجْزَ إِلَىٰٓ أَجَلٍ هُم بَـٰلِغُوهُ إِذَا هُمْ يَنكُثُونَ

    To, a lõkacin da Muka kuranye azãba daga barinsu zuwa a wani ajali wanda suke mãsu iske shi ne, sai gã su sunã warwarẽwa!

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 135 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  49. 136

    فَٱنتَقَمْنَا مِنْهُمْ فَأَغْرَقْنَـٰهُمْ فِى ٱلْيَمِّ بِأَنَّهُمْ كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا وَكَانُوا۟ عَنْهَا غَـٰفِلِينَ

    Sai Muka yi azãbar rãmuwa, daga gare su, sabõda haka Muka nutsar da su a cikin tẽku, dõmin lalle ne sũ, sun ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma sun kasance daga barinsu, gãfilai.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 136 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  50. 137

    وَأَوْرَثْنَا ٱلْقَوْمَ ٱلَّذِينَ كَانُوا۟ يُسْتَضْعَفُونَ مَشَـٰرِقَ ٱلْأَرْضِ وَمَغَـٰرِبَهَا ٱلَّتِى بَـٰرَكْنَا فِيهَا ۖ وَتَمَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ ٱلْحُسْنَىٰ عَلَىٰ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ بِمَا صَبَرُوا۟ ۖ وَدَمَّرْنَا مَا كَانَ يَصْنَعُ فِرْعَوْنُ وَقَوْمُهُۥ وَمَا كَانُوا۟ يَعْرِشُونَ

    Kuma Muka gãdar da mutãnen, waɗanda sun kasance anã raunana su, a gabacin ƙasa da yammacinta, wadda Muka sanya albarka a cikinta, kuma kalmar Ubangijinka mai kyau ta cika a kan Banĩ Isrã'ĩla, sabõda abin dasuka yi na haƙuri. Kuma Muka murtsuke abin da Fir'auna da mutãnensa suka kasance sunã sanã'antawa, da abin da suka kasance sunã shimfiɗãwa.[1]

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Wannan shi ne ƙarshen ƙissar faɗan gaskiya daga wajen Mũsã da ƙarya daga wajen Fir'auna da rundunarsa da dũkiyarsa. Haka dai ƙarya kõme duhunta, to, na banzane, a ƙarshe zã ta wãtsa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 137 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  51. 138

    وَجَـٰوَزْنَا بِبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱلْبَحْرَ فَأَتَوْا۟ عَلَىٰ قَوْمٍ يَعْكُفُونَ عَلَىٰٓ أَصْنَامٍ لَّهُمْ ۚ قَالُوا۟ يَـٰمُوسَى ٱجْعَل لَّنَآ إِلَـٰهًا كَمَا لَهُمْ ءَالِهَةٌ ۚ قَالَ إِنَّكُمْ قَوْمٌ تَجْهَلُونَ

    Kuma Muka ƙẽtarar da Banĩ Isra'ila ga tẽku, sai suka jẽ a kan wasu mutãne waɗanda sunã lizimta da ibãda a kan wasu gumãka, nãsu suka ce: "Yã Mũsã! Ka sanya mana wani abin bautawa kamar yadda suke da abũbuwan bautãwa "[1] Ya ce: "Lalle ne kũ, mutãne ne kunã jahilta."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Farkon faɗan ƙarya da gaskiya a tsakãnin Banĩ Isra'ila da Mũsã wajen son kõmawa ga al'ãdu da ƙãri a cikin Addini ta hanyar bidi'a.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 138 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  52. 139

    إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ مُتَبَّرٌ مَّا هُمْ فِيهِ وَبَـٰطِلٌ مَّا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

    "Lalle ne waɗannan, abin da suke a cikinsa halakakke ne, kuma abin da suka kasance sunã aikãtawa ƙarya ne."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 139 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  53. 140

    قَالَ أَغَيْرَ ٱللَّهِ أَبْغِيكُمْ إِلَـٰهًا وَهُوَ فَضَّلَكُمْ عَلَى ٱلْعَـٰلَمِينَ

    Ya ce: "Shin, wanin Allah nike nẽma muku ya zama abin bautãwa, alhãli kuwa Shĩ (Allah) Ya fĩfĩta ku a kan halittu?"

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 140 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  54. 141

    وَإِذْ أَنجَيْنَـٰكُم مِّنْ ءَالِ فِرْعَوْنَ يَسُومُونَكُمْ سُوٓءَ ٱلْعَذَابِ ۖ يُقَتِّلُونَ أَبْنَآءَكُمْ وَيَسْتَحْيُونَ نِسَآءَكُمْ ۚ وَفِى ذَٰلِكُم بَلَآءٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَظِيمٌ

    Kuma a lõkacin da Muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã tayã muku mugunyar azãba. sunã karkashe ɗiyanku maza, kuma sunã rãyar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa daga Ubangijinku,[1] Mai girma.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Lamĩrin Musulmi ne waɗanda ake yi wa magana yanzu a harshen Muhammadu, domin su wa'aztu da labarun mutanen farko.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 141 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  55. 142

    ۞ وَوَٰعَدْنَا مُوسَىٰ ثَلَـٰثِينَ لَيْلَةً وَأَتْمَمْنَـٰهَا بِعَشْرٍ فَتَمَّ مِيقَـٰتُ رَبِّهِۦٓ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً ۚ وَقَالَ مُوسَىٰ لِأَخِيهِ هَـٰرُونَ ٱخْلُفْنِى فِى قَوْمِى وَأَصْلِحْ وَلَا تَتَّبِعْ سَبِيلَ ٱلْمُفْسِدِينَ

    Kuma Muka yi wa'adi ga Mũsã da dare talãtin[1] kuma Muka cikã su da gõma, sai miƙatin Ubangijinsa ya cika dare arba'in. Kuma Mũsã ya ce wa ɗan'uwansa, Hãrũna: "Ka maye mini a cikin mutãnena, kuma ka gyãra, kuma kada ka bi hanyar mãsu fasãdi."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Ƙissõshin da ke tafe daga nan, suna nũna hani ga a ƙãra wani abu a cikin umarnin Allah. Kõwane irin ƙãri shi ne ake cewa bidi' a, kuma kõ dã an yi shi ne da nufin ƙwarai. Bidi'a tanã kãwo fitina ga mãsu ita.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 142 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  56. 143

    وَلَمَّا جَآءَ مُوسَىٰ لِمِيقَـٰتِنَا وَكَلَّمَهُۥ رَبُّهُۥ قَالَ رَبِّ أَرِنِىٓ أَنظُرْ إِلَيْكَ ۚ قَالَ لَن تَرَىٰنِى وَلَـٰكِنِ ٱنظُرْ إِلَى ٱلْجَبَلِ فَإِنِ ٱسْتَقَرَّ مَكَانَهُۥ فَسَوْفَ تَرَىٰنِى ۚ فَلَمَّا تَجَلَّىٰ رَبُّهُۥ لِلْجَبَلِ جَعَلَهُۥ دَكًّا وَخَرَّ مُوسَىٰ صَعِقًا ۚ فَلَمَّآ أَفَاقَ قَالَ سُبْحَـٰنَكَ تُبْتُ إِلَيْكَ وَأَنَا۠ أَوَّلُ ٱلْمُؤْمِنِينَ

    Kuma a lõkacin da Mũsã ya jẽ ga mĩkatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Mũsã ya ce: "Yã Ubangijina! Ka nũna mini in yi dũbi zuwa gare Ka!" Ya ce: "Bã zã ka gan Ni ba, kuma amma ka dũba zuwa ga dũtse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, zã ka gan Ni." Sa'an nan a lõkacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dũtsen, Ya sanyã shi niƙaƙƙe. Kuma Mũsã ya fãɗi sõmamme. To, a lõkacin da ya farka, ya ce: "TsarkinKa ya tabbata! Nã tũba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon mũminai."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 143 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  57. 144

    قَالَ يَـٰمُوسَىٰٓ إِنِّى ٱصْطَفَيْتُكَ عَلَى ٱلنَّاسِ بِرِسَـٰلَـٰتِى وَبِكَلَـٰمِى فَخُذْ مَآ ءَاتَيْتُكَ وَكُن مِّنَ ٱلشَّـٰكِرِينَ

    Ya ce: "Ya Mũsã! Lalle ne Nĩ, Nã zãɓe ka bisa ga mutãne da manzanciNa, kuma da maganãTa. Sabõda haka ka riƙi abin da Nã bã ka, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 144 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  58. 145

    وَكَتَبْنَا لَهُۥ فِى ٱلْأَلْوَاحِ مِن كُلِّ شَىْءٍ مَّوْعِظَةً وَتَفْصِيلًا لِّكُلِّ شَىْءٍ فَخُذْهَا بِقُوَّةٍ وَأْمُرْ قَوْمَكَ يَأْخُذُوا۟ بِأَحْسَنِهَا ۚ سَأُو۟رِيكُمْ دَارَ ٱلْفَـٰسِقِينَ

    Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa'azi da rarrabẽwa ga dukan kõwane abu: "Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutãnenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu;[1] zã Ni nũna muku gidan fãsiƙai."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Mafi kyau daga Attaura shi ne wanda yake bayyananne; watau kada a yi aiki da abin da yake bai bayyana ba, sai da abin da ya bayyana, bayan an yarda cewa dukansu daga Allah suke.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 145 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  59. 146

    سَأَصْرِفُ عَنْ ءَايَـٰتِىَ ٱلَّذِينَ يَتَكَبَّرُونَ فِى ٱلْأَرْضِ بِغَيْرِ ٱلْحَقِّ وَإِن يَرَوْا۟ كُلَّ ءَايَةٍ لَّا يُؤْمِنُوا۟ بِهَا وَإِن يَرَوْا۟ سَبِيلَ ٱلرُّشْدِ لَا يَتَّخِذُوهُ سَبِيلًا وَإِن يَرَوْا۟ سَبِيلَ ٱلْغَىِّ يَتَّخِذُوهُ سَبِيلًا ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا وَكَانُوا۟ عَنْهَا غَـٰفِلِينَ

    Zã Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, daga ãyõyiNa. Kuma idan sun ga dukan ãyã, bã zã su yi ĩmãni da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, bã zã su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, dõmin lalle ne su, sun ƙaryata da ãyõyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gãfilai.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 146 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  60. 147

    وَٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا وَلِقَآءِ ٱلْـَٔاخِرَةِ حَبِطَتْ أَعْمَـٰلُهُمْ ۚ هَلْ يُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

    Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu da gamuwa da Lãhira, ayyukansu sun ɓãci. Shin, ana saka musu, fãce da abin da suka kasance suna aikatãwa?

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 147 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  61. 148

    وَٱتَّخَذَ قَوْمُ مُوسَىٰ مِنۢ بَعْدِهِۦ مِنْ حُلِيِّهِمْ عِجْلًا جَسَدًا لَّهُۥ خُوَارٌ ۚ أَلَمْ يَرَوْا۟ أَنَّهُۥ لَا يُكَلِّمُهُمْ وَلَا يَهْدِيهِمْ سَبِيلًا ۘ ٱتَّخَذُوهُ وَكَانُوا۟ ظَـٰلِمِينَ

    Kuma mutãnen Mũsã suka riƙi maraƙi[1], jikin mutãne, yanã rũri, daga bãyan tafiyarsa, daga kãyan ƙawarsu. Shin, ba su ganĩ ba, cẽwa lalle ne shi, bã ya yi musu magana, kuma bã ya shiryar da su ga hanya, sun riƙa shi, kuma sun kasance mãsu zãlunci.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Riƙon maraƙi shi ne bauta masa. Shĩ maraƙin an yĩ shi ne da mundãyen ƙawarsu, yanã da jiki irin na mutãne, kuma yanã rũri kamar na shãnu. Bã shi yin magana. Sun bauta masa a bãyan tafiyar Mũsã, a cikin kwana gõma na ƙãrin mĩƙãtin.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 148 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  62. 149

    وَلَمَّا سُقِطَ فِىٓ أَيْدِيهِمْ وَرَأَوْا۟ أَنَّهُمْ قَدْ ضَلُّوا۟ قَالُوا۟ لَئِن لَّمْ يَرْحَمْنَا رَبُّنَا وَيَغْفِرْ لَنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلْخَـٰسِرِينَ

    Kuma a lõkacin da suka yi nadãma, kuma suka ga cẽwalalle ne sũ haƙĩƙa sun ɓace, suka ce: "Haƙĩƙa, idan UbangijinMu bai yi mana rahama ba, kuma Ya gãfarta mana, lalle ne munã kasancẽwa daga mãsu hasãra."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 149 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  63. 150

    وَلَمَّا رَجَعَ مُوسَىٰٓ إِلَىٰ قَوْمِهِۦ غَضْبَـٰنَ أَسِفًا قَالَ بِئْسَمَا خَلَفْتُمُونِى مِنۢ بَعْدِىٓ ۖ أَعَجِلْتُمْ أَمْرَ رَبِّكُمْ ۖ وَأَلْقَى ٱلْأَلْوَاحَ وَأَخَذَ بِرَأْسِ أَخِيهِ يَجُرُّهُۥٓ إِلَيْهِ ۚ قَالَ ٱبْنَ أُمَّ إِنَّ ٱلْقَوْمَ ٱسْتَضْعَفُونِى وَكَادُوا۟ يَقْتُلُونَنِى فَلَا تُشْمِتْ بِىَ ٱلْأَعْدَآءَ وَلَا تَجْعَلْنِى مَعَ ٱلْقَوْمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ

    Kuma a lõkacin da Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa, yanã mai fushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Tir da abin da kuka yi mini wakilci, a bãyanã! Shin, kun nẽmi gaggawar umurnin Ubangijinku ne?" Kuma ya jefar da Allunan, kuma ya yi riƙo ga kan ɗan'uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Ya ce: "Yã ɗan'uwata! Lalle ne mutãnen, sun ɗauke ni mai rauni, kuma sun yi kusa su kashe ni, sabõda haka kada ka dãrantar da maƙiya game da ni, kuma kada ka sanya ni tãre da mutãne Azzãlumai."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 150 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  64. 151

    قَالَ رَبِّ ٱغْفِرْ لِى وَلِأَخِى وَأَدْخِلْنَا فِى رَحْمَتِكَ ۖ وَأَنتَ أَرْحَمُ ٱلرَّٰحِمِينَ

    Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka gãfarta mini, nĩ da ɗan'uwana, kuma Ka shigar da mu a cikin rahamarKa, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama!"

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 151 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  65. 152

    إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُوا۟ ٱلْعِجْلَ سَيَنَالُهُمْ غَضَبٌ مِّن رَّبِّهِمْ وَذِلَّةٌ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُفْتَرِينَ

    Lalle ne waɗanda suka riƙi maraƙin, wani fushi daga Ubangijinsu da wani walãkanci a cikin rãyuwar dũniya, zã su sãme su: Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu ƙirƙira ƙarya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 152 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  66. 153

    وَٱلَّذِينَ عَمِلُوا۟ ٱلسَّيِّـَٔاتِ ثُمَّ تَابُوا۟ مِنۢ بَعْدِهَا وَءَامَنُوٓا۟ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعْدِهَا لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ

    Kuma waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka, sa'an nan suka tũba daga bãyansu kuma sukayi ĩmãni, lalle ne Ubangijinka daga bãyansu, haƙĩƙa, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 153 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  67. 154

    وَلَمَّا سَكَتَ عَن مُّوسَى ٱلْغَضَبُ أَخَذَ ٱلْأَلْوَاحَ ۖ وَفِى نُسْخَتِهَا هُدًى وَرَحْمَةٌ لِّلَّذِينَ هُمْ لِرَبِّهِمْ يَرْهَبُونَ

    Kuma a lõkacin da fushin ya kwanta daga barin Mũsã, sai ya riƙi Allunan, kuma a cikin kwafensu akwai shiriya da rahama ga waɗanda suke sũ, ga Ubangijinsu, mãsu jin tsõro ne.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 154 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  68. 155

    وَٱخْتَارَ مُوسَىٰ قَوْمَهُۥ سَبْعِينَ رَجُلًا لِّمِيقَـٰتِنَا ۖ فَلَمَّآ أَخَذَتْهُمُ ٱلرَّجْفَةُ قَالَ رَبِّ لَوْ شِئْتَ أَهْلَكْتَهُم مِّن قَبْلُ وَإِيَّـٰىَ ۖ أَتُهْلِكُنَا بِمَا فَعَلَ ٱلسُّفَهَآءُ مِنَّآ ۖ إِنْ هِىَ إِلَّا فِتْنَتُكَ تُضِلُّ بِهَا مَن تَشَآءُ وَتَهْدِى مَن تَشَآءُ ۖ أَنتَ وَلِيُّنَا فَٱغْفِرْ لَنَا وَٱرْحَمْنَا ۖ وَأَنتَ خَيْرُ ٱلْغَـٰفِرِينَ

    Kuma Mũsã ya zãɓi mutãnensa, namiji saba'in dõmin miƙãtinMu. To, a lõkacin da tsãwa ta kãma su, ya ce: "Yã Ubangijina! Dã Kã so, dã Kã halakar da su daga gabãni, sũ da ni. Shin zã Kahalaka mu, sabõda abin da wãwãyen daga gare mu suka aikata? Ba ta zama ba fãce fitinarKa Kanã ɓatarwa, da ita, wanda Kake so kuma kanã shiryarwa da ita, wanda Kake so; Kai ne Majiɓincinmu. Sai Ka gãfarta mana; kuma Ka yi mana rahama, alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãfara."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 155 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  69. 156

    ۞ وَٱكْتُبْ لَنَا فِى هَـٰذِهِ ٱلدُّنْيَا حَسَنَةً وَفِى ٱلْـَٔاخِرَةِ إِنَّا هُدْنَآ إِلَيْكَ ۚ قَالَ عَذَابِىٓ أُصِيبُ بِهِۦ مَنْ أَشَآءُ ۖ وَرَحْمَتِى وَسِعَتْ كُلَّ شَىْءٍ ۚ فَسَأَكْتُبُهَا لِلَّذِينَ يَتَّقُونَ وَيُؤْتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلَّذِينَ هُم بِـَٔايَـٰتِنَا يُؤْمِنُونَ

    "Kuma Ka rubũta mana alhẽri a cikin wannan dũniya, kuma a cikin Lãhira. Lalle ne mũ, mun tũba zuwa gare Ka." Ya ce: "AzãbaTa Inã sãmu, da ita, wanda Nike so, kuma rahamaTa, ta yalwaci dukan kõme. Sa'an nan zã Ni rubũta ta ga waɗanda suke yin taƙawa, kuma sunã bãyar da zakka, da waɗanda suke, game da ãyõyin Mu mũminai ne."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 156 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  70. 157

    ٱلَّذِينَ يَتَّبِعُونَ ٱلرَّسُولَ ٱلنَّبِىَّ ٱلْأُمِّىَّ ٱلَّذِى يَجِدُونَهُۥ مَكْتُوبًا عِندَهُمْ فِى ٱلتَّوْرَىٰةِ وَٱلْإِنجِيلِ يَأْمُرُهُم بِٱلْمَعْرُوفِ وَيَنْهَىٰهُمْ عَنِ ٱلْمُنكَرِ وَيُحِلُّ لَهُمُ ٱلطَّيِّبَـٰتِ وَيُحَرِّمُ عَلَيْهِمُ ٱلْخَبَـٰٓئِثَ وَيَضَعُ عَنْهُمْ إِصْرَهُمْ وَٱلْأَغْلَـٰلَ ٱلَّتِى كَانَتْ عَلَيْهِمْ ۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ بِهِۦ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَٱتَّبَعُوا۟ ٱلنُّورَ ٱلَّذِىٓ أُنزِلَ مَعَهُۥٓ ۙ أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُفْلِحُونَ

    "Waɗanda suke sunã bin Manzo[1], Annabi, Ummiyyi wanda suke sãmun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla.yanã umurnin su da alhẽri, kuma yana hana su daga barin abin da bã a so; kuma yana halatta musu abũ- buwa masu dadi, kuma yana haramtarwar mũnana a kansu. Kuma yanã kãyar da nauyinsu daga barinsu, da ƙuƙummai waɗannan da suka kasance a kansu. To, wa- ɗanda suka yi ĩmãni da shi kuma suka ƙarfafa shi, kuma suka tai- make shi, kuma suka bi haske wan- da aka saukar tãre da shi, waɗan- nan ne mãsu cin nasara.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Bayãnin bisharar Attaura da Linjĩla game da Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi. Kuma bishãrar da Allah ya gaya wa Annabi Mũsã wurin Miƙatinsa tãre da mutãne saba'in, dõmin maganar ɗinke take.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 157 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  71. 158

    قُلْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّى رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيْكُمْ جَمِيعًا ٱلَّذِى لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۖ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْىِۦ وَيُمِيتُ ۖ فَـَٔامِنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ٱلنَّبِىِّ ٱلْأُمِّىِّ ٱلَّذِى يُؤْمِنُ بِٱللَّهِ وَكَلِمَـٰتِهِۦ وَٱتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ

    Ka ce: "Yã kũ mutãne![1] Lalle ne nĩ manzon Allah nezuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni daAllah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Mutãne a nan, anã nufin Yahũdu da wasunsu. Anã kiran su zuwa ga abin da Attaura ta yi musu bishãra da zuwansa,a cikin sifõfin da ta sifantã Shi da su.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 158 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  72. 159

    وَمِن قَوْمِ مُوسَىٰٓ أُمَّةٌ يَهْدُونَ بِٱلْحَقِّ وَبِهِۦ يَعْدِلُونَ

    Kuma daga mutãnen[1] Mũsã akwai al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke yin ãdalci.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Anã nũna cewa duka yadda mutãne suka ɓãci, bã zã a rasa na kirki a cikin su ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 159 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  73. 160

    وَقَطَّعْنَـٰهُمُ ٱثْنَتَىْ عَشْرَةَ أَسْبَاطًا أُمَمًا ۚ وَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ إِذِ ٱسْتَسْقَىٰهُ قَوْمُهُۥٓ أَنِ ٱضْرِب بِّعَصَاكَ ٱلْحَجَرَ ۖ فَٱنۢبَجَسَتْ مِنْهُ ٱثْنَتَا عَشْرَةَ عَيْنًا ۖ قَدْ عَلِمَ كُلُّ أُنَاسٍ مَّشْرَبَهُمْ ۚ وَظَلَّلْنَا عَلَيْهِمُ ٱلْغَمَـٰمَ وَأَنزَلْنَا عَلَيْهِمُ ٱلْمَنَّ وَٱلسَّلْوَىٰ ۖ كُلُوا۟ مِن طَيِّبَـٰتِ مَا رَزَقْنَـٰكُمْ ۚ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَـٰكِن كَانُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ

    Kuma Muka yayyanka su sibɗi gõma shã biyu, al'ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã a lõkacin da mutãnensasuka nẽme shi, ga shãyarwa, cẽwa: "Ka dõki dũtsen[1] da sandarka."Sai marmaro gõma shã biyu suka ɓuɓɓuga daga gare shi: Lalle ne kõwaɗanne mutãne sun san mashãyarsu. Kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kansu."Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku."Kuma ba su zãluncẽ Mu ba; kuma amma rãyukansu suke zãlunta.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Watau dũtsen da ya gudu da tufafinsa ne a lõkacin da yake yin wanka dõmin a nũna wa Banĩ Isra'ila, waɗanda suka sõke shi da gwaiwa, cewa lãfiya lau yake. Kuma aka umurce shi da ɗaukar dũtsen, kuma yanzu aka umurce shi da ya dõke shi dõmin ruwa ya fito sabõda shansu.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 160 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  74. 161

    وَإِذْ قِيلَ لَهُمُ ٱسْكُنُوا۟ هَـٰذِهِ ٱلْقَرْيَةَ وَكُلُوا۟ مِنْهَا حَيْثُ شِئْتُمْ وَقُولُوا۟ حِطَّةٌ وَٱدْخُلُوا۟ ٱلْبَابَ سُجَّدًا نَّغْفِرْ لَكُمْ خَطِيٓـَٔـٰتِكُمْ ۚ سَنَزِيدُ ٱلْمُحْسِنِينَ

    Kuma a lõkacin da aka ce masu: "Ku zauna ga wannan alƙarya[1], kuma ku ci daga gare ta, inda kuka so, kuma ku ce: 'Saryarwa,' kuma ku shiga kõfa kuna mãsu sujada; Mu gãfarta muku laifuffukanku, kuma zã Mu ɗãra wa mãsu kyautatãwa."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Alƙaryar ita ce Baitil Maƙdis, bisa shugabancin Yũsha'u. 'Saryarwa,' watau a saryar mana da zunubinmu, yã Allah!, 'Shiga ƙõfa da sujada,' watau da tawãli'u.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 161 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  75. 162

    فَبَدَّلَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ مِنْهُمْ قَوْلًا غَيْرَ ٱلَّذِى قِيلَ لَهُمْ فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِجْزًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ بِمَا كَانُوا۟ يَظْلِمُونَ

    Sai waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, suka musanya magana[1] watar wadda aka ce musu, sai Muka aika azãba a kansu, daga sama, sabõda abin da suka kasance sunã yi na zãlunci.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Suka musanya hiɗɗa da hinɗa: watau alkama. (Aya ta 161) Sai aka saukar da azãba a kansu, sabõda haka wannan yã nũna cewa Allah ba ya son a musanya addininSa da kõme, sai dai mutum ya yi shi kamar yadda ya zo masa. Musanyawar umarnin, yãƙi ne a tsakãnin gaskiya da ƙarya. Ma'anar hiɗɗa ita ce kãyar da zunubi.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 162 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  76. 163

    وَسْـَٔلْهُمْ عَنِ ٱلْقَرْيَةِ ٱلَّتِى كَانَتْ حَاضِرَةَ ٱلْبَحْرِ إِذْ يَعْدُونَ فِى ٱلسَّبْتِ إِذْ تَأْتِيهِمْ حِيتَانُهُمْ يَوْمَ سَبْتِهِمْ شُرَّعًا وَيَوْمَ لَا يَسْبِتُونَ ۙ لَا تَأْتِيهِمْ ۚ كَذَٰلِكَ نَبْلُوهُم بِمَا كَانُوا۟ يَفْسُقُونَ

    Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga tẽku, a lõkacin da suke ƙẽtare haddi a cikin Asabar, a lõkacin da kĩfãyensu, suke je musu a rãnar Asabar[1] ɗinsu jẽre. Kuma a rãnar da ba su yi Asabar ba, bã su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Wata alƙarya anã ce da ita Ailata a bãkin gãɓar Bahr Al Kulzum a zãmanin Dãwũda, Allah ya umurce su a kan harshen Dãwũda su riƙi Jumma'a rãnar ĩdi, su yanke aiki a ciki, dõmin ibãda, sai suka ƙi Jumma'a suka zãɓi Asabar, ma'anarsa yankewa. To, sai Allah ya tsananta musu, Ya hana su farautar kĩfi a rãnar Asabar, Ya halatta musu shi, a sauran kwãnukan mãko. Sai a rãnar Asabar, su sãmi kĩfi wani kan wani, amma sauran kwanuka bã su sãmunsa haka. Sai Iblis ya sanar da su ga su aikata matarar ruwa a gefen tekun, a rãnar Asabar, su bũde kifi ya shiga su rufe, har rãnar Lahadi su kãma. Sai garin ya kasu uku: kashi ɗaya suka yi farauta, wasu suka hana, sũ kuma suka yi gãru a tsakãninsu da mãsu yi, na uku ba su yi farautar ba kuma ba su hana ba. A bãyan 'yan kwãnaki sai aka mayar da mãsu farautar birai, sa'an nan suka mutu.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 163 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  77. 164

    وَإِذْ قَالَتْ أُمَّةٌ مِّنْهُمْ لِمَ تَعِظُونَ قَوْمًا ۙ ٱللَّهُ مُهْلِكُهُمْ أَوْ مُعَذِّبُهُمْ عَذَابًا شَدِيدًا ۖ قَالُوا۟ مَعْذِرَةً إِلَىٰ رَبِّكُمْ وَلَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ

    Kuma a lõkacin da wata al'umma daga gare su ta ce: "Don me kuke yin wa'azi ga mutãne waɗanda Allah Yake Mai halaka su kõ kuwa Mai yi musu azãba, azãba mai tsanani?" Suka ce: "Dõmin nẽman hanzari zuwa ga Ubangijinku, kuma tsammãninsu, sunã yin taƙawa."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 164 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  78. 165

    فَلَمَّا نَسُوا۟ مَا ذُكِّرُوا۟ بِهِۦٓ أَنجَيْنَا ٱلَّذِينَ يَنْهَوْنَ عَنِ ٱلسُّوٓءِ وَأَخَذْنَا ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ بِعَذَابٍۭ بَـِٔيسٍۭ بِمَا كَانُوا۟ يَفْسُقُونَ

    To, a lõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, Mun tsĩrar da waɗanda suke hani daga cũta, kuma Muka kãma waɗanda suka yi zãlunci, da azãba mai tsanani dõmin abin da suka kasance sunã yi, na fasiƙanci.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 165 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  79. 166

    فَلَمَّا عَتَوْا۟ عَن مَّا نُهُوا۟ عَنْهُ قُلْنَا لَهُمْ كُونُوا۟ قِرَدَةً خَـٰسِـِٔينَ

    Sa'an nan a lõkacin da suka yi girman kai daga barin abin da aka hana su daga gare shi, Muka ce musu: "Ku kasance birai ƙasƙantattu."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 166 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  80. 167

    وَإِذْ تَأَذَّنَ رَبُّكَ لَيَبْعَثَنَّ عَلَيْهِمْ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ مَن يَسُومُهُمْ سُوٓءَ ٱلْعَذَابِ ۗ إِنَّ رَبَّكَ لَسَرِيعُ ٱلْعِقَابِ ۖ وَإِنَّهُۥ لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ

    Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, lalle ne, zã Ya aika a kansu (Yahũd), zuwa, Rãnar¡iyãma, wanda zai ɗanɗana musu mummunar azãba, lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai gaggawar uƙũba ne, kuma shĩ haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 167 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  81. 168

    وَقَطَّعْنَـٰهُمْ فِى ٱلْأَرْضِ أُمَمًا ۖ مِّنْهُمُ ٱلصَّـٰلِحُونَ وَمِنْهُمْ دُونَ ذَٰلِكَ ۖ وَبَلَوْنَـٰهُم بِٱلْحَسَنَـٰتِ وَٱلسَّيِّـَٔاتِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ

    Kuma Muka yayyanka su, a cikin ƙasa, al'ummõmi, daga gare su akwai sãlihai, kuma daga gare su akwai wanda bã haka ba. Muka jarrabe su da abũbuwan alhẽri da na musĩfa; Tsammãninsu, sunã kõmõwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 168 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  82. 169

    فَخَلَفَ مِنۢ بَعْدِهِمْ خَلْفٌ وَرِثُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ يَأْخُذُونَ عَرَضَ هَـٰذَا ٱلْأَدْنَىٰ وَيَقُولُونَ سَيُغْفَرُ لَنَا وَإِن يَأْتِهِمْ عَرَضٌ مِّثْلُهُۥ يَأْخُذُوهُ ۚ أَلَمْ يُؤْخَذْ عَلَيْهِم مِّيثَـٰقُ ٱلْكِتَـٰبِ أَن لَّا يَقُولُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلْحَقَّ وَدَرَسُوا۟ مَا فِيهِ ۗ وَٱلدَّارُ ٱلْـَٔاخِرَةُ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ

    Sai wasu' yan bãya suka maye daga bãyansu, sun gaji Littãfin, sunã karɓar sifar[1] wannan ƙasƙantacciya, sunã cẽwa: "Zã a gãfarta mana. "Iadan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karɓe ta. Shin, ba a karɓi alkawarin Littãfi ba a kansu cẽwa kada su faɗa ga Allah, fãce gaskiya, alhãli kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma Gidan Lãhira ne mafi alhẽriga wanda ya yi taƙawa? Shin, bã zã ku hankalta ba?

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Sifar ƙasƙantacciya ita ce kãyan dũniya na haram, kamar rashawa. An kira ta sifa dõmin bã aba ce mai tsayuwa da kanta ba, kuma bã sifar abin kirki ba, sai dai abin da yake halaka ne nan da nan. Tãke gaskiya faɗa ne da Addini, watau yaƙi a tsakãnin gaskiya da ƙarya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 169 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  83. 170

    وَٱلَّذِينَ يُمَسِّكُونَ بِٱلْكِتَـٰبِ وَأَقَامُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجْرَ ٱلْمُصْلِحِينَ

    Kuma waɗanda suke riƙẽwa da laittãfi kuma suka tsayar da salla, lalle ne Mũ, bã Mu tõzarta lãdar mãsu gyãrãwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 170 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  84. 171

    ۞ وَإِذْ نَتَقْنَا ٱلْجَبَلَ فَوْقَهُمْ كَأَنَّهُۥ ظُلَّةٌ وَظَنُّوٓا۟ أَنَّهُۥ وَاقِعٌۢ بِهِمْ خُذُوا۟ مَآ ءَاتَيْنَـٰكُم بِقُوَّةٍ وَٱذْكُرُوا۟ مَا فِيهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ

    Kuma a lõkacin da muka ɗaukaka dũtse[1] sama da su, kumar dai shi girgije ne, kuma suka haƙƙaƙe, lalle ne shĩ, mai fãɗuwa ne a gare su, (aka ce): "Ku karɓi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammãninku kunã yin taƙawa."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] A lõkacin da Mũsã ya karanta wa Banĩ Isra'ila Attaura da hukunce-hukuncen da suke a cikinta, mãsu wuya gare su, sai suka ƙi yarda da ita. Allah Ya yanka dũtse daidai da garinsu, Ya ɗaukaka shi a kansu, ko su yi aiki da ita kõ ya fãɗa a kansu. Daga nan idan suna salla, sai su yi sujada da rabin gõshi a kan tsãgin hagu, sunã kallon dũtsen. Kuma yin sujada a haka ya zama sunnarsu har yanzu. Watau bã a iya tsare gaskiya daga yãƙin ƙarya sai an yi amfãni da wani ƙarfi.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 171 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  85. 172

    وَإِذْ أَخَذَ رَبُّكَ مِنۢ بَنِىٓ ءَادَمَ مِن ظُهُورِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَأَشْهَدَهُمْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمْ أَلَسْتُ بِرَبِّكُمْ ۖ قَالُوا۟ بَلَىٰ ۛ شَهِدْنَآ ۛ أَن تَقُولُوا۟ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ إِنَّا كُنَّا عَنْ هَـٰذَا غَـٰفِلِينَ

    Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya karɓi (alkawari) daga ɗiyan Ãdam, daga bãyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rãyukansu, (Ya ce): "Shin, bã Nĩ ne Ubangijinku ba?" Suka ce: "Na'am! Mun yi shaida!" (ya ce): "Kada ku ce a Rãnar Kiyãma: Lalle ne mũ, daga wannan, gafalallu ne."[1]

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Watau kada ku ce ba ku san wannan alkawari ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 172 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  86. 173

    أَوْ تَقُولُوٓا۟ إِنَّمَآ أَشْرَكَ ءَابَآؤُنَا مِن قَبْلُ وَكُنَّا ذُرِّيَّةً مِّنۢ بَعْدِهِمْ ۖ أَفَتُهْلِكُنَا بِمَا فَعَلَ ٱلْمُبْطِلُونَ

    Kõ kuwa ku ce: "Abin sani kawai, ubanninmu suka yi shirki daga farko, kuma mũ, mun kasance zũriya daga bãyansu. Shin fa, Kanã halaka mu, sabõda abin da mãsu ɓãtãwa suka aikata?"

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 173 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  87. 174

    وَكَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلْـَٔايَـٰتِ وَلَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ

    Kuma kamar haka Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki; tsammãninsu, sunã kõmõwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 174 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  88. 175

    وَٱتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ ٱلَّذِىٓ ءَاتَيْنَـٰهُ ءَايَـٰتِنَا فَٱنسَلَخَ مِنْهَا فَأَتْبَعَهُ ٱلشَّيْطَـٰنُ فَكَانَ مِنَ ٱلْغَاوِينَ

    Ka karanta a kansu lãbãrin wanda Muka kãwo masa[1] ãyõyinMu, sai ya sãɓule daga gare su, sai shaidan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Asalin ƙissar anã cewa daga Bil'amu ɗan Bã'ura ne; Allah ya bã shi ilmi, sai ya bar ilmin. Yanã daga cikin mãlaman Banĩ Isrã' ĩla, yã kasance wanda ake karɓar addu'arsa, sunã gabatar da shi a cikin tsanance-tsanance, sai Mũsã ya aike shi zuwa ga sarkin Madyana ya kirãye shi zuwa ga Allah. Sai sarkin ya yanka masa ƙasa, ya bã shi, sai ya bi addinin sarkin, ya bar addinin Mũsã. Ya zama misãli ga duk mãlamin da bai yi aiki da ilminsa ba. Idan mãlami ya halaka, to, yã fi Shaiɗan sharri dõmin haka shaiɗan yake binsa wajen taimakon ƙarya a kan gaskiya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 175 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  89. 176

    وَلَوْ شِئْنَا لَرَفَعْنَـٰهُ بِهَا وَلَـٰكِنَّهُۥٓ أَخْلَدَ إِلَى ٱلْأَرْضِ وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ ۚ فَمَثَلُهُۥ كَمَثَلِ ٱلْكَلْبِ إِن تَحْمِلْ عَلَيْهِ يَلْهَثْ أَوْ تَتْرُكْهُ يَلْهَث ۚ ذَّٰلِكَ مَثَلُ ٱلْقَوْمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا ۚ فَٱقْصُصِ ٱلْقَصَصَ لَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ

    Kuma dã Mun so, da Mun ɗaukakã shi da su, kuma amma shĩ, ya nẽmi dawwama a cikin ƙasa, kuma ya bi son zũciyarsa. To, misãlinsa kamar misãlin kare ne, idan ka yi ɗauki a kansa ya yi lallage, kõ kuwa ka bar shi sai ya yi lallage, wannan ne misãlin mutãne waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu: Ka jẽranta karãtun lãbãrun; tsammãninsu sunã tunãni.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 176 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  90. 177

    سَآءَ مَثَلًا ٱلْقَوْمُ ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا وَأَنفُسَهُمْ كَانُوا۟ يَظْلِمُونَ

    Tir da zama misãli, mutãnen da suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma kansu suka kasance sunã zãlunta.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 177 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  91. 178

    مَن يَهْدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلْمُهْتَدِى ۖ وَمَن يُضْلِلْ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْخَـٰسِرُونَ

    Wanda[1] Allah Ya shiryar, to, shĩ ne Mai shiryuwa, kuma wanda Ya ɓatar, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] An sifanta Musulmi da abin da aka sifanta Yahũdu da shi cewa a cikinsu akwai na kirki, kuma akwai miyãgu, dõmin yãƙi a tsakãnin gaskiya da ƙarya ya dõge.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 178 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  92. 179

    وَلَقَدْ ذَرَأْنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيرًا مِّنَ ٱلْجِنِّ وَٱلْإِنسِ ۖ لَهُمْ قُلُوبٌ لَّا يَفْقَهُونَ بِهَا وَلَهُمْ أَعْيُنٌ لَّا يُبْصِرُونَ بِهَا وَلَهُمْ ءَاذَانٌ لَّا يَسْمَعُونَ بِهَآ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ كَٱلْأَنْعَـٰمِ بَلْ هُمْ أَضَلُّ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْغَـٰفِلُونَ

    Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sabõda Jahannama, mãsu yawa daga aljannu da mutãne, sunã da zukãta, ba su fahimta da su, kuma sunã da idãnu, bã su gani da su, kuma sunã da kunnuwa, ba su ji da su; waɗancan kamar bisãshe suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa; Waɗancan sũ ne gafalallu.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 179 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  93. 180

    وَلِلَّهِ ٱلْأَسْمَآءُ ٱلْحُسْنَىٰ فَٱدْعُوهُ بِهَا ۖ وَذَرُوا۟ ٱلَّذِينَ يُلْحِدُونَ فِىٓ أَسْمَـٰٓئِهِۦ ۚ سَيُجْزَوْنَ مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

    Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau.[1] Sai ku rõƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa: zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Waɗanda suke rõƙon Allah bã da sũnãyenSa mãsu kyau ba, sũ ne aka sifanta da dabbõbi, har dabbõbi sun fi su, dõmin dabba tanã gudun abinda yake cũtar ta, amma sũ ba su san abin da yake cũtar su ba, balle su guje shi. Kuma anã fahimtar cewa bã a rõƙon Allah da wani sũna Nãsa, idan bai kasance a cikin sanayenSa mãsu kyau ba, sai fa idan ya zama a dunƙule ne, kamar a ce, "Ya Allah inã rõƙonKa da sũnayenKa waɗanda na sani da waɗanda ban sani ba," dõmin Hadĩsi ya nũna a yi haka. Kiran Allah bã da sunãyenSa mãsu kyau ba yana cikin yãƙi a tsakãnin ƙarya da gaskiya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 180 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  94. 181

    وَمِمَّنْ خَلَقْنَآ أُمَّةٌ يَهْدُونَ بِٱلْحَقِّ وَبِهِۦ يَعْدِلُونَ

    Kuma daga waɗanda Muka halitta akwai wata al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma, da ita suke yin ãdalci.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 181 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  95. 182

    وَٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا سَنَسْتَدْرِجُهُم مِّنْ حَيْثُ لَا يَعْلَمُونَ

    Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 182 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  96. 183

    وَأُمْلِى لَهُمْ ۚ إِنَّ كَيْدِى مَتِينٌ

    Kuma Inã yi musu jinkiri, lalle ne kaidĩNa, mai ƙarfi ne.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 183 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  97. 184

    أَوَلَمْ يَتَفَكَّرُوا۟ ۗ مَا بِصَاحِبِهِم مِّن جِنَّةٍ ۚ إِنْ هُوَ إِلَّا نَذِيرٌ مُّبِينٌ

    Shin, ba su yi tunĩni ba, cẽwa bãbu wata hauka ga ma'abucinsu?[1] shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Watau, Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bã ya da hauka sai hankali, sabõda haka mãsu yin addini da hauka, kamar mãsu da'awar tasawwufi, ƙarya suke yi, sunã faɗa ne da gaskiya. Kuma sũkar mai wa'azi da sũnãye faɗa da gaskiya ne.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 184 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  98. 185

    أَوَلَمْ يَنظُرُوا۟ فِى مَلَكُوتِ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا خَلَقَ ٱللَّهُ مِن شَىْءٍ وَأَنْ عَسَىٰٓ أَن يَكُونَ قَدِ ٱقْتَرَبَ أَجَلُهُمْ ۖ فَبِأَىِّ حَدِيثٍۭ بَعْدَهُۥ يُؤْمِنُونَ

    Shin, ba su yi dũbi ba a cikin mulkin sammai da ƙasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kõme, kuma akwai tsammãni kasancewar ajalinsu, haƙĩƙa, ya kusanta? To, da wane lãbãri a bãyansa suke yin ĩmãni?

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 185 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  99. 186

    مَن يُضْلِلِ ٱللَّهُ فَلَا هَادِىَ لَهُۥ ۚ وَيَذَرُهُمْ فِى طُغْيَـٰنِهِمْ يَعْمَهُونَ

    Wanda Allah Ya ɓatar to bãbu mai shiryarwa a gare shi: kuma Yanã barin su, a cikin ɓatarsu sunã ɗimuwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 186 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  100. 187

    يَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَىٰهَا ۖ قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِندَ رَبِّى ۖ لَا يُجَلِّيهَا لِوَقْتِهَآ إِلَّا هُوَ ۚ ثَقُلَتْ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ لَا تَأْتِيكُمْ إِلَّا بَغْتَةً ۗ يَسْـَٔلُونَكَ كَأَنَّكَ حَفِىٌّ عَنْهَا ۖ قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِندَ ٱللَّهِ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ

    Sunã tambayar ka[1] daga Sa'a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Bãbu mai bayyana ta ga lõkacinta fãce shĩ Tã yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Bã zã ta zo muku ba fãce kwatsam." sunã tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutãne bã su sani."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Tambayar abin da Allah bai bayyana shi ba, kamar Rãnar Tãshin Kiyãma, yãƙi ne a tsakanin ƙarya da gaskiya. cewa wani mutum yã san gaibi ko yanã iya kãwo alheri kõ ya tunkuɗe wani sharri, ƙarya ne, kuma faɗã da gaskiya ne.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 187 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  101. 188

    قُل لَّآ أَمْلِكُ لِنَفْسِى نَفْعًا وَلَا ضَرًّا إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُ ۚ وَلَوْ كُنتُ أَعْلَمُ ٱلْغَيْبَ لَٱسْتَكْثَرْتُ مِنَ ٱلْخَيْرِ وَمَا مَسَّنِىَ ٱلسُّوٓءُ ۚ إِنْ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٌ وَبَشِيرٌ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ

    Ka ce: "Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, fãceabin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhẽri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba fĩce mai gargaɗi, kumamai bãyar da bishãra ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 188 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  102. 189

    ۞ هُوَ ٱلَّذِى خَلَقَكُم مِّن نَّفْسٍ وَٰحِدَةٍ وَجَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَا لِيَسْكُنَ إِلَيْهَا ۖ فَلَمَّا تَغَشَّىٰهَا حَمَلَتْ حَمْلًا خَفِيفًا فَمَرَّتْ بِهِۦ ۖ فَلَمَّآ أَثْقَلَت دَّعَوَا ٱللَّهَ رَبَّهُمَا لَئِنْ ءَاتَيْتَنَا صَـٰلِحًا لَّنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّـٰكِرِينَ

    Shĩ ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kumaYa sanya, daga gare[1] ta, ma'auranta, dõmin ya natsu zuwa gare ta. Sa'an nan a lõkacin da ya rufe ta, ta yi ciki, ciki sassauƙa, sai ta shũɗe dashi. Sa'an nan a lõkacin da ya yi nauyi, sai suka rõƙi Allah, Ubangijinsu: "Lalle ne idan Ka bã mu abin ƙwarai, haƙĩƙa, zã mu kasance dagamãsu gõdiya."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Asalin halitta, rai guda ce, watau Ãdam, Allah ya fitar da Hauwã'u daga Ãdamu, ya mayar da ita mãtarsa, daga gare su zũriya ta yaɗu, kuma ya zama sunnar rai, namijin ya natsu zuwa ga macen. Kuma daga nan zama ya ci gaba har idan mace ta yi ciki, bã ta damuwa da shi sai yã yi nauyi, ita da miji su dinga addu'a, sunã rõƙon Allah. A bãyan bukãtarsu tã biya sai su manta da Allah, su ɗõra jingina abũbuwa zuwa ga sabubbansu, su bar tunãnin Mai sabbabawa. Daga nan abu ya yi zurfi har ya kasance shirki; bauta wa wani tãre da Allah, yãƙi ne a tsakãnin gaskiya da ƙarya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 189 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  103. 190

    فَلَمَّآ ءَاتَىٰهُمَا صَـٰلِحًا جَعَلَا لَهُۥ شُرَكَآءَ فِيمَآ ءَاتَىٰهُمَا ۚ فَتَعَـٰلَى ٱللَّهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ

    To, a lõkacin da Ya bã su abin ƙwarai, suka sanya Masa abõkan tarayya a cikin abin da Ya ba su. To, Allah Yã tsarkaka daga abin da suke yi na shirki.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 190 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  104. 191

    أَيُشْرِكُونَ مَا لَا يَخْلُقُ شَيْـًٔا وَهُمْ يُخْلَقُونَ

    Shin, sunã shirki da abin da bã ya halittar kõme, kuma sũne ake halittãwa?

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 191 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  105. 192

    وَلَا يَسْتَطِيعُونَ لَهُمْ نَصْرًا وَلَآ أَنفُسَهُمْ يَنصُرُونَ

    Kuma ba su iya bãyar da taimako gare su, kuma kansu ma, bã su iya taimaka!

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 192 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  106. 193

    وَإِن تَدْعُوهُمْ إِلَى ٱلْهُدَىٰ لَا يَتَّبِعُوكُمْ ۚ سَوَآءٌ عَلَيْكُمْ أَدَعَوْتُمُوهُمْ أَمْ أَنتُمْ صَـٰمِتُونَ

    Kuma idan kun kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su bĩ ku ba, daidai ne a gare ku, shin, kun kirãye su, kõ kuwa kũ mãsu kawaici ne!

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 193 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  107. 194

    إِنَّ ٱلَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ عِبَادٌ أَمْثَالُكُمْ ۖ فَٱدْعُوهُمْ فَلْيَسْتَجِيبُوا۟ لَكُمْ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ

    Lalle ne waɗannan da kuke kira, baicin Allah, bãyĩ ne misãlanku: to, ku kirãye su, sa'an nan su karɓa muku, idan kun kasance mãsu gaskiya!

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 194 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  108. 195

    أَلَهُمْ أَرْجُلٌ يَمْشُونَ بِهَآ ۖ أَمْ لَهُمْ أَيْدٍ يَبْطِشُونَ بِهَآ ۖ أَمْ لَهُمْ أَعْيُنٌ يُبْصِرُونَ بِهَآ ۖ أَمْ لَهُمْ ءَاذَانٌ يَسْمَعُونَ بِهَا ۗ قُلِ ٱدْعُوا۟ شُرَكَآءَكُمْ ثُمَّ كِيدُونِ فَلَا تُنظِرُونِ

    Shin sunã da ƙafãfu da suke yin tafia da su? Kõ sunã da hannãye da suke damƙa da su? Kõ sunã da idãnu da suke gani da su? Ko sunã da kunnuwa da suke saurãre da su? Ka ce: "Ku kirãwo abũbuwan[1] shirkinku sa'an nan kuma ku yi mini kaidi, sa'an nan kada ku saurãra mini."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Bãyar da tsoro da wani abin bautãwa ko jingina wata bukãta a gare shi, duka yãƙi ne a tsakãnin gaskiya da ƙarya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 195 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  109. 196

    إِنَّ وَلِـِّۧىَ ٱللَّهُ ٱلَّذِى نَزَّلَ ٱلْكِتَـٰبَ ۖ وَهُوَ يَتَوَلَّى ٱلصَّـٰلِحِينَ

    "Lalle ne, Majiɓincĩna Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi kuma Shĩ ne Yake jiɓintar sãlihai,"

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 196 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  110. 197

    وَٱلَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَسْتَطِيعُونَ نَصْرَكُمْ وَلَآ أَنفُسَهُمْ يَنصُرُونَ

    "Kuma waɗanda kuke kira, baicinSa, bã su iya taimakõn ku, kuma kansu ma, bã su iya taimaka."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 197 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  111. 198

    وَإِن تَدْعُوهُمْ إِلَى ٱلْهُدَىٰ لَا يَسْمَعُوا۟ ۖ وَتَرَىٰهُمْ يَنظُرُونَ إِلَيْكَ وَهُمْ لَا يُبْصِرُونَ

    Kuma idan ka kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su ji ba, kuma kanã ganin su, sunã dũbi zuwa gare ka, alhãli kuwa sũ, bã su gani.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 198 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  112. 199

    خُذِ ٱلْعَفْوَ وَأْمُرْ بِٱلْعُرْفِ وَأَعْرِضْ عَنِ ٱلْجَـٰهِلِينَ

    Ka riƙi abin da ya sauƙaƙa; Kuma ka yi umurni da alhẽri, Kuma ka kau da kai daga jãhilai.[1]

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Bayãnin sifõfin mai wa'azi, watau mataimakin gaskiya a kan ƙarya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 199 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  113. 200

    وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ ٱلشَّيْطَـٰنِ نَزْغٌ فَٱسْتَعِذْ بِٱللَّهِ ۚ إِنَّهُۥ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

    Kuma imma wata fizga daga Shaiɗan ta fizge ka, sai ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai jĩ ne, Masani.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 200 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  114. 201

    إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوْا۟ إِذَا مَسَّهُمْ طَـٰٓئِفٌ مِّنَ ٱلشَّيْطَـٰنِ تَذَكَّرُوا۟ فَإِذَا هُم مُّبْصِرُونَ

    Lalle ne waɗanda suka yi taƙawa idan wani tãshin hankali daga Shaiɗan ya shãfe su, sai su tuna (Allah) sai gã su, sun zama masu basĩra.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 201 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  115. 202

    وَإِخْوَٰنُهُمْ يَمُدُّونَهُمْ فِى ٱلْغَىِّ ثُمَّ لَا يُقْصِرُونَ

    Kuma 'yan'uwan su (shaiɗanu) sunã taimakon su a cikin ɓata, sa'an nan kuma bã su taƙaitãwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 202 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  116. 203

    وَإِذَا لَمْ تَأْتِهِم بِـَٔايَةٍ قَالُوا۟ لَوْلَا ٱجْتَبَيْتَهَا ۚ قُلْ إِنَّمَآ أَتَّبِعُ مَا يُوحَىٰٓ إِلَىَّ مِن رَّبِّى ۚ هَـٰذَا بَصَآئِرُ مِن رَّبِّكُمْ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ

    Kuma idan ba ka je musu da wata ãyã ba, su ce: "Don me ba ka ƙãga ta ba?" Ka ce: "Abin sani kawai, inã biyar abin da aka yõ wahayi zuwa gare ni ne, daga Ubangjina. Wannan abũbuwan kula ne daga Ubangijinku, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin imãni."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 203 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  117. 204

    وَإِذَا قُرِئَ ٱلْقُرْءَانُ فَٱسْتَمِعُوا۟ لَهُۥ وَأَنصِتُوا۟ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ

    Kuma idan an karanta[1] Alƙur'ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Bãyãn an sifanta Alƙur'ãni da cewa abin kula ne ga mãsu ĩmãni, sai kuma ya yi umurni da saurãre, a lõkacin da ake karatunsa. Sauraren yana wajabta a cikin salla, idan lĩman ya bayyana karãtu kuma da a cikin huɗubar Jumma'a. Yanã zama mustahabbi ga sauran lõkatai. Kur'ãni shi ne abin da ake wa'azi da shi kuma shi ne ãyã da kansa. Hana saurãrensa yãƙi ne da gaskiya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 204 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  118. 205

    وَٱذْكُر رَّبَّكَ فِى نَفْسِكَ تَضَرُّعًا وَخِيفَةً وَدُونَ ٱلْجَهْرِ مِنَ ٱلْقَوْلِ بِٱلْغُدُوِّ وَٱلْـَٔاصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ ٱلْغَـٰفِلِينَ

    Kuma ka ambaci[1] Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsõro, kuma kõmabãyan bayyanawa na magana, da sãfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Sa'an nan kuma ya yi umurni da ambaton Allah da addu'a a farko da ƙarshen rãna kamar yadda ya yi umurni da yin salla a waɗannan lõkatai, watau wannan shine makãmin gaskiya a kan ƙarya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 205 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  119. 206

    إِنَّ ٱلَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ لَا يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِهِۦ وَيُسَبِّحُونَهُۥ وَلَهُۥ يَسْجُدُونَ ۩

    Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka bã su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sunã tsarake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 206 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
Rufewar sura: Tafsirin As-Sa'di (Larabci)

تم تفسير سورة الأعراف. ولله الحمد والشكر والثناء. وصلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم

Tafsirin As-Sa'di, Larabci v1.0.0, QuranEnc.com

Tafsiri

الأنفال

Al-Anfal

ayoyi 75MadaniyaJuzu'i 9
Saitunan karatu

Jagorar launukan tajwidi

Sunaye, misalai da layukan ƙasa iri-iri suna bayyana ƙa'idojin baya ga launi. An ɗauko misalan daga rubutun Alƙur'ani da aka wallafa.

Gunna
وَمِمَّا2:3
Nau'o'in Ikhfa'i
يُنفِقُونَ2:3
Nau'o'in Idgami
هُدًى لِّلْمُتَّقِينَ2:2
Iƙlabi
أَلِيمٌۢ بِمَا2:10
Ƙalƙala
رَزَقْنَـٰهُمْ2:3
Madda: harka 2
ٱلرَّحْمَـٰنِ1:1
Madda: harka 2, 4 ko 6
ٱلرَّحِيمِ1:1
Madda: harka 4 ko 5
بِمَآ2:4
Madda: harka 6
ٱلضَّآلِّينَ1:7
Hamzatul wasli
ٱللَّهِ1:1
Lam Shamsiyya
ٱلرَّحْمَـٰنِ1:1
Haruffan da ba a furtawa
ٱلصَّلَوٰةَ2:3

Alamomin tajwidi: cpfair/quran-tajweed (CC BY 4.0), an gina su daga ReciteQuran.com da mus'hafan tajwidi na Dar al-Maarifah; an daidaita wurarensu da rubutun Tanzil na yanzu.

Gabatarwar sura: Tafsirin As-Sa'di (Larabci)

تفسير سورة الأنفال

وهي مدنية

Tafsirin As-Sa'di, Larabci v1.0.0, QuranEnc.com

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Fassarar Hausa - Abubakar Gumi. Siga: 1.2.2. Sabuntawa ta ƙarshe: 2025-06-26. QuranEnc.com

  1. 1

    يَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلْأَنفَالِ ۖ قُلِ ٱلْأَنفَالُ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِ ۖ فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَصْلِحُوا۟ ذَاتَ بَيْنِكُمْ ۖ وَأَطِيعُوا۟ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ

    Suna tambayar ka[1] ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance Mũminai."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Yã fãra Sũrar da tambayar Sahabbai ga Annabi cewa. wãne ne ya fi cancanta da dũkiyar ganĩmar da aka sãmu a yãƙin Badar Babba, samãri mayãƙa kõ tsõfaffi mãsu bãyar da shãwara da ra'ayõyinsu, mãsu kyau. Sa'annan ya yi jawãbi da cewa: "Ka ce ganimar ta Allah ce da ManzonSa," sabõda dalĩlan da suke tafe ga ayõyin da suke biye. Ana nufi wanke sõja daga jãyayya a kan dũkiya. AllahYa fi sani.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 1 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  2. 2

    إِنَّمَا ٱلْمُؤْمِنُونَ ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَجِلَتْ قُلُوبُهُمْ وَإِذَا تُلِيَتْ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتُهُۥ زَادَتْهُمْ إِيمَـٰنًا وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ

    Abin sani kawai, nũminai sũ ne waɗanda suke idan an ambaci, Allah, zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyõyinSa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãni, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 2 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  3. 3

    ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقْنَـٰهُمْ يُنفِقُونَ

    Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azũrtã su sunã ciyarwa.[1]

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Watau sunã yin ibãda ta jiki da ta dũkiya wãjiba da nãfila.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 3 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  4. 4

    أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُؤْمِنُونَ حَقًّا ۚ لَّهُمْ دَرَجَـٰتٌ عِندَ رَبِّهِمْ وَمَغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ

    Waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya. Sunã da darajõji a wurin Ubangijinsu, da wata gãfara da arziki na karimci.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 4 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  5. 5

    كَمَآ أَخْرَجَكَ رَبُّكَ مِنۢ بَيْتِكَ بِٱلْحَقِّ وَإِنَّ فَرِيقًا مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ لَكَـٰرِهُونَ

    Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka da gaskiya, alhãli kuwa lalle wani ɓangare na mũminai, haƙĩƙa, sunã ƙyãma.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 5 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  6. 6

    يُجَـٰدِلُونَكَ فِى ٱلْحَقِّ بَعْدَ مَا تَبَيَّنَ كَأَنَّمَا يُسَاقُونَ إِلَى ٱلْمَوْتِ وَهُمْ يَنظُرُونَ

    Sunã jãyayya da kai a cikin (sha'anin) gaskiya a bãyan tã bayYanã, kamar dai lalle anã kõra su zuwa ga mutuwa ne alhãli kuwa sunã kallo.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 6 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  7. 7

    وَإِذْ يَعِدُكُمُ ٱللَّهُ إِحْدَى ٱلطَّآئِفَتَيْنِ أَنَّهَا لَكُمْ وَتَوَدُّونَ أَنَّ غَيْرَ ذَاتِ ٱلشَّوْكَةِ تَكُونُ لَكُمْ وَيُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُحِقَّ ٱلْحَقَّ بِكَلِمَـٰتِهِۦ وَيَقْطَعَ دَابِرَ ٱلْكَـٰفِرِينَ

    Kuma a lõkacin[1] da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cẽwa lalle ita tãku ce: kuma kunã gũrin cẽwa lalle ƙungiya wadda bã ta da ƙaya ta kasance gare ku, kuma Allah Yanã nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kuma Ya kãtse ƙarshen kãfirai;

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Asalin fitar Musulmi zuwa Badar shi ne Annabi ya ji lãbãrin Abu Sufyãna yã fito daga Makka da ãyari zuwa Shãm, watau "Syria" , sai ya fita dõmin a kãma shi, suka sãmi Abu Sufyãna yã shige da dũkiya, sabõda haka Annabi daga Badar ya kõma Madĩna. Wannan fita, anã kiran ta Badar karama. Da Abu Sufyãna ya sãmi lãbãri, sai ya aika wa Kuraishãwa, dõmin su fito, su tsare dũkiyarsu daga Musulmi. Annabi, da ya ji lãbãrin kõmõwar Abu Sufyãna, sai ya fita tãre da jama'arsa, wanda ya ji Yanã son fita, kuma yanã da abin hawa. Abu Sufyãna tãre da ãyari sũ ne wajen da bãbu ƙaya. Yaƙin Kuraishãwa shĩ ne wajen da yake da ƙaya. Musulmi a tsakiya. Abu Sufyãna ya saki hanya ya tsĩra .Ya nemi Kuraishãwa da su kõma, Abu Jahal ya ce sai Allah Yã yi hukunci a tsakãninsu da Muhammadu wanda ya kãtse zumuntã, ya bar addinin iyãye.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 7 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  8. 8

    لِيُحِقَّ ٱلْحَقَّ وَيُبْطِلَ ٱلْبَـٰطِلَ وَلَوْ كَرِهَ ٱلْمُجْرِمُونَ

    Dõmin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya ɓãta ƙarya, kuma kõdã mãsu laifi sun ƙi.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 8 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  9. 9

    إِذْ تَسْتَغِيثُونَ رَبَّكُمْ فَٱسْتَجَابَ لَكُمْ أَنِّى مُمِدُّكُم بِأَلْفٍ مِّنَ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةِ مُرْدِفِينَ

    A lõkacin da kuke nẽman Ubangijinku tairnako, sai Ya karɓa muku cẽwa: "Lalle ne Nĩ, Mai taimakon ku ne da dubu daga malã'iku, jẽre."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 9 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  10. 10

    وَمَا جَعَلَهُ ٱللَّهُ إِلَّا بُشْرَىٰ وَلِتَطْمَئِنَّ بِهِۦ قُلُوبُكُمْ ۚ وَمَا ٱلنَّصْرُ إِلَّا مِنْ عِندِ ٱللَّهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ

    Kuma Allah bai sanya shi ba fãce Dõmin bishãra, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi, kuma taimakon, bai zama ba fãce daga wurin Allah; Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 10 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  11. 11

    إِذْ يُغَشِّيكُمُ ٱلنُّعَاسَ أَمَنَةً مِّنْهُ وَيُنَزِّلُ عَلَيْكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً لِّيُطَهِّرَكُم بِهِۦ وَيُذْهِبَ عَنكُمْ رِجْزَ ٱلشَّيْطَـٰنِ وَلِيَرْبِطَ عَلَىٰ قُلُوبِكُمْ وَيُثَبِّتَ بِهِ ٱلْأَقْدَامَ

    A lõkacin da (Allah) Yake rufe ku da gyangyaɗi, ɗõmin aminci daga gare Shi, kuma Yanã saukar da ruwa[1] daga sama, a kanku, dõmin Ya tsarkake ku da shi, kuma Ya tafiyar da ƙazantar Shaiɗan daga barinku, kuma dõmin Ya ɗaure a kan zukãtanku, kuma Ya tabbatar da ƙafãfu da shi.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] A lõkacin zãfi ne na bazara, kuma aka faralta azumi, sai Allah Ya saukar da ruwa daidai da sansanin Musulmi, suka shã, suka yi wanka sa'an nan kuma aka daddale musu rairayi dõmin sauƙin tafiya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 11 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  12. 12

    إِذْ يُوحِى رَبُّكَ إِلَى ٱلْمَلَـٰٓئِكَةِ أَنِّى مَعَكُمْ فَثَبِّتُوا۟ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ۚ سَأُلْقِى فِى قُلُوبِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ ٱلرُّعْبَ فَٱضْرِبُوا۟ فَوْقَ ٱلْأَعْنَاقِ وَٱضْرِبُوا۟ مِنْهُمْ كُلَّ بَنَانٍ

    A lõkacin da Ubangijinka Yake yin wahayi zuwa ga Malã'iku cẽwa: "Lalle ne Ni, Inã tãre da ku, sai ku tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni: Zã Ni jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta, sai ku yi dũka bisa ga wuyõyi kuma ku yi dũka daga gare su ga dukkan yãtsu.[1]

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Sa'an nan kuma Annabi da umurnin Allah ya ɗebi tsakuwa da hannunsa mai daraja ya jefa a jihar kãfirai. Bãbu wanda ya rage a cikinsu, fãce tsakuwar nan tã shiga a cikin idãnunsa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 12 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  13. 13

    ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ شَآقُّوا۟ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ ۚ وَمَن يُشَاقِقِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَإِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلْعِقَابِ

    Wancan ne, dõmin lalle ne sũ, sunã sãɓa wa Allah da ManzonSa. Kuma wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 13 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  14. 14

    ذَٰلِكُمْ فَذُوقُوهُ وَأَنَّ لِلْكَـٰفِرِينَ عَذَابَ ٱلنَّارِ

    Wancan ne: "Ku ɗanɗane shi, kuma lalle ne akwai azãbar wuta ga kãfirai."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 14 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  15. 15

    يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِذَا لَقِيتُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ زَحْفًا فَلَا تُوَلُّوهُمُ ٱلْأَدْبَارَ

    Yã kũ wacɗanda suka yiĩmãni! Idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta ga yãƙi, to, kada ku jũya musu bãyayyakin ku.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 15 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  16. 16

    وَمَن يُوَلِّهِمْ يَوْمَئِذٍ دُبُرَهُۥٓ إِلَّا مُتَحَرِّفًا لِّقِتَالٍ أَوْ مُتَحَيِّزًا إِلَىٰ فِئَةٍ فَقَدْ بَآءَ بِغَضَبٍ مِّنَ ٱللَّهِ وَمَأْوَىٰهُ جَهَنَّمُ ۖ وَبِئْسَ ٱلْمَصِيرُ

    Kuma duka wanda[1] ya jũya musu bãyansa a yinin nan, fãce wanda ya karkata dõmin kõɗayya, kõ kuwa wanda ya jẽ dõmin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya kõma da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makõma ita!

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Gudu a wurin yãƙin Jihãdi shĩ ne mafi girman haram duka, matuƙar kãfirai ba su fi ninki biyu na adadin Musulmi ba, kamar yadda zai zo. Wanda ya yi gudu a wurin jihãdi kamar yã nemi kãfirci ya rinjãyi Musulunci ne.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 16 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  17. 17

    فَلَمْ تَقْتُلُوهُمْ وَلَـٰكِنَّ ٱللَّهَ قَتَلَهُمْ ۚ وَمَا رَمَيْتَ إِذْ رَمَيْتَ وَلَـٰكِنَّ ٱللَّهَ رَمَىٰ ۚ وَلِيُبْلِىَ ٱلْمُؤْمِنِينَ مِنْهُ بَلَآءً حَسَنًا ۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

    To, bã kũ ne kuka kashe su ba; kuma amma Allah ne Ya kashe su: kuma ba ka yi jĩfa ba a lõkacin da ka yi jĩfa;[1] kuma amma Allah ne Ya yi jĩfar. Kuma dõminYa jarraba Musulmi da jarrabãwa mai kyau daga gare shi. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Kisan da aka yi musu, Allah ne Ya kashe su, haka Annabi ya ɗebi tsakuwa da hannunsa mai daraja ya jefa wa kãfirai, tsakuwar ta shiga cikin idãnun kõwane ɗaya daga cikinsu. To, wannan jĩfar daga Allah take. Sabõda haka duk ganĩmar dai ta Allah ce da ManzonSa, sai yadda Ya so, zã a raba ta.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 17 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  18. 18

    ذَٰلِكُمْ وَأَنَّ ٱللَّهَ مُوهِنُ كَيْدِ ٱلْكَـٰفِرِينَ

    Wancan ne, kuma lalle ne, Allah Mai raunana kaidin kãfirai ne.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 18 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  19. 19

    إِن تَسْتَفْتِحُوا۟ فَقَدْ جَآءَكُمُ ٱلْفَتْحُ ۖ وَإِن تَنتَهُوا۟ فَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ ۖ وَإِن تَعُودُوا۟ نَعُدْ وَلَن تُغْنِىَ عَنكُمْ فِئَتُكُمْ شَيْـًٔا وَلَوْ كَثُرَتْ وَأَنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلْمُؤْمِنِينَ

    Idan kun yi alfãnun cin nasara to lalle nasarar tã je muku, kuma idan kun hanu, to Shi ne Mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun kõma zã Mu kõma, kuma jama'arku bã zã ta wadãtar muku da kõme ba, kõ dã tã yi yawa. Kuma lalle ne cẽwa Allah Yanã tãre da mũminai!

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 19 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  20. 20

    يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَطِيعُوا۟ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَا تَوَلَّوْا۟ عَنْهُ وَأَنتُمْ تَسْمَعُونَ

    Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku jũya daga barinSa, alhãli kunã ji.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 20 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  21. 21

    وَلَا تَكُونُوا۟ كَٱلَّذِينَ قَالُوا۟ سَمِعْنَا وَهُمْ لَا يَسْمَعُونَ

    Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka ce: "Mun ji, alhãli kuwa sũ bã su ji."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 21 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  22. 22

    ۞ إِنَّ شَرَّ ٱلدَّوَآبِّ عِندَ ٱللَّهِ ٱلصُّمُّ ٱلْبُكْمُ ٱلَّذِينَ لَا يَعْقِلُونَ

    Lalle ne, mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne kurãme, bẽbãye, waɗanda bã, su yin hankali.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 22 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  23. 23

    وَلَوْ عَلِمَ ٱللَّهُ فِيهِمْ خَيْرًا لَّأَسْمَعَهُمْ ۖ وَلَوْ أَسْمَعَهُمْ لَتَوَلَّوا۟ وَّهُم مُّعْرِضُونَ

    Dã Allah Yã san wani alhẽri a cikinsu, dã Yã jiyar da su, kuma kõ da Yãjiyar da su, haƙĩƙa, dã sun jũya, alhãli sũ, sunã mãsu hinjirẽwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 23 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  24. 24

    يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱسْتَجِيبُوا۟ لِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ إِذَا دَعَاكُمْ لِمَا يُحْيِيكُمْ ۖ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ يَحُولُ بَيْنَ ٱلْمَرْءِ وَقَلْبِهِۦ وَأَنَّهُۥٓ إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ

    Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku karɓa wa Allah, kuma ku karɓa wa Manzo, idan Ya kirãye ku zuwa ga abin da Yake rãyar da ku; Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã shãmakacẽwa a tsakãnin mutum da zũciyarsa, kuma lalle ne Shĩ, a zuwa gare Shi ake tãra ku.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 24 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  25. 25

    وَٱتَّقُوا۟ فِتْنَةً لَّا تُصِيبَنَّ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ مِنكُمْ خَآصَّةً ۖ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلْعِقَابِ

    Kuma ku ji tsõron fitina wadda bã ta sãmun waɗanda suka yi zãlunci daga gare ku kẽɓe, kuma ku sani, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 25 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  26. 26

    وَٱذْكُرُوٓا۟ إِذْ أَنتُمْ قَلِيلٌ مُّسْتَضْعَفُونَ فِى ٱلْأَرْضِ تَخَافُونَ أَن يَتَخَطَّفَكُمُ ٱلنَّاسُ فَـَٔاوَىٰكُمْ وَأَيَّدَكُم بِنَصْرِهِۦ وَرَزَقَكُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَـٰتِ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

    Ku tuna a lõkacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwã a cikin ƙasa kunã tsõron mutãne su cafe ku, sai Ya tattara ku (a wurin natsuwa, Maɗina), kuma Ya ƙarfafã ku da taimakonSa kuma Ya azurtã ku daga abũbuwa mãsu dãɗi; Tsammãninku, kunã gõdẽwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 26 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  27. 27

    يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَخُونُوا۟ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ وَتَخُونُوٓا۟ أَمَـٰنَـٰتِكُمْ وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ

    Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yaudari Allah da ManzonSa, kuma ku yaudari amãnõninku, alhãli kuwa kunã sane.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 27 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  28. 28

    وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّمَآ أَمْوَٰلُكُمْ وَأَوْلَـٰدُكُمْ فِتْنَةٌ وَأَنَّ ٱللَّهَ عِندَهُۥٓ أَجْرٌ عَظِيمٌ

    Kuma ku sani cẽwa abin sani kawai, dũkiyõyinku da 'ya'yanku, wata fitina ce, kuma lalle ne Allah, a wurin Sa, akwai ijãra mai girma.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 28 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  29. 29

    يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِن تَتَّقُوا۟ ٱللَّهَ يَجْعَل لَّكُمْ فُرْقَانًا وَيُكَفِّرْ عَنكُمْ سَيِّـَٔاتِكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ۗ وَٱللَّهُ ذُو ٱلْفَضْلِ ٱلْعَظِيمِ

    Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun bi Allah da taƙawa, zai sanyã muku mararraba (da tsõro) kuma Ya kankare ƙanãnan zunubanku daga barinku. Kuma Ya gãfartã muku. Kuma Allah ne Ma'abũcin falalã Mai girma.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 29 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  30. 30

    وَإِذْ يَمْكُرُ بِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لِيُثْبِتُوكَ أَوْ يَقْتُلُوكَ أَوْ يُخْرِجُوكَ ۚ وَيَمْكُرُونَ وَيَمْكُرُ ٱللَّهُ ۖ وَٱللَّهُ خَيْرُ ٱلْمَـٰكِرِينَ

    Kuma a lõkacin da waɗanda[1] suka kãfirta sukẽ yin mãkirci game da kai, dõmin su tabbatar da kai, kõ kuwa su kashe ka, kõ kuwa su fitar da kai, sunã mãkirci kuma Allah Yanã mayar musa da mãkirci kuma Allah ne Mafificin mãsu mãkirci.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Ƙuraishãwa suka tãru sunã shãwarar yadda zã su yi da Muhammadu; kõ su ɗaure shi a cikin gida, kõ su kashe shi, kõ su kõre shi. Ra'ayinsu ya tsaya ga su kashe shi da zãɓaɓɓun mutãne daga kõwace ƙabĩla yadda danginsa, Banĩ Hãshim, bã su iya faɗa da dukkan Lãrabãwa, har su kõma ga diyya. A rãnar da suka shirya kashe shi, Allah Ya umurce shi da hijira zuwa Madĩna. A lõkacin da ya fita daga gidansa ya iske su tsaitsaye, sunã barci, ya zuba turɓãya a kunnuwansu, sa'annan ya shige suka tafi tãre da Abũbakar, suka sauka a cikin kõgon dũtsen Thaur. Bãyan kwãnaki uku, suka fita zuwa Madina.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 30 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  31. 31

    وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتُنَا قَالُوا۟ قَدْ سَمِعْنَا لَوْ نَشَآءُ لَقُلْنَا مِثْلَ هَـٰذَآ ۙ إِنْ هَـٰذَآ إِلَّآ أَسَـٰطِيرُ ٱلْأَوَّلِينَ

    Kuma idan aka karanta, ãyõyinMu a kansu, sukan ce: "Lalle ne mun ji dã muna so, haƙĩƙa, da mun faɗi irin wannan; wannan bai zama ba fãce tãtsunãyõyin mutãnen farko."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 31 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  32. 32

    وَإِذْ قَالُوا۟ ٱللَّهُمَّ إِن كَانَ هَـٰذَا هُوَ ٱلْحَقَّ مِنْ عِندِكَ فَأَمْطِرْ عَلَيْنَا حِجَارَةً مِّنَ ٱلسَّمَآءِ أَوِ ٱئْتِنَا بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

    A lõkacin da suka ce: "Yã Allah! Idan wannan ya kasancc shĩ ne gaskiya daga wurinKa, sai Ka yi ruwan duwãtsu, a kanmu, daga sama, kõ kuwa Kazõ mana da wata azãba, mai raɗaɗi."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 32 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  33. 33

    وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُعَذِّبَهُمْ وَأَنتَ فِيهِمْ ۚ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ مُعَذِّبَهُمْ وَهُمْ يَسْتَغْفِرُونَ

    Kuma Allah bai kasance Yanã yi musu azãba ba alhãli kuwa kai kanã cikinsu,[1] kuma Allah bai kasance Mai yi musu azãba ba alhãli kuwa sunã yin istigfãri.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Rãyuwar Annabi a cikin mutãne aminci ne daga azãba, haka kuma yin istigfãri aminci ne. Wanda ke son wadãta da aminci daga Allah, sai ya lazimci istigfãri da bin sunnar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 33 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  34. 34

    وَمَا لَهُمْ أَلَّا يُعَذِّبَهُمُ ٱللَّهُ وَهُمْ يَصُدُّونَ عَنِ ٱلْمَسْجِدِ ٱلْحَرَامِ وَمَا كَانُوٓا۟ أَوْلِيَآءَهُۥٓ ۚ إِنْ أَوْلِيَآؤُهُۥٓ إِلَّا ٱلْمُتَّقُونَ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ

    Kuma mẽne ne a gare su da Allah ba zai yi musu azãba ba, alhãli kuwa sũ, sunã kangẽwa daga Masallaci Mai alfarma kuma ba su kasance majiɓintanSa ba? Bãbu majiɓintanSa fãce mãsu taƙawa. Kuma mafi yawansu ba su sani ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 34 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  35. 35

    وَمَا كَانَ صَلَاتُهُمْ عِندَ ٱلْبَيْتِ إِلَّا مُكَآءً وَتَصْدِيَةً ۚ فَذُوقُوا۟ ٱلْعَذَابَ بِمَا كُنتُمْ تَكْفُرُونَ

    Kuma sallarsu a wurin ¦ãkin ba ta kasance ba fãce shẽwa da yãyã; sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 35 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  36. 36

    إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ يُنفِقُونَ أَمْوَٰلَهُمْ لِيَصُدُّوا۟ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ ۚ فَسَيُنفِقُونَهَا ثُمَّ تَكُونُ عَلَيْهِمْ حَسْرَةً ثُمَّ يُغْلَبُونَ ۗ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ إِلَىٰ جَهَنَّمَ يُحْشَرُونَ

    Lalle ne waɗanda suka kãfirta, sunã ciyar da dũkiyõyinsu, dõmin su kange daga hanyar Allah; to, zã a su ciyar da ita, sa' an nan kuma ta kasance nadãma a kansu, sa'an nan kuma a rinjãye su. Kuma waɗanda suka kãfirta zuwa ga Jahannama ake tãra su;

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 36 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  37. 37

    لِيَمِيزَ ٱللَّهُ ٱلْخَبِيثَ مِنَ ٱلطَّيِّبِ وَيَجْعَلَ ٱلْخَبِيثَ بَعْضَهُۥ عَلَىٰ بَعْضٍ فَيَرْكُمَهُۥ جَمِيعًا فَيَجْعَلَهُۥ فِى جَهَنَّمَ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْخَـٰسِرُونَ

    Dõmin Allah Ya rarrabe mummũna daga mai kyau, kuma Ya sanya mummũnan, sãshensa a kan sãshe, sa'an nan Ya shirga shi gabã daya, sa'an nan Ya sanyã shi a cikin Jahannama. Waɗannan sũ ne mãsu hasãra.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 37 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  38. 38

    قُل لِّلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ إِن يَنتَهُوا۟ يُغْفَرْ لَهُم مَّا قَدْ سَلَفَ وَإِن يَعُودُوا۟ فَقَدْ مَضَتْ سُنَّتُ ٱلْأَوَّلِينَ

    Ka ce wa waɗanda suka kãfirta, idan sun hanu, zã a gãfarta musu abin da ya riga ya shige, kuma idan sun kõma, to, hanyar kãfiran farko, haƙĩƙa, ta shũɗe.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 38 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  39. 39

    وَقَـٰتِلُوهُمْ حَتَّىٰ لَا تَكُونَ فِتْنَةٌ وَيَكُونَ ٱلدِّينُ كُلُّهُۥ لِلَّهِ ۚ فَإِنِ ٱنتَهَوْا۟ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِمَا يَعْمَلُونَ بَصِيرٌ

    Kuma ku yãƙe su har wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini dukansa ya kasance na Allah. To, idan sun hanu to lalle ne, Allah ia abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 39 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  40. 40

    وَإِن تَوَلَّوْا۟ فَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ مَوْلَىٰكُمْ ۚ نِعْمَ ٱلْمَوْلَىٰ وَنِعْمَ ٱلنَّصِيرُ

    Kuma idan sun jũya, to, ku sani cẽwa lalle Allah ne Majiɓincinku: Mãdalla da Majiɓinci, kuma mãdalla da Mai taimako, Shĩ.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 40 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri

Tafsiri

Ba da rahoton kuskure

Ƙari