الإسراء

Al-Isra'i

ayoyi 111MakkiyaJuzu'i 15

Mahmoud Khalil Al-HussaryHafsu daga Asim - Murattal

Saitunan karatu

Jagorar launukan tajwidi

Sunaye, misalai da layukan ƙasa iri-iri suna bayyana ƙa'idojin baya ga launi. An ɗauko misalan daga rubutun Alƙur'ani da aka wallafa.

Gunna
وَمِمَّا2:3
Nau'o'in Ikhfa'i
يُنفِقُونَ2:3
Nau'o'in Idgami
هُدًى لِّلْمُتَّقِينَ2:2
Iƙlabi
أَلِيمٌۢ بِمَا2:10
Ƙalƙala
رَزَقْنَـٰهُمْ2:3
Madda: harka 2
ٱلرَّحْمَـٰنِ1:1
Madda: harka 2, 4 ko 6
ٱلرَّحِيمِ1:1
Madda: harka 4 ko 5
بِمَآ2:4
Madda: harka 6
ٱلضَّآلِّينَ1:7
Hamzatul wasli
ٱللَّهِ1:1
Lam Shamsiyya
ٱلرَّحْمَـٰنِ1:1
Haruffan da ba a furtawa
ٱلصَّلَوٰةَ2:3

Alamomin tajwidi: cpfair/quran-tajweed (CC BY 4.0), an gina su daga ReciteQuran.com da mus'hafan tajwidi na Dar al-Maarifah; an daidaita wurarensu da rubutun Tanzil na yanzu.

Gabatarwar sura: Tafsirin As-Sa'di (Larabci)

تفسير سورة بني إسرائيل

وهي مكية

بسم الله الرحمن الرحيم

Tafsirin As-Sa'di, Larabci v1.0.0, QuranEnc.com

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Fassarar Hausa - Abubakar Gumi. Siga: 1.2.2. Sabuntawa ta ƙarshe: 2025-06-26. QuranEnc.com

  1. 1

    سُبْحَـٰنَ ٱلَّذِىٓ أَسْرَىٰ بِعَبْدِهِۦ لَيْلًا مِّنَ ٱلْمَسْجِدِ ٱلْحَرَامِ إِلَى ٱلْمَسْجِدِ ٱلْأَقْصَا ٱلَّذِى بَـٰرَكْنَا حَوْلَهُۥ لِنُرِيَهُۥ مِنْ ءَايَـٰتِنَآ ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْبَصِيرُ

    Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare[1] da bãwanSa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa[2] wanda Muka sanya albarka a gefensa dõmin Mu nũna masa daga ãyõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Isrã'i, shi ne tafiyar dare da Allah Ya yi da Annabi daga Makka zuwa Baitil Maƙadis. Sa'an nan Mi'iraji zuwa sama inda aka ba shi sallõli. [2] Muƙarana a tsakãnin Masjidil Harãm watau tsararre daga a yãki mutãnensa da Masjidil Aƙsã wanda ba tsararre ba. Isrã'i da Mi'irãji sun fi Miƙãtin Mũsã da gãnãwarsa da Ubangiji a Ɗũr-Sĩna'a.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 1 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  2. 2

    وَءَاتَيْنَا مُوسَى ٱلْكِتَـٰبَ وَجَعَلْنَـٰهُ هُدًى لِّبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ أَلَّا تَتَّخِذُوا۟ مِن دُونِى وَكِيلًا

    Kuma Mun bai wa Mũsã[1] littafi, kuma Mun sanya shi shiriya ga Banĩ Isrã'ila, cẽwa kada ku riƙi wani wakĩli baici Na.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Tsakãnin Bãwan Allah Muhammadu da Mũsã, kuma an aiko Mũsã ga Banĩ Isrã'ila kawai, kuma Nũhu an ce masa bãwa amma ba a jingina shi kamar yadda aka jingina bawanSa ba. Sa'an nan kuma Jingina Yahũdu ga Nũhu ya daidaita su da sauran mutãne wajen da'awar ɗaukaka da nasaba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 2 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  3. 3

    ذُرِّيَّةَ مَنْ حَمَلْنَا مَعَ نُوحٍ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَبْدًا شَكُورًا

    Zuriyar waɗanda Muka ɗauka tãre da Nũhu. Lalle ne shi ya kasance wani bãwa mai gõdiya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 3 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  4. 4

    وَقَضَيْنَآ إِلَىٰ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ فِى ٱلْكِتَـٰبِ لَتُفْسِدُنَّ فِى ٱلْأَرْضِ مَرَّتَيْنِ وَلَتَعْلُنَّ عُلُوًّا كَبِيرًا

    Kuma Mun hukunta zuwa ga Bani Isrã'ĩla a cikin Littãfi, cewa lalle ne, kunã yin ɓarna a cikin ƙasa sau biyu, kuma lalle ne kunã zãlunci, zãlunci mai girma.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 4 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  5. 5

    فَإِذَا جَآءَ وَعْدُ أُولَىٰهُمَا بَعَثْنَا عَلَيْكُمْ عِبَادًا لَّنَآ أُو۟لِى بَأْسٍ شَدِيدٍ فَجَاسُوا۟ خِلَـٰلَ ٱلدِّيَارِ ۚ وَكَانَ وَعْدًا مَّفْعُولًا

    To idan wa'adin na farkonsu yajẽ, za Mu aika, a kanku waɗansu bãyi[1] Nãmu, ma'abũta yãƙi mafĩ tsanani, har su yi yãwo a tsakãnin gidãjenku, kuma yã zama wa'adi abin aikatawa.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Sun yi fasãdi da barin aiki da Taurãti, sabõda haka aka aika Jãlũta a kansu. Ya kashe su kuma ya kãma zuriyarsu.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 5 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  6. 6

    ثُمَّ رَدَدْنَا لَكُمُ ٱلْكَرَّةَ عَلَيْهِمْ وَأَمْدَدْنَـٰكُم بِأَمْوَٰلٍ وَبَنِينَ وَجَعَلْنَـٰكُمْ أَكْثَرَ نَفِيرًا

    Sa'an nan kuma Mu nwayar da ɗauki a gare ku a kansu, kuma Mu taimake ku da dũkiyõyi da ɗiya kuma Mu sanya ku mafiya yawan mãsu fita yãƙi.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 6 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  7. 7

    إِنْ أَحْسَنتُمْ أَحْسَنتُمْ لِأَنفُسِكُمْ ۖ وَإِنْ أَسَأْتُمْ فَلَهَا ۚ فَإِذَا جَآءَ وَعْدُ ٱلْـَٔاخِرَةِ لِيَسُـۥٓـُٔوا۟ وُجُوهَكُمْ وَلِيَدْخُلُوا۟ ٱلْمَسْجِدَ كَمَا دَخَلُوهُ أَوَّلَ مَرَّةٍ وَلِيُتَبِّرُوا۟ مَا عَلَوْا۟ تَتْبِيرًا

    Idan kun kyautata, kun kyautata dõmin kanku, kuma idan kun mũnana to dõmĩnsu. Sa'an nan idan wa'adin na ƙarshe[1] ya jẽ, (za su je) dõmin su baƙanta fuskokinku, kuma su shiga masallaci kamar yadda suka shige shi a farkon lõkaci, kuma dõmin su halakar da abin da suka rinjaya a kansa, halakarwa.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Suka yi fasãdi marra ta biyu da kashe Zakariyya da Yahaya, sai aka aika musu da Bukht Nasar daga Bãbila ya karkashe su, kuma ya kãma zuriyarsu, kuma ya rũshe Baitil Maƙadis. Waɗannan lãbaru biyu na ɓarnar Banĩ Isrã'ila sunã cikin bãyar da lãbaru ga gaibi. Idan an daidaita su da lãbarun gaibi waɗanda Alƙur'ãni ya faɗã, waɗansu suka auku kuma waɗansu sunã ta aukuwa zã a san falalar Alƙur'ãni a kan Taurãti kamar yadda ya bayyana cewa Attaura ta yi kira zuwa ga tauhidi da shiriya, sa'an nan ya bayyana abũbuwan da Alƙur'ãnĩ yake karantarwa daga ãyã ta 9 zuwa ga ãyã ta 38 inda ya tãra hãlãyen ƙwarai kuma ya kõre mũnãna.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 7 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  8. 8

    عَسَىٰ رَبُّكُمْ أَن يَرْحَمَكُمْ ۚ وَإِنْ عُدتُّمْ عُدْنَا ۘ وَجَعَلْنَا جَهَنَّمَ لِلْكَـٰفِرِينَ حَصِيرًا

    Akwai tsammãnin Ubangijinku Ya yi muku rahama. Kuma idan kun sãke Mu sãke. Kuma Mun sanya Jahannama matsara ga kãfirai.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 8 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  9. 9

    إِنَّ هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانَ يَهْدِى لِلَّتِى هِىَ أَقْوَمُ وَيُبَشِّرُ ٱلْمُؤْمِنِينَ ٱلَّذِينَ يَعْمَلُونَ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ أَنَّ لَهُمْ أَجْرًا كَبِيرًا

    Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã shiryarwa ga (hãlayen) waɗanda suke mafi daidaita[1] kuma yanã bãyar da bushãra ga mũminai waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai (cẽwa) "Lalle ne sunã da wata ijãra. mai girma."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Bãyan ya faɗi abũbuwan da Attaura ta karantar, ya ce: "Alƙur'ãni yanã shiryarwa zuwa ga hãlãyen da suka fi daidaita daga abin da Attaura ta karantar." Sa'an nan ya ci gaba da bayãnin abũbuwan da Alƙur'ãni yake karantarwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 9 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  10. 10

    وَأَنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ أَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا

    Kuma lalle ne, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, Mun yimusu tattalin wata azãba mai raɗaɗi.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 10 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  11. 11

    وَيَدْعُ ٱلْإِنسَـٰنُ بِٱلشَّرِّ دُعَآءَهُۥ بِٱلْخَيْرِ ۖ وَكَانَ ٱلْإِنسَـٰنُ عَجُولًا

    Kuma mutum yanã[1] yin addu'a da sharri kamar addu'arsa da alhẽri, kuma mutum ya kasance mai gaggãwa.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Alƙur'ani yanã shiryar da mutum har ga yadda yake yin addu'a dõmin kada ya yi wa kansa addu'a ta sharri alhãli kuwa yanã nufin ya yi alhħri dõmin an halicci mutum da son gaggãwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 11 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  12. 12

    وَجَعَلْنَا ٱلَّيْلَ وَٱلنَّهَارَ ءَايَتَيْنِ ۖ فَمَحَوْنَآ ءَايَةَ ٱلَّيْلِ وَجَعَلْنَآ ءَايَةَ ٱلنَّهَارِ مُبْصِرَةً لِّتَبْتَغُوا۟ فَضْلًا مِّن رَّبِّكُمْ وَلِتَعْلَمُوا۟ عَدَدَ ٱلسِّنِينَ وَٱلْحِسَابَ ۚ وَكُلَّ شَىْءٍ فَصَّلْنَـٰهُ تَفْصِيلًا

    Kuma Mun sanya dare da rãna, ãyõyi biyu, sa'an nan Muka shãfe ãyar dare, kuma Muka sanya ãyar rãna mai sanyãwa a yi gani, dõmin ku nẽmi falala daga Ubangijinku, kuma dõmin ku san ƙidãyar shẽkara da lissafi. Kuma dukan kõme Mun bayyana shi daki-dakin bayyanãwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 12 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  13. 13

    وَكُلَّ إِنسَـٰنٍ أَلْزَمْنَـٰهُ طَـٰٓئِرَهُۥ فِى عُنُقِهِۦ ۖ وَنُخْرِجُ لَهُۥ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ كِتَـٰبًا يَلْقَىٰهُ مَنشُورًا

    Kuma kõwane mutum Mun lazimta masa abin rekõdinsa a cikin wuyansa, kuma Mu fitar masa a Rãnar ¡iyãma da littãfi wanda zai haɗu da shi buɗaɗɗe.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 13 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  14. 14

    ٱقْرَأْ كِتَـٰبَكَ كَفَىٰ بِنَفْسِكَ ٱلْيَوْمَ عَلَيْكَ حَسِيبًا

    "Karanta Littãfinka. Ranka ya isa ya zama mai hisãbi a kanka a yau."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 14 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  15. 15

    مَّنِ ٱهْتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهْتَدِى لِنَفْسِهِۦ ۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيْهَا ۚ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰ ۗ وَمَا كُنَّا مُعَذِّبِينَ حَتَّىٰ نَبْعَثَ رَسُولًا

    Wanda ya nẽmi shiryuwa, to, ya nẽmi shiryuwa ne dõminkansa kawai kuma wanda ya ɓace, to, ya ɓace ne a kansa kawai kuma rai mai ɗaukar nauyi bã ya ɗaukar nauyin wani ran, kuma ba Mu zama mãsu yin azãba ba, sai Mun aika wani Manzo.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 15 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  16. 16

    وَإِذَآ أَرَدْنَآ أَن نُّهْلِكَ قَرْيَةً أَمَرْنَا مُتْرَفِيهَا فَفَسَقُوا۟ فِيهَا فَحَقَّ عَلَيْهَا ٱلْقَوْلُ فَدَمَّرْنَـٰهَا تَدْمِيرًا

    Kuma idan Mun yi nufin Mu halakar da wata alƙarya, sai Mu umurci mawadãtanta, har su yi fasadi a cikinta, sa'an nan maganar azãba ta wajaba a kanta, sa'an nan Mu darkãke ta, darkãkẽwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 16 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  17. 17

    وَكَمْ أَهْلَكْنَا مِنَ ٱلْقُرُونِ مِنۢ بَعْدِ نُوحٍ ۗ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ بِذُنُوبِ عِبَادِهِۦ خَبِيرًۢا بَصِيرًا

    Kuma da yawa Muka halakar da al'ummomi a bãyan Nũhu. Kuma Ubangijinka Ya isa ya zama Mai ƙididdigewa ga zunubban bãyinSa, Mai gani.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 17 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  18. 18

    مَّن كَانَ يُرِيدُ ٱلْعَاجِلَةَ عَجَّلْنَا لَهُۥ فِيهَا مَا نَشَآءُ لِمَن نُّرِيدُ ثُمَّ جَعَلْنَا لَهُۥ جَهَنَّمَ يَصْلَىٰهَا مَذْمُومًا مَّدْحُورًا

    Wanda ya kasance yanã nufin mai gaggãwa, sai Mu gaggauta masa a cikinta, abin da Muke so ga wanda Muke nufi, sa'an nan kuma Mu sanya masa Jahannama, ya ƙõnu da ita, yanã abin zargi kuma abin tunkuɗewa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 18 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  19. 19

    وَمَنْ أَرَادَ ٱلْـَٔاخِرَةَ وَسَعَىٰ لَهَا سَعْيَهَا وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ كَانَ سَعْيُهُم مَّشْكُورًا

    Kuma wanda ya nufi Lãhira, kuma ya yi aiki sabõda ita irin aikinta alhãli kuwa yanã mũmĩni, to, waɗannan aikinsu ya kasance gõdadde.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 19 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  20. 20

    كُلًّا نُّمِدُّ هَـٰٓؤُلَآءِ وَهَـٰٓؤُلَآءِ مِنْ عَطَآءِ رَبِّكَ ۚ وَمَا كَانَ عَطَآءُ رَبِّكَ مَحْظُورًا

    Dukkansu Munã taimakon waɗannan da waɗancan daga kyautar Ubangijinka, kuma kyautar Ubangijinka ba ta kasance hananna ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 20 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  21. 21

    ٱنظُرْ كَيْفَ فَضَّلْنَا بَعْضَهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ ۚ وَلَلْـَٔاخِرَةُ أَكْبَرُ دَرَجَـٰتٍ وَأَكْبَرُ تَفْضِيلًا

    Ka duba yadda Muka fĩfĩtar da sãshensu a kan sãshe! Kuma lalle ne Lãhira ce mafi girman darajõji, kuma mafi girman fĩfĩtãwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 21 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  22. 22

    لَّا تَجْعَلْ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ فَتَقْعُدَ مَذْمُومًا مَّخْذُولًا

    Kada ka sanya wani abin bautawa na daban tãre da Allah har ka zauna kana abin zargi, yarɓaɓɓe.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 22 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  23. 23

    ۞ وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوٓا۟ إِلَّآ إِيَّاهُ وَبِٱلْوَٰلِدَيْنِ إِحْسَـٰنًا ۚ إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِندَكَ ٱلْكِبَرَ أَحَدُهُمَآ أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُل لَّهُمَآ أُفٍّ وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُل لَّهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا

    Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi, kum game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsũfa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsãwace su kuma ka faɗa musu magana mai karimci.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 23 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  24. 24

    وَٱخْفِضْ لَهُمَا جَنَاحَ ٱلذُّلِّ مِنَ ٱلرَّحْمَةِ وَقُل رَّبِّ ٱرْحَمْهُمَا كَمَا رَبَّيَانِى صَغِيرًا

    Kuma ka sassauta musu fikãfikan tausasãwa na rahama. Kuma ka ce: "Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rẽnõna, ina ƙarami."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 24 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  25. 25

    رَّبُّكُمْ أَعْلَمُ بِمَا فِى نُفُوسِكُمْ ۚ إِن تَكُونُوا۟ صَـٰلِحِينَ فَإِنَّهُۥ كَانَ لِلْأَوَّٰبِينَ غَفُورًا

    Ubangijin ku ne Mafi sani ga abin da yake a cikin rãyukanku. Idan kun kasan ce sãlihai to lalle ne shĩ Ya kasance ga mãsu kõmawa gare Shi, Mai gãfara.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 25 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  26. 26

    وَءَاتِ ذَا ٱلْقُرْبَىٰ حَقَّهُۥ وَٱلْمِسْكِينَ وَٱبْنَ ٱلسَّبِيلِ وَلَا تُبَذِّرْ تَبْذِيرًا

    Kuma ka bai wa ma'abũcin zumunta hakkinsa[1] da miskĩna da ɗan hanya. Kuma kada ka bazzara dũkiyar ka, bazzarãwa.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Hakkin zumunta shi ne alheri da sãdar da zumunta. Hakkin miskini da ɗan hanya zakka da sadakar taɗawwa'i da liyãfar kwana uku ga bãƙo bisa al'ada da alheri, bã bisa ɓarna da kallafãwa ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 26 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  27. 27

    إِنَّ ٱلْمُبَذِّرِينَ كَانُوٓا۟ إِخْوَٰنَ ٱلشَّيَـٰطِينِ ۖ وَكَانَ ٱلشَّيْطَـٰنُ لِرَبِّهِۦ كَفُورًا

    Lalle ne mubazzarai sun kasance 'yan'uwan shaiɗanu. Kuma Shaiɗan ya kasance ga Ubangijinsa, mai yawan kãfirci.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 27 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  28. 28

    وَإِمَّا تُعْرِضَنَّ عَنْهُمُ ٱبْتِغَآءَ رَحْمَةٍ مِّن رَّبِّكَ تَرْجُوهَا فَقُل لَّهُمْ قَوْلًا مَّيْسُورًا

    Ko dai ka kau da kai daga gare su dõmin nẽman rahama daga Ubangijinka, wadda kake fãtanta, to sai ka gaya musu magana mai laushi.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 28 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  29. 29

    وَلَا تَجْعَلْ يَدَكَ مَغْلُولَةً إِلَىٰ عُنُقِكَ وَلَا تَبْسُطْهَا كُلَّ ٱلْبَسْطِ فَتَقْعُدَ مَلُومًا مَّحْسُورًا

    Kuma kada ka sanya hannunka ƙuƙuntacce zuwa ga wuyanka, kuma kada ka shimfiɗa shi dukan shimfiɗãwa har ka zama abin zargi, wanda ake yanke wa.[1]

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Kada ka zama marõwaci a zarge ka, kuma kada ka zama almubazzari ka rasa mutãne, su yanke daga gare ka.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 29 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  30. 30

    إِنَّ رَبَّكَ يَبْسُطُ ٱلرِّزْقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقْدِرُ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرًۢا بَصِيرًا

    Lalle ne Ubangijinka Yanã shimfiɗa arzĩki ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntãwa. Lalle Shi, Yã kasance Mai sani ga bãyinSa, Mai gani.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 30 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  31. 31

    وَلَا تَقْتُلُوٓا۟ أَوْلَـٰدَكُمْ خَشْيَةَ إِمْلَـٰقٍ ۖ نَّحْنُ نَرْزُقُهُمْ وَإِيَّاكُمْ ۚ إِنَّ قَتْلَهُمْ كَانَ خِطْـًٔا كَبِيرًا

    Kuma kada ku kashe 'yã'yanku dõmin tsõron talauci. Mu ne ke arzũta su, su da ku. Lalle ne kashe su yã kasance kuskure babba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 31 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  32. 32

    وَلَا تَقْرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰٓ ۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةً وَسَآءَ سَبِيلًا

    Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 32 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  33. 33

    وَلَا تَقْتُلُوا۟ ٱلنَّفْسَ ٱلَّتِى حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلْحَقِّ ۗ وَمَن قُتِلَ مَظْلُومًا فَقَدْ جَعَلْنَا لِوَلِيِّهِۦ سُلْطَـٰنًا فَلَا يُسْرِف فِّى ٱلْقَتْلِ ۖ إِنَّهُۥ كَانَ مَنصُورًا

    Kuma kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da haƙƙi, kuma wanda aka kashe, yanã wanda aka zãlunta to, haƙĩƙa Mun sanya hujja ga waliyyinsa, sai dai kada ya ƙẽtare haddi a cikin kashẽwar. Lalle shĩ ya kasance wanda ake taimako.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 33 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  34. 34

    وَلَا تَقْرَبُوا۟ مَالَ ٱلْيَتِيمِ إِلَّا بِٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ حَتَّىٰ يَبْلُغَ أَشُدَّهُۥ ۚ وَأَوْفُوا۟ بِٱلْعَهْدِ ۖ إِنَّ ٱلْعَهْدَ كَانَ مَسْـُٔولًا

    Kuma kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce dai da sifa wadda take ita ce mafi kyau, har ya isa ga mafi ƙarfinsa. Kuma ku cika alkawari. Lalle alkawari yã kasance abin tambayãwa ne.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 34 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  35. 35

    وَأَوْفُوا۟ ٱلْكَيْلَ إِذَا كِلْتُمْ وَزِنُوا۟ بِٱلْقِسْطَاسِ ٱلْمُسْتَقِيمِ ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا

    Kuma ku cika mũdu idan kun yi awo, kuma ku auna nauyi da sikẽli madaidaici. Wancan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 35 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  36. 36

    وَلَا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِۦ عِلْمٌ ۚ إِنَّ ٱلسَّمْعَ وَٱلْبَصَرَ وَٱلْفُؤَادَ كُلُّ أُو۟لَـٰٓئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْـُٔولًا

    Kuma kada ka bi abin da bã ka da ilmi game da shi. Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 36 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  37. 37

    وَلَا تَمْشِ فِى ٱلْأَرْضِ مَرَحًا ۖ إِنَّكَ لَن تَخْرِقَ ٱلْأَرْضَ وَلَن تَبْلُغَ ٱلْجِبَالَ طُولًا

    Kuma kada ka yi tafiya a cikin ƙasa da alfahari. Lalle kai bã zã ka hũda ƙasa ba kuma bã zã ka kai a duwãtsu ba ga tsawo.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 37 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  38. 38

    كُلُّ ذَٰلِكَ كَانَ سَيِّئُهُۥ عِندَ رَبِّكَ مَكْرُوهًا

    Dukan wancan mli mũninsa yã kasance abin ƙyãma a wurin Ubangijin ka.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 38 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  39. 39

    ذَٰلِكَ مِمَّآ أَوْحَىٰٓ إِلَيْكَ رَبُّكَ مِنَ ٱلْحِكْمَةِ ۗ وَلَا تَجْعَلْ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ فَتُلْقَىٰ فِى جَهَنَّمَ مَلُومًا مَّدْحُورًا

    Wancan yãnã daga abin da Ubangijinka Ya yi wahayi zuwa gare ka na hikima. Kuma kada ka sanya wani abin bautãwa na daban tãre da Allah har a jẽfa ka a cikin Jahannama kanã wanda ake zargi, wanda ake tunkuɗẽwa[1]

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Wannan shĩ ne ƙarshen muƙãrana tsakãnin shiryarwar da Alƙur'ãni ya kãwo wa dũniya da abin da Attaura ta kãwo wa Banĩ Isrã'ĩla. Kuma akwai daidatãwa a cikinsu a tsakãnin hãlãye mãsu kyau da kĩshiyõyinsu, watau hãlãye mãsu mũni.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 39 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  40. 40

    أَفَأَصْفَىٰكُمْ رَبُّكُم بِٱلْبَنِينَ وَٱتَّخَذَ مِنَ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةِ إِنَـٰثًا ۚ إِنَّكُمْ لَتَقُولُونَ قَوْلًا عَظِيمًا

    Shin fa, Ubangijinku Ya zãɓe ku da ɗiya maza ne, kuma Ya riƙi 'ya'ya mãta daga malã'iku?[1] Lalle ne kũ, haƙĩƙa, kunã faɗar magana mai girma!

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Farkon muƙãrana a tsakãnin al'ãdun mushirikai da shiryarwar Alƙur'ãni dõmin gyãra tunãninsu ga karɓar ĩmãnin tauhĩdi.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 40 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  41. 41

    وَلَقَدْ صَرَّفْنَا فِى هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانِ لِيَذَّكَّرُوا۟ وَمَا يَزِيدُهُمْ إِلَّا نُفُورًا

    Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarrafa bayãni a cikin wannan Alƙur'ãni dõmin su yi tunãni, kuma bã ya ƙãra musu kõme fãce gudu.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 41 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  42. 42

    قُل لَّوْ كَانَ مَعَهُۥٓ ءَالِهَةٌ كَمَا يَقُولُونَ إِذًا لَّٱبْتَغَوْا۟ إِلَىٰ ذِى ٱلْعَرْشِ سَبِيلًا

    Ka ce: "Dã akwai waɗansu abũbuwan bautãwa tãre da shi, kamar yadda suka faɗa, a lõkacin, dã (abũbuwan bautãwar) sun nẽmi wata hanya[1] zuwa ga Ma'abũcin Al'arshi."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Dã su abõkan tãrayyar sun nemi hanya zuwa ga Allah dõmin su yãƙe shi sabõda Ya ce Al'arshi Tãsa ce, Shi kaɗai, dõmin su sãmi nãsu rabon, sabõda Al'arshi tã haɗiye kõme, har da su.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 42 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  43. 43

    سُبْحَـٰنَهُۥ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا يَقُولُونَ عُلُوًّا كَبِيرًا

    TsarkinSa yã tabbata kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke faɗã, ɗaukaka mai girma.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 43 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  44. 44

    تُسَبِّحُ لَهُ ٱلسَّمَـٰوَٰتُ ٱلسَّبْعُ وَٱلْأَرْضُ وَمَن فِيهِنَّ ۚ وَإِن مِّن شَىْءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ بِحَمْدِهِۦ وَلَـٰكِن لَّا تَفْقَهُونَ تَسْبِيحَهُمْ ۗ إِنَّهُۥ كَانَ حَلِيمًا غَفُورًا

    Sammai bakwai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sunã yi Masa tasbĩhi. Kuma bãbu wani abu fãce yanã tasbĩhi game da gõde Masa, kuma amma ba ku fahimtar tasbĩhinsu. Lalle ne shĩ, Ya kasance Mai haƙuri ne, Mai gãfara.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 44 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  45. 45

    وَإِذَا قَرَأْتَ ٱلْقُرْءَانَ جَعَلْنَا بَيْنَكَ وَبَيْنَ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ حِجَابًا مَّسْتُورًا

    Kuma idan ka karanta Alƙur'ani,[1] sai Mu sanya a tsakãninka da tsakanin waɗanda bã su yin ĩmãni da Lãhira wani shãmaki mai suturcẽwa.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Mushirikai jahilai ne, ba su iya ɗaukar jãyayyar magana, sabõda sun fi kusanta zuwa ga dabbõbi ga tunãninsu, bisa gare su zuwa ga mutãne, kõ da yake sauran jikinsu na mutãne ne. Sabõda haka a kõ yaushe sunã kusa ga faɗan tãyar da hankali da dõke-dõke. Sabõda haka Allah Ya sanya tsari ga AnnabinSa da wanda ya bi hanyar Annabin, wajen shiryar da mutãne game da karanta Alƙur'ãni. Bã zã su iya fãɗa mai karanta Alƙur'ãni da dũka ba, kuma tsõronsa suke ji dõmin kwarjinin Alƙur'ãni.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 45 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  46. 46

    وَجَعَلْنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ أَكِنَّةً أَن يَفْقَهُوهُ وَفِىٓ ءَاذَانِهِمْ وَقْرًا ۚ وَإِذَا ذَكَرْتَ رَبَّكَ فِى ٱلْقُرْءَانِ وَحْدَهُۥ وَلَّوْا۟ عَلَىٰٓ أَدْبَـٰرِهِمْ نُفُورًا

    Kuma Mu sanya marufai a kan zukãtansu dõmin kada su fahimce shi, da, wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma idan ka ambaci Ubangijinka, a cikin Alƙur'ãni shĩ kaɗai, sai su jũya a kan bayayyakinsu dõmin gudu.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 46 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  47. 47

    نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَسْتَمِعُونَ بِهِۦٓ إِذْ يَسْتَمِعُونَ إِلَيْكَ وَإِذْ هُمْ نَجْوَىٰٓ إِذْ يَقُولُ ٱلظَّـٰلِمُونَ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا رَجُلًا مَّسْحُورًا

    Mũ ne Mafi sani game da abin da suke saurãre da shi a lõkacin da suke yin saurãren zuwa gare ka, kuma a lõkacin da suke mãsu gãnãwa a tsakãninsu a lõkacin da azzãlumai suke cẽwa, "Bã ku biyar kõwa fãce wani namiji sihirtacce."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 47 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  48. 48

    ٱنظُرْ كَيْفَ ضَرَبُوا۟ لَكَ ٱلْأَمْثَالَ فَضَلُّوا۟ فَلَا يَسْتَطِيعُونَ سَبِيلًا

    Ka dũba yadda suka buga maka misãlai, sai suka ɓace bã su iya sãmun hanya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 48 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  49. 49

    وَقَالُوٓا۟ أَءِذَا كُنَّا عِظَـٰمًا وَرُفَـٰتًا أَءِنَّا لَمَبْعُوثُونَ خَلْقًا جَدِيدًا

    Kuma suka ce: "Shin, idan mun kasance ƙasũsuwa da, niƙaƙƙun gaɓãɓuwa ashe, lalle ne mũ haƙĩƙa, waɗanda ake tãyarwa ne a wata halitta sãbuwa?"

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 49 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  50. 50

    ۞ قُلْ كُونُوا۟ حِجَارَةً أَوْ حَدِيدًا

    Ka ce: "Ku kasance duwãtsu ko kuwa baƙin ƙarfe."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 50 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  51. 51

    أَوْ خَلْقًا مِّمَّا يَكْبُرُ فِى صُدُورِكُمْ ۚ فَسَيَقُولُونَ مَن يُعِيدُنَا ۖ قُلِ ٱلَّذِى فَطَرَكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ ۚ فَسَيُنْغِضُونَ إِلَيْكَ رُءُوسَهُمْ وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هُوَ ۖ قُلْ عَسَىٰٓ أَن يَكُونَ قَرِيبًا

    "Kõ kuwa wata halitta daga abin da yake da girma a cikin ƙirazanku." To zã su ce "Wãne ne zai mayar da mu?" Ka ce: "Wanda Ya ƙaga halittarku a fabkon lõkaci." To, zã su gyaɗa kansu zuwa gare ka, kuma sunã cẽwa, "A yaushene shi?" Ka ce: "Akwai tsammãninsa ya kasance kusa."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 51 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  52. 52

    يَوْمَ يَدْعُوكُمْ فَتَسْتَجِيبُونَ بِحَمْدِهِۦ وَتَظُنُّونَ إِن لَّبِثْتُمْ إِلَّا قَلِيلًا

    "A rãnar da Yake kiran ku, sa'an nan ku riƙa karɓãwa game dã gõde Masa, kuma kunã zaton ba ku zauna ba fãce kaɗan."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 52 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  53. 53

    وَقُل لِّعِبَادِى يَقُولُوا۟ ٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ ۚ إِنَّ ٱلشَّيْطَـٰنَ يَنزَغُ بَيْنَهُمْ ۚ إِنَّ ٱلشَّيْطَـٰنَ كَانَ لِلْإِنسَـٰنِ عَدُوًّا مُّبِينًا

    Kuma ka cẽ wa bãyiNa, su faɗi kalma[1] wadda take mafi kyau. Lalle ne Shaiɗan yanã sanya ɓarna a tsakãninsu. Lalle ne Shaiɗan ya kasance ga mutum, maƙiyi bayyanan ne.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Ka ce wa bãyĩNa, mutãne, idan sunã magana su auna kalmõmin da suke zance da su, sa'an nan su riƙa amfãni da kalma mafi kyãwo dõmin kada shaiɗan ya sãmi mashiga daga maganarsu zuwa ga zukãtansu, ya sanya ɓarna a tsakãninsu.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 53 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  54. 54

    رَّبُّكُمْ أَعْلَمُ بِكُمْ ۖ إِن يَشَأْ يَرْحَمْكُمْ أَوْ إِن يَشَأْ يُعَذِّبْكُمْ ۚ وَمَآ أَرْسَلْنَـٰكَ عَلَيْهِمْ وَكِيلًا

    Ubangijinku ne Mafi sani game da ku. Idan Ya so, zai yi muku rahama, kõ kuwa idan Yã so zai azabtãku. Kuma ba Mu aika ka kanã wakĩli a kansu ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 54 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  55. 55

    وَرَبُّكَ أَعْلَمُ بِمَن فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۗ وَلَقَدْ فَضَّلْنَا بَعْضَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ عَلَىٰ بَعْضٍ ۖ وَءَاتَيْنَا دَاوُۥدَ زَبُورًا

    Kuma Ubangijinka ne Mafi sani game da wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun fĩfĩta sãshen Annabãwa a kan sãshe kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra.[1]

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Muƙãrana a tsakãnin Annabãwa. Allah Yã fĩfĩta waɗansu a kan waɗansu. Falalar Dãwũda a kan waɗansu Annabãwa da Zabũra ne to inã fĩfĩkon wanda aka bai wa Alƙur'ãni mafĩfĩcin littafi da sauran Annabãwa?.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 55 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  56. 56

    قُلِ ٱدْعُوا۟ ٱلَّذِينَ زَعَمْتُم مِّن دُونِهِۦ فَلَا يَمْلِكُونَ كَشْفَ ٱلضُّرِّ عَنكُمْ وَلَا تَحْوِيلًا

    Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya, baicinSa." To, ba su mallakar kuranyẽwar cũta daga gare ku, kuma haka jũyarwa."[1]

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Bã zã su iya jũyar da cũta daga gare ku zuwa ga wani ko kuwa daga wani zuwa gare ku ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 56 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  57. 57

    أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يَدْعُونَ يَبْتَغُونَ إِلَىٰ رَبِّهِمُ ٱلْوَسِيلَةَ أَيُّهُمْ أَقْرَبُ وَيَرْجُونَ رَحْمَتَهُۥ وَيَخَافُونَ عَذَابَهُۥٓ ۚ إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ كَانَ مَحْذُورًا

    Waɗancan, waɗanda suke kiran[1], sunã nẽman tsãni zuwa ga Ubangijinsu. Waɗanne ne suke mafĩfĩta a kusanta? Kuma sunã fãtan sãmun rahamarSa, kuma sunã tsõron azãbarSa. Lalle ne azãbar Ubangijinka ta kasance abar tsõro ce.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Waɗanda kãfirai ke neman tawassuli da su zuwa ga Allah, sũ ma sunã neman abin da zai sãdar da su zuwa ga Allah, sabõda haka bãbu bambanci a tsakãnin mai tawassuli da wanda ake tawassulin da shi ga kusanta zuwa ga Allah. Bãbu mai kusanta zuwa ga Allah sai da taƙawa ga ibãdarSa kawai.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 57 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  58. 58

    وَإِن مِّن قَرْيَةٍ إِلَّا نَحْنُ مُهْلِكُوهَا قَبْلَ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ أَوْ مُعَذِّبُوهَا عَذَابًا شَدِيدًا ۚ كَانَ ذَٰلِكَ فِى ٱلْكِتَـٰبِ مَسْطُورًا

    Kuma bãbu wata alƙarya fãce, Mu ne mãsu halaka ta a gabãnin Rãnar ¡iyãma kõ kuwa Mũ mãsu azãbta ta ne da azãba mai tsanani. Wancan ya kasance a cikin littãfi rubũtacce.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 58 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  59. 59

    وَمَا مَنَعَنَآ أَن نُّرْسِلَ بِٱلْـَٔايَـٰتِ إِلَّآ أَن كَذَّبَ بِهَا ٱلْأَوَّلُونَ ۚ وَءَاتَيْنَا ثَمُودَ ٱلنَّاقَةَ مُبْصِرَةً فَظَلَمُوا۟ بِهَا ۚ وَمَا نُرْسِلُ بِٱلْـَٔايَـٰتِ إِلَّا تَخْوِيفًا

    Kuma bãbu abin da ya hana Mu, Mu aika da ãyõyi fãce sabõda mutãnen farko sun ƙaryata game da su. Kuma Mun bai wa Samũdãwa tãguwa, ãyã bayyananna, sai suka yi zãlunci game da ita. Kuma bã Mu aikãwa da ãyõyi fãce dõmin tsõratarwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 59 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  60. 60

    وَإِذْ قُلْنَا لَكَ إِنَّ رَبَّكَ أَحَاطَ بِٱلنَّاسِ ۚ وَمَا جَعَلْنَا ٱلرُّءْيَا ٱلَّتِىٓ أَرَيْنَـٰكَ إِلَّا فِتْنَةً لِّلنَّاسِ وَٱلشَّجَرَةَ ٱلْمَلْعُونَةَ فِى ٱلْقُرْءَانِ ۚ وَنُخَوِّفُهُمْ فَمَا يَزِيدُهُمْ إِلَّا طُغْيَـٰنًا كَبِيرًا

    Kuma a lõkacin da Muka ce maka, "Lalle ne Ubangijinka Yã kẽwaye mutãne." Kuma ba Mu sanya abin da ya gani wanda[1] Muka nũna maka ba, fãce dõmin fitina ga mutãne, da itãciya wadda aka la'anta a cikin Alƙur'ani. Kuma Munã tsõratar da su, sa'an nan (tsõratarwar) bã ta ƙãra su fãce da kangara mai girma.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Abũbuwan da Annabi ya gani a daren Isrã'i da Mi'irãji, watau tafiyarsa zuwa sama wadda aka yi ishãrã da ita a farkon sũrar. Itãciyar da aka la'anta ita ce Zaƙƙũm abincin mutãnen Wuta. Akwai muƙãrana, a cikin wannan,cħwa ãyõyin da aka bai wa wani Annabi sun fi waɗanda aka bai wa wasu Annabãwa girma.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 60 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  61. 61

    وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسْجُدُوا۟ لِـَٔادَمَ فَسَجَدُوٓا۟ إِلَّآ إِبْلِيسَ قَالَ ءَأَسْجُدُ لِمَنْ خَلَقْتَ طِينًا

    Kuma a lõkacin[1] da Muka cẽ wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu," sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa, ya ce: "shin, zan yi sujada ga wanda ka[2] halitta shi yanã lãka?"

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Muƙãrana a tsakãnin jinsin mutum da malã'iku da aljannu. An fĩfĩtar da jinsin mutum da sanya wa sauran jinsõshi biyu su yi masa sujada, sa'an nan aka ɗaukaka jinsin malã'ika sabõda ɗã'a, kuma aka la'anci jinsin Iblĩsa da sãɓo. [2] Rubũta "ka" da ƙaramin "ka" ne kõ da yake lamĩrin Allah ne, dõmin ya nuna hãlin maganar Shaiɗan zuwa ga Allah Mai girma. Yanã yin maganar da hushi, ba da girmamawa ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 61 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  62. 62

    قَالَ أَرَءَيْتَكَ هَـٰذَا ٱلَّذِى كَرَّمْتَ عَلَىَّ لَئِنْ أَخَّرْتَنِ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ لَأَحْتَنِكَنَّ ذُرِّيَّتَهُۥٓ إِلَّا قَلِيلًا

    Ya ce: "Shin, kã gan ka[1]! Wannan wanda ka girmama a kaina, lalle ne idan ka jinkirtã mini zuwa ga Rãnar ¡iyãma lalle ne, zan tumɓuke zuriyarsa, fãce kaɗan."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Mai sãɓõ sabõda hassada bã ya ganin girman Ubangijinsa. A cikin maganar Iblĩs akwai rashin ladabi da nũna ƙiyayya ga Ãdamu, har zuwa ga zuriyarsa, wadda ba a haifã ba tukuna.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 62 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  63. 63

    قَالَ ٱذْهَبْ فَمَن تَبِعَكَ مِنْهُمْ فَإِنَّ جَهَنَّمَ جَزَآؤُكُمْ جَزَآءً مَّوْفُورًا

    Ya ce: "Ka tafi. Sa'an nan wanda ya bĩ ka daga gare su, to, Jahannama ce sakamakonku, (Mu ba ku shi) sakamako cikakke."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 63 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  64. 64

    وَٱسْتَفْزِزْ مَنِ ٱسْتَطَعْتَ مِنْهُم بِصَوْتِكَ وَأَجْلِبْ عَلَيْهِم بِخَيْلِكَ وَرَجِلِكَ وَشَارِكْهُمْ فِى ٱلْأَمْوَٰلِ وَٱلْأَوْلَـٰدِ وَعِدْهُمْ ۚ وَمَا يَعِدُهُمُ ٱلشَّيْطَـٰنُ إِلَّا غُرُورًا

    "Kuma ka rikitar da wanda ka sãmi ĩko a kansa, daga gare su, da sautinka, kuma ka yi hari a kansu da dawãkinka da dãkãrunka kuma ka yi tãrẽwa da su a cikin dũkiyõyi da ɗiyã, kumaka yi musu wa'adi. Alhãli kuwa Shaiɗan bã ya yi musu wa'adin kõme fãce da ruɗi."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 64 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  65. 65

    إِنَّ عِبَادِى لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَـٰنٌ ۚ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ وَكِيلًا

    "Lalle ne bãyiNa, bã ka da wani ƙarfi a kansu. Kuma Ubangijinka Ya isa Ya zama wakĩli."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 65 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  66. 66

    رَّبُّكُمُ ٱلَّذِى يُزْجِى لَكُمُ ٱلْفُلْكَ فِى ٱلْبَحْرِ لِتَبْتَغُوا۟ مِن فَضْلِهِۦٓ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِكُمْ رَحِيمًا

    Ubangijinku ne Yake gudãnar da jirgi a cikin tẽku, dõmin ku nema daga falalarSa. Lalle ne Shĩ, Yã kasance a gare ku Mai jin ƙai.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 66 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  67. 67

    وَإِذَا مَسَّكُمُ ٱلضُّرُّ فِى ٱلْبَحْرِ ضَلَّ مَن تَدْعُونَ إِلَّآ إِيَّاهُ ۖ فَلَمَّا نَجَّىٰكُمْ إِلَى ٱلْبَرِّ أَعْرَضْتُمْ ۚ وَكَانَ ٱلْإِنسَـٰنُ كَفُورًا

    Kuma idan cũta ta shãfe ku, a cikin tẽku, sai wanda kuke kira ya ɓace fãce Shi. To, a lõkacin da Ya tsira da ku zuwa, ga tudu sai kuka bijire. Kuma mutum ya kasance mai yawan butulci.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 67 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  68. 68

    أَفَأَمِنتُمْ أَن يَخْسِفَ بِكُمْ جَانِبَ ٱلْبَرِّ أَوْ يُرْسِلَ عَلَيْكُمْ حَاصِبًا ثُمَّ لَا تَجِدُوا۟ لَكُمْ وَكِيلًا

    Shin fa kun amince cẽwa (Allah) bã Ya shãfe gẽfen ƙasa game da ku kõ kuwa Ya aika da iska mai tsakuwa a kanku, sa'an nan kuma bã zã ku sãmi wani wakĩli ba dõminku?

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 68 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  69. 69

    أَمْ أَمِنتُمْ أَن يُعِيدَكُمْ فِيهِ تَارَةً أُخْرَىٰ فَيُرْسِلَ عَلَيْكُمْ قَاصِفًا مِّنَ ٱلرِّيحِ فَيُغْرِقَكُم بِمَا كَفَرْتُمْ ۙ ثُمَّ لَا تَجِدُوا۟ لَكُمْ عَلَيْنَا بِهِۦ تَبِيعًا

    Ko kun amince ga Ya mayar da ku a cikin tẽkun a wani lõkaci na dabam, sa'an na Ya aika wata gũguwa mai karya abũbuwa daga iska, har ya nutsar da ku sabõda abin da kuka yi na kãfirci? Sa'an nan kuma bã ku sãmun mai bin hakki sabõda ku, a kanMu, game da Shi.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 69 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  70. 70

    ۞ وَلَقَدْ كَرَّمْنَا بَنِىٓ ءَادَمَ وَحَمَلْنَـٰهُمْ فِى ٱلْبَرِّ وَٱلْبَحْرِ وَرَزَقْنَـٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَـٰتِ وَفَضَّلْنَـٰهُمْ عَلَىٰ كَثِيرٍ مِّمَّنْ خَلَقْنَا تَفْضِيلًا

    Kuma lalle ne Mun girmama 'yan Adam[1], kuma Muka ɗauke su a cikin ƙasa da tẽku kuma Muka azurta su daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma Muka fĩfĩta su a kan mãsu yawa daga waɗanda Muka halitta, fĩfĩtãwa.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Muƙãrana a tsakãnin jinsin mutum da sauran halittar Allah.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 70 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  71. 71

    يَوْمَ نَدْعُوا۟ كُلَّ أُنَاسٍۭ بِإِمَـٰمِهِمْ ۖ فَمَنْ أُوتِىَ كِتَـٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ يَقْرَءُونَ كِتَـٰبَهُمْ وَلَا يُظْلَمُونَ فَتِيلًا

    A rãnar da Muke kiran[1] kõwane mutãne da lĩmãminsu to, wanda aka bai wa littafinsa a dã, mansa, to, waɗannan sunã karãtun littãfinsu, kuma bã a zãluntar su da zaren bãkin gurtsin dabĩno.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Muƙãrana a Lãhira a tsakãnin al'ummõmi kuma da tsakãnin mũminai da kãfirai,.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 71 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  72. 72

    وَمَن كَانَ فِى هَـٰذِهِۦٓ أَعْمَىٰ فَهُوَ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ أَعْمَىٰ وَأَضَلُّ سَبِيلًا

    Kuma wanda ya kasance makãho[1] a cikin wannan sabõda haka shi a Lãhira makãho ne kuma mafi ɓata ga hanya.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Muƙarana a tsakãnin makantar basĩra da makantar ganin ido.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 72 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  73. 73

    وَإِن كَادُوا۟ لَيَفْتِنُونَكَ عَنِ ٱلَّذِىٓ أَوْحَيْنَآ إِلَيْكَ لِتَفْتَرِىَ عَلَيْنَا غَيْرَهُۥ ۖ وَإِذًا لَّٱتَّخَذُوكَ خَلِيلًا

    Kuma lalle ne sun yi kusa haƙĩƙa, su fitinẽ ka daga abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, dõmin ka ƙirƙira waninsa a gare Mu, a lõkacin, haƙĩƙa, dã sun riƙe ka masoyi.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 73 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  74. 74

    وَلَوْلَآ أَن ثَبَّتْنَـٰكَ لَقَدْ كِدتَّ تَرْكَنُ إِلَيْهِمْ شَيْـًٔا قَلِيلًا

    Kuma bã dõmin[1] Mun tabbatar da kai ba, lalle ne, haƙĩƙa, dã kã yi kusa ka karkata zuwa gare su ta wani abu kaɗan.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Muƙãrana a tsakãnin sarauta da Manzancin Allah. Sarkin dũniya yanã canja manufarsa dõmin neman yardar mutãnensa. Amman Manzon Allah bã ya sãke abin da Allah Ya umurce shi da shi dõmin neman yardar Mutãne.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 74 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  75. 75

    إِذًا لَّأَذَقْنَـٰكَ ضِعْفَ ٱلْحَيَوٰةِ وَضِعْفَ ٱلْمَمَاتِ ثُمَّ لَا تَجِدُ لَكَ عَلَيْنَا نَصِيرًا

    A lõkacin, lalle ne, dã Mun ɗanɗana maka ninkin azãbar rãyuwa da ninkin azãbar mutuwa, sa'an nan kuma bã zã ka sãmi mataimaki ba a kanMu.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 75 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  76. 76

    وَإِن كَادُوا۟ لَيَسْتَفِزُّونَكَ مِنَ ٱلْأَرْضِ لِيُخْرِجُوكَ مِنْهَا ۖ وَإِذًا لَّا يَلْبَثُونَ خِلَـٰفَكَ إِلَّا قَلِيلًا

    Kuma lalle ne, sun[1] yi kusa, haƙĩƙa, su tãyar da hankalinka daga ƙasar, dõmin su fitar da kai daga gare ta. Kuma a lõkacin, bã zã su zauna ba a kan sãɓãninka fãce kaɗan.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Muƙãrana a tsakãnin mai aiki dõmin Allah, bã a iya jũyar da shi daga aikinsa dõmin neman wata kamãla, amma mai aikin dũniya anã iya canja shi dõmin haka. Kuma bambancin hijira da kõra waɗanda suka kõri Annabinsu sai a halaka su, amma waɗanda Annabinsu ya yi hijira gabãnin azãba, to, bã zã a halaka su ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 76 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  77. 77

    سُنَّةَ مَن قَدْ أَرْسَلْنَا قَبْلَكَ مِن رُّسُلِنَا ۖ وَلَا تَجِدُ لِسُنَّتِنَا تَحْوِيلًا

    Hanyar waɗanda, haƙĩƙa, Muka aika a gabãninka, daga ManzanninMu, kuma bã zã ka sãmi jũyarwa ba ga hanyar Mu.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 77 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  78. 78

    أَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِدُلُوكِ ٱلشَّمْسِ إِلَىٰ غَسَقِ ٱلَّيْلِ وَقُرْءَانَ ٱلْفَجْرِ ۖ إِنَّ قُرْءَانَ ٱلْفَجْرِ كَانَ مَشْهُودًا

    Ka tsayar da salla[1] a karkatar rãnã zuwa ga duhun dare da lõkacin fitar alfijir[2] lalle ne karãtun fitar alfijir ya kasance wanda ake halarta.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Tsayar da salla a cikin lõkutanta, shi ne yake hana a yaudari mutum da magana har a sanya shi ya yi abin da bai kamãta ba, ko kuma ya yi abin da sharĩ'a ta hana. [2] Karãtun fitar alfijir, ana nufin sallar asuba. Sabõda haka anã son dõgon karãtu a cikinta, gwargwadon fãrã ta a duhun dare a bayan fitar Alfijir.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 78 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  79. 79

    وَمِنَ ٱلَّيْلِ فَتَهَجَّدْ بِهِۦ نَافِلَةً لَّكَ عَسَىٰٓ أَن يَبْعَثَكَ رَبُّكَ مَقَامًا مَّحْمُودًا

    Kuma da dare, sai ka yi hĩra[1] da shi (Alƙur'ãni) akan ƙãri gare ka. Akwai tsammãnin Ubangijin ka Ya tãyar da kai a wani matsayi gõdadde.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Hĩra da Alƙur'ãni, watau a yi sallõlin nãfila na dare, shafa'i bibbiyu, a ƙãre da wutri. Ga Annabi tahajjudi da wutrin wãjibi ne ƙãri a kan abin da aka ɗõra wa sauran mutãne, a lõkacin da yake zaune a gida. Ga sauran mutãne wutri sunna ce, kamar sallõlin ĩdi da rõkon ruwa da husũfin rãnã da na wata. A nan akwai bambanci a tsakãnin Annabi da jama'arsa a wajen wutri.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 79 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  80. 80

    وَقُل رَّبِّ أَدْخِلْنِى مُدْخَلَ صِدْقٍ وَأَخْرِجْنِى مُخْرَجَ صِدْقٍ وَٱجْعَل لِّى مِن لَّدُنكَ سُلْطَـٰنًا نَّصِيرًا

    Kuma ka ce: "Yã Ubangijĩna[1]! Ka shigar, da ni shigar gaskiya, kuma Ka fitar da ni fitar gaskiya. Kuma Ka sanya mini, daga gun Ka, wani ƙarfi mai taimako."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Kuma ka yi addu'a a cikin sallarka da bãyanta da wannan addu'a dõmin ta nũna sallamãwarka ga Ubangijinka Allah.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 80 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  81. 81

    وَقُلْ جَآءَ ٱلْحَقُّ وَزَهَقَ ٱلْبَـٰطِلُ ۚ إِنَّ ٱلْبَـٰطِلَ كَانَ زَهُوقًا

    Kuma ka ce: "Gaskiya tã zo, kuma ƙarya ta lãlãce. Lalle ne ƙarya ta kasance lãlãtacciya."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 81 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  82. 82

    وَنُنَزِّلُ مِنَ ٱلْقُرْءَانِ مَا هُوَ شِفَآءٌ وَرَحْمَةٌ لِّلْمُؤْمِنِينَ ۙ وَلَا يَزِيدُ ٱلظَّـٰلِمِينَ إِلَّا خَسَارًا

    Kuma Munã sassaukarwa daga Alƙur'ãni, abin da yake waraka ne da rahama ga mũminai. Kuma bã ya ƙãra wa azzãlumai (kõme) fãce hasãra.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 82 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  83. 83

    وَإِذَآ أَنْعَمْنَا عَلَى ٱلْإِنسَـٰنِ أَعْرَضَ وَنَـَٔا بِجَانِبِهِۦ ۖ وَإِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ كَانَ يَـُٔوسًا

    Kuma idan Muka yi ni'ima a kan mutum,[1] sai ya hinjire, kuma ya nĩsanta da gefensa, kuma idan sharri ya shãfe shi, sai ya kasance mai yanke ƙauna.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Muƙãrana a tsakãnin hãlãye biyu na mutum, hãlin tsanani da hãlin cũta.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 83 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  84. 84

    قُلْ كُلٌّ يَعْمَلُ عَلَىٰ شَاكِلَتِهِۦ فَرَبُّكُمْ أَعْلَمُ بِمَنْ هُوَ أَهْدَىٰ سَبِيلًا

    Ka ce: "Kõwa ya yi aiki a kan hanyarsa. Sa'an nan Ubangijinka ne Mafi sani ga wanda yake mafi shiryuwa ga Hanya."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 84 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  85. 85

    وَيَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلرُّوحِ ۖ قُلِ ٱلرُّوحُ مِنْ أَمْرِ رَبِّى وَمَآ أُوتِيتُم مِّنَ ٱلْعِلْمِ إِلَّا قَلِيلًا

    Sunã tambayar ka ga rũhi. Ka ce: "Rũhi daga al'amarin Ubangijina ne, kuma ba a bã ku (kõme) ba daga ilmi fãce kaɗan."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 85 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  86. 86

    وَلَئِن شِئْنَا لَنَذْهَبَنَّ بِٱلَّذِىٓ أَوْحَيْنَآ إِلَيْكَ ثُمَّ لَا تَجِدُ لَكَ بِهِۦ عَلَيْنَا وَكِيلًا

    Kuma lalle ne idan Mun so, haƙĩƙa, Munã tafiya da abinda Muka yi wahayi zuwa gare ka. Sa'an nan kuma bã za ka sãmi wani wakĩli ba dõminka game da shi a kanMu.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 86 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  87. 87

    إِلَّا رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ ۚ إِنَّ فَضْلَهُۥ كَانَ عَلَيْكَ كَبِيرًا

    Fãce da rahama daga Ubangijinka. Lalle ne falalarSa ta kasance mai girma a kanka.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 87 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  88. 88

    قُل لَّئِنِ ٱجْتَمَعَتِ ٱلْإِنسُ وَٱلْجِنُّ عَلَىٰٓ أَن يَأْتُوا۟ بِمِثْلِ هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانِ لَا يَأْتُونَ بِمِثْلِهِۦ وَلَوْ كَانَ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ ظَهِيرًا

    Ka ce: "Lalle ne idan mutãne da aljannu sun tãru a kan su zo da misãlin wannan Alƙur'ãni bã zã su zo da misãlinsa ba, kuma kõ dã sãshinsu yã kasance, mataimaki ga sãshi."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 88 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  89. 89

    وَلَقَدْ صَرَّفْنَا لِلنَّاسِ فِى هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانِ مِن كُلِّ مَثَلٍ فَأَبَىٰٓ أَكْثَرُ ٱلنَّاسِ إِلَّا كُفُورًا

    Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun caccanza dõmin mutãne, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli sai mafi yawan mutãne suka ƙi (kõme) fãce kãfirci,

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 89 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  90. 90

    وَقَالُوا۟ لَن نُّؤْمِنَ لَكَ حَتَّىٰ تَفْجُرَ لَنَا مِنَ ٱلْأَرْضِ يَنۢبُوعًا

    Kuma suka ce: "Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka sai kã ɓuɓɓugar[1] da idan ruwa daga ƙasa.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Kãfiri bã ya iya hangen abinda bã a iya taɓa shi da gaɓoɓin ji na jiki, dõmin haka suka nemi ɗayan waɗannan abũbuwa ya auku kãmin su yi ĩmãni. Mũmini yanã kange da ganin basĩra, dõmin haka ya wadãtu da zaman Alƙur'ani ãyã mai isa ga ya yi ĩmãni da shi.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 90 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  91. 91

    أَوْ تَكُونَ لَكَ جَنَّةٌ مِّن نَّخِيلٍ وَعِنَبٍ فَتُفَجِّرَ ٱلْأَنْهَـٰرَ خِلَـٰلَهَا تَفْجِيرًا

    "Kõ kuma wata gõna daga dabĩnai da inabi ta kasance a gare ka. Sa'an nan ka ɓuɓɓugar da ƙõramu a tsakãninta ɓuɓɓugarwa."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 91 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  92. 92

    أَوْ تُسْقِطَ ٱلسَّمَآءَ كَمَا زَعَمْتَ عَلَيْنَا كِسَفًا أَوْ تَأْتِىَ بِٱللَّهِ وَٱلْمَلَـٰٓئِكَةِ قَبِيلًا

    "Kõ kuwa ka kãyar da sama a kanmu kaɓukka kõ kuwa ka zo da Allah, da malã'iku banga-banga."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 92 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  93. 93

    أَوْ يَكُونَ لَكَ بَيْتٌ مِّن زُخْرُفٍ أَوْ تَرْقَىٰ فِى ٱلسَّمَآءِ وَلَن نُّؤْمِنَ لِرُقِيِّكَ حَتَّىٰ تُنَزِّلَ عَلَيْنَا كِتَـٰبًا نَّقْرَؤُهُۥ ۗ قُلْ سُبْحَانَ رَبِّى هَلْ كُنتُ إِلَّا بَشَرًا رَّسُولًا

    "Kõ kuwa wani gida na zĩnãriya ya kasance a gare ka, kõ kuwa ka tãka a cikin sama. Kuma bã zã mu yi ĩmãni ba ga tãkawarka, sai ka sassaukõ da wani littãfi a kanmu, munã karantã shi." Ka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijĩna! Ban kasance ba fãce mutum, Manzo."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 93 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  94. 94

    وَمَا مَنَعَ ٱلنَّاسَ أَن يُؤْمِنُوٓا۟ إِذْ جَآءَهُمُ ٱلْهُدَىٰٓ إِلَّآ أَن قَالُوٓا۟ أَبَعَثَ ٱللَّهُ بَشَرًا رَّسُولًا

    Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni, a lõkacin da shiriya ta jẽ musu, fãce sunce, "Shin, Allah zai aiko mutum ya zamo yana Manzo."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 94 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  95. 95

    قُل لَّوْ كَانَ فِى ٱلْأَرْضِ مَلَـٰٓئِكَةٌ يَمْشُونَ مُطْمَئِنِّينَ لَنَزَّلْنَا عَلَيْهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَلَكًا رَّسُولًا

    Ka ce: "Dã malã'iku sun kasance a cikin ƙasa, kuma sunã tafiya, sunã masu natsuwa, lalle ne dã mun saukar da malã'ika daga sama ya zama manzo a kansu."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 95 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  96. 96

    قُلْ كَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدًۢا بَيْنِى وَبَيْنَكُمْ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرًۢا بَصِيرًا

    Ka ce: "Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da ku. Lalle Shi Ya kasance ga bãyinsa, mai ƙididdigewa ne Mai gani."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 96 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  97. 97

    وَمَن يَهْدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلْمُهْتَدِ ۖ وَمَن يُضْلِلْ فَلَن تَجِدَ لَهُمْ أَوْلِيَآءَ مِن دُونِهِۦ ۖ وَنَحْشُرُهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمْ عُمْيًا وَبُكْمًا وَصُمًّا ۖ مَّأْوَىٰهُمْ جَهَنَّمُ ۖ كُلَّمَا خَبَتْ زِدْنَـٰهُمْ سَعِيرًا

    Kuma wanda Allah Ya shiryar, to, shĩ ne shiryayye, kuma wanda Ya ɓatar to bã zã ka sãmi waɗansu masõya gare su ba baicinSa. Kuma Munã tãra su a Rãnar ¡iyãma a kan fuskõkinsu, sunã makãfi, kuma bẽbãye da kurãme. Matattararsu Jahannama ce, kõ da yaushe ta bice, sai Mu ƙãra musu wata wuta mai tsanani.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 97 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  98. 98

    ذَٰلِكَ جَزَآؤُهُم بِأَنَّهُمْ كَفَرُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا وَقَالُوٓا۟ أَءِذَا كُنَّا عِظَـٰمًا وَرُفَـٰتًا أَءِنَّا لَمَبْعُوثُونَ خَلْقًا جَدِيدًا

    Wancan ne sãkamakonsu sabõda lalle sũ, sun kãfirta da ãyõ yinMu, kuma suka ce: "Shin idan muka kasance ƙasũsuwa da nĩƙaƙƙun gaɓũɓuwa, shin lalle mũ, haƙĩ ka, waɗanda ake tãyarwa ne a cikin wata halitta sãbuwa?"

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 98 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  99. 99

    ۞ أَوَلَمْ يَرَوْا۟ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِى خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ قَادِرٌ عَلَىٰٓ أَن يَخْلُقَ مِثْلَهُمْ وَجَعَلَ لَهُمْ أَجَلًا لَّا رَيْبَ فِيهِ فَأَبَى ٱلظَّـٰلِمُونَ إِلَّا كُفُورًا

    Shin, kuma ba su ganĩ[1] ba (cẽwa) lalle ne Allah, wandaYa halicci sammai da ƙasa, Mai ikon yi ne a kan Ya halicci misãlinsu? Kuma Ya sanya wani ajali wanda bãbu kõkwanto a cikinsa? Sai azzãlumai suka ƙi fãce kãfirci.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Muƙãrana a tsakãnin farkon halitta da mayarwa da ita, idan fãrãwa ba ta buwãya ba, mayarwa bã zã ta buwãya ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 99 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  100. 100

    قُل لَّوْ أَنتُمْ تَمْلِكُونَ خَزَآئِنَ رَحْمَةِ رَبِّىٓ إِذًا لَّأَمْسَكْتُمْ خَشْيَةَ ٱلْإِنفَاقِ ۚ وَكَانَ ٱلْإِنسَـٰنُ قَتُورًا

    Ka ce: "Dã dai kũ, kunã mallakar[1] taskõkin rahamar Ubangijĩna, a lõkacin, haƙĩƙa dã kun kãme dõmin tsõron ƙãrẽwar taskõkin. Kuma mutum yã kasance mai ƙwauro ne."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Muƙãrana a tsakãnin kyautar mutum da rõwarsa ga dũkiyar da ya mallaka.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 100 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  101. 101

    وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا مُوسَىٰ تِسْعَ ءَايَـٰتٍۭ بَيِّنَـٰتٍ ۖ فَسْـَٔلْ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ إِذْ جَآءَهُمْ فَقَالَ لَهُۥ فِرْعَوْنُ إِنِّى لَأَظُنُّكَ يَـٰمُوسَىٰ مَسْحُورًا

    Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun bai wa Mũsã ãyõyi[1] guda tara bayyanannu, sai ka tambayi Banĩ Isrã'ila, a lõkacin da ya jẽ musu, sai Fir'auna ya ce masa, "Lalle nĩ, inã zaton ka, ya Mũsã, sihirtacce."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Muƙãrana a tsakãnin maganar makangari Fir'auna da Manzon Allah, Mũsã dõmin nũna ãyar Annabãwa ba su tsõron kõwa wajen iyar da Manzancin Allah, kuma bã su ganin wani ƙarfi a gabansu fãce na Allah.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 101 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  102. 102

    قَالَ لَقَدْ عَلِمْتَ مَآ أَنزَلَ هَـٰٓؤُلَآءِ إِلَّا رَبُّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ بَصَآئِرَ وَإِنِّى لَأَظُنُّكَ يَـٰفِرْعَوْنُ مَثْبُورًا

    Ya ce: "lalle ne haƙĩƙa ka sani bãbu wanda ya saukar da waɗannan, fãce Ubangijin sammai da ƙasa dõmĩn su zama abũbuwan lũra. Kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, ina zaton ka, yã Fir'auna, halakakke."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 102 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  103. 103

    فَأَرَادَ أَن يَسْتَفِزَّهُم مِّنَ ٱلْأَرْضِ فَأَغْرَقْنَـٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ جَمِيعًا

    Sai ya yi nufin fitar da su daga ƙasar, sai Muka nutsar da shi, shi da wanda yake tãre da shi gabã ɗaya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 103 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  104. 104

    وَقُلْنَا مِنۢ بَعْدِهِۦ لِبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱسْكُنُوا۟ ٱلْأَرْضَ فَإِذَا جَآءَ وَعْدُ ٱلْـَٔاخِرَةِ جِئْنَا بِكُمْ لَفِيفًا

    Kuma Muka ce: daga bãyansa ga Banĩ Isrã'ĩla, "Ku zauni ƙasar. Sa'an nan idan wa'adin ƙarshe ya zo, zã Mu jẽ da ku jama'a-jama'a."[1]

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Wannan magana tanã kamã da da'awar Yahũdu cewa yanã rubuce a cikin littãfinsu za su kõma haɗuwa bãyan rarraba a nan dũniya kuma Hadĩsin kõmawar Yahũdu a Falasɗĩnu, har Musulmi su yi yãƙi da su, sunã a kan gãɓar gabas kuma su Yahũdãwa suna a kan gãɓar yamma daga Kõgin Urdun yanã ƙarfafa wannan ra'ayi. Kuma an ruwaito cewa daga cikin alãmõmin Tãshin Ƙiyãma akwai kõmãwar Yahũdu a Falasɗinu. Allah ne Mafi sani.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 104 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  105. 105

    وَبِٱلْحَقِّ أَنزَلْنَـٰهُ وَبِٱلْحَقِّ نَزَلَ ۗ وَمَآ أَرْسَلْنَـٰكَ إِلَّا مُبَشِّرًا وَنَذِيرًا

    Kuma da gaskiya Muka saukar da shi, kuma da gaskiya ya sauka. Kuma ba Mu aike ka ba fãce kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 105 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  106. 106

    وَقُرْءَانًا فَرَقْنَـٰهُ لِتَقْرَأَهُۥ عَلَى ٱلنَّاسِ عَلَىٰ مُكْثٍ وَنَزَّلْنَـٰهُ تَنزِيلًا

    Kuma yanã abin karãtu Mun rarraba shi dõmin ka karanta shi ga mutane a kan jinkiri kuma Mun sassaukar da shi sassaukarwa.[1]

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Saukar da Alƙur'ãni a cikin shekaru ashirin ko ashirin da uku ya yi kama da saukar ãyõyin Mũsã tãre a lõkacin da yake kiran Fir'auna zuwa ga addini.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 106 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  107. 107

    قُلْ ءَامِنُوا۟ بِهِۦٓ أَوْ لَا تُؤْمِنُوٓا۟ ۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ مِن قَبْلِهِۦٓ إِذَا يُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ يَخِرُّونَ لِلْأَذْقَانِ سُجَّدًا

    Ka ce: "Ku yi ĩmãni[1] da Shi, ko kuwa kada ku yi ĩmãni, lalle ne waɗanda aka bai wa ilmi daga gabãninsa, idan anã karãtunsa a kansu, sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu, sunã mãsu sujada."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Muƙãranar yin ĩmãni da rashin ĩmãnin mutãne ga Alƙur'ãni ba zai rage gaskiyarsa da kõme ba, sai dai waɗanda suka ƙi ĩmãnin ne zã su cũtu, sa'an nan da bambanci a tsakãnin mai ilmi da jãhili. Mai ilmi yanã da sauƙin jãwuwa zuwa ga gaskiya har ya rasa abin da zai aikata fãce ya fãɗi rikice, a kan haɓarsa, yanã mayar da al'amari ga Allah kuma yanã tawali'u.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 107 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  108. 108

    وَيَقُولُونَ سُبْحَـٰنَ رَبِّنَآ إِن كَانَ وَعْدُ رَبِّنَا لَمَفْعُولًا

    "Kuma sunã cẽwa: Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle ne wa'adin Ubangijinmu ya kasance, haƙĩƙa, abin aikatãwa."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 108 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  109. 109

    وَيَخِرُّونَ لِلْأَذْقَانِ يَبْكُونَ وَيَزِيدُهُمْ خُشُوعًا ۩

    Kuma sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu sunã kũka, kuma yanã ƙara musu tsõro.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 109 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  110. 110

    قُلِ ٱدْعُوا۟ ٱللَّهَ أَوِ ٱدْعُوا۟ ٱلرَّحْمَـٰنَ ۖ أَيًّا مَّا تَدْعُوا۟ فَلَهُ ٱلْأَسْمَآءُ ٱلْحُسْنَىٰ ۚ وَلَا تَجْهَرْ بِصَلَاتِكَ وَلَا تُخَافِتْ بِهَا وَٱبْتَغِ بَيْنَ ذَٰلِكَ سَبِيلًا

    Ka ce: "Ku kirayi Allah[1] kõ kuwa ku kirãyi Mai rahama. Kõwane kuka kira to Yanã da sũnãye mafi kyau. Kuma, kada ka bayyana[2] ga sallarka, kuma kada ka ɓõye ta. Ka nẽmi hanya a tsakãnin wancan."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Muƙarana a tsakãnin sũnayen Allah waɗanda ake kiran sa da su wajen rõƙo da waɗanda bã a yin roko da su. Sũnãyen mafiya kyau da ake kiran Allah da su Hadĩsi ya kãwo su sai a nħma daga Jalãlaini. [2] Kuma tsakaitãwa wajen karãtun salla ko addu'a kamar yadda aikin Annabi ya nũna yadda ake yi, kada a bayyana kada a ɓõye. Sai dai tsaka.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 110 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  111. 111

    وَقُلِ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ ٱلَّذِى لَمْ يَتَّخِذْ وَلَدًا وَلَمْ يَكُن لَّهُۥ شَرِيكٌ فِى ٱلْمُلْكِ وَلَمْ يَكُن لَّهُۥ وَلِىٌّ مِّنَ ٱلذُّلِّ ۖ وَكَبِّرْهُ تَكْبِيرًۢا

    Kuma ka ce: "Gõdiyã[1] ta tabbata ga Allah wanda bai riƙi ɗã ba kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa, kuma wani masõyi sabõda wulãkancin bai kasance a gare Shi ba." Kuma ka girmama Shi, girmamãwa.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Ka ce: "Allah ba Shi da abõkin muƙãrana a kõwace jiha. Shi kaɗai Ya cancanci girmamãwa." Sabõda haka ka girmama Shi, girmãmãwar da ta dãce da Shi.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 111 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
Rufewar sura: Tafsirin As-Sa'di (Larabci)

تم تفسير سورة الإسراء ولله الحمد والمنة والثناء الحسن على يد جامعه عبد الرحمن بن ناصر بن عبد الله بن سعدي. غفر الله له ولوالديه ولجميع المسلمين. آمين. وصلى الله على محمد وسلم تسليماً كثيراً. وذلك في 7 جمادى الأولى سنة 1344 هـ. ونقلته من خط المؤلف بقلم الفقير إلى ربه سليمان الحمد البسام غفر الله له ولوالديه ولجميع المسلمين. آمين. وصلى الله على محمد وعلى آله وصحبه أجمعين. آمين ثم آمين.

Tafsirin As-Sa'di, Larabci v1.0.0, QuranEnc.com

Tafsiri

Sura ta gabaAl-Kahfالكهف

Rubutun Alƙur'ani: Tanzil

Ba da rahoton kuskure

Ƙari