ق

Ƙaf

ayoyi 45MakkiyaJuzu'i 26

Mahmoud Khalil Al-HussaryHafsu daga Asim - Murattal

Saitunan karatu

Jagorar launukan tajwidi

Sunaye, misalai da layukan ƙasa iri-iri suna bayyana ƙa'idojin baya ga launi. An ɗauko misalan daga rubutun Alƙur'ani da aka wallafa.

Gunna
وَمِمَّا2:3
Nau'o'in Ikhfa'i
يُنفِقُونَ2:3
Nau'o'in Idgami
هُدًى لِّلْمُتَّقِينَ2:2
Iƙlabi
أَلِيمٌۢ بِمَا2:10
Ƙalƙala
رَزَقْنَـٰهُمْ2:3
Madda: harka 2
ٱلرَّحْمَـٰنِ1:1
Madda: harka 2, 4 ko 6
ٱلرَّحِيمِ1:1
Madda: harka 4 ko 5
بِمَآ2:4
Madda: harka 6
ٱلضَّآلِّينَ1:7
Hamzatul wasli
ٱللَّهِ1:1
Lam Shamsiyya
ٱلرَّحْمَـٰنِ1:1
Haruffan da ba a furtawa
ٱلصَّلَوٰةَ2:3

Alamomin tajwidi: cpfair/quran-tajweed (CC BY 4.0), an gina su daga ReciteQuran.com da mus'hafan tajwidi na Dar al-Maarifah; an daidaita wurarensu da rubutun Tanzil na yanzu.

Gabatarwar sura: Tafsirin As-Sa'di (Larabci)

تفسير سورة ق

وهي مكية

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Tafsirin As-Sa'di, Larabci v1.0.0, QuranEnc.com

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Fassarar Hausa - Abubakar Gumi. Siga: 1.2.2. Sabuntawa ta ƙarshe: 2025-06-26. QuranEnc.com

  1. 1

    قٓ ۚ وَٱلْقُرْءَانِ ٱلْمَجِيدِ

    K. Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 1 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  2. 2

    بَلْ عَجِبُوٓا۟ أَن جَآءَهُم مُّنذِرٌ مِّنْهُمْ فَقَالَ ٱلْكَـٰفِرُونَ هَـٰذَا شَىْءٌ عَجِيبٌ

    Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 2 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  3. 3

    أَءِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا ۖ ذَٰلِكَ رَجْعٌۢ بَعِيدٌ

    "Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 3 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  4. 4

    قَدْ عَلِمْنَا مَا تَنقُصُ ٱلْأَرْضُ مِنْهُمْ ۖ وَعِندَنَا كِتَـٰبٌ حَفِيظٌۢ

    Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurin Mu akwai wani littãfi mai tsarẽwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 4 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  5. 5

    بَلْ كَذَّبُوا۟ بِٱلْحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمْ فَهُمْ فِىٓ أَمْرٍ مَّرِيجٍ

    Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 5 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  6. 6

    أَفَلَمْ يَنظُرُوٓا۟ إِلَى ٱلسَّمَآءِ فَوْقَهُمْ كَيْفَ بَنَيْنَـٰهَا وَزَيَّنَّـٰهَا وَمَا لَهَا مِن فُرُوجٍ

    Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi?

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 6 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  7. 7

    وَٱلْأَرْضَ مَدَدْنَـٰهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَٰسِىَ وَأَنۢبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍۭ بَهِيجٍ

    Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa?

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 7 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  8. 8

    تَبْصِرَةً وَذِكْرَىٰ لِكُلِّ عَبْدٍ مُّنِيبٍ

    Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali?

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 8 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  9. 9

    وَنَزَّلْنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً مُّبَـٰرَكًا فَأَنۢبَتْنَا بِهِۦ جَنَّـٰتٍ وَحَبَّ ٱلْحَصِيدِ

    Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 9 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  10. 10

    وَٱلنَّخْلَ بَاسِقَـٰتٍ لَّهَا طَلْعٌ نَّضِيدٌ

    Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 10 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  11. 11

    رِّزْقًا لِّلْعِبَادِ ۖ وَأَحْيَيْنَا بِهِۦ بَلْدَةً مَّيْتًا ۚ كَذَٰلِكَ ٱلْخُرُوجُ

    Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 11 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  12. 12

    كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ وَأَصْحَـٰبُ ٱلرَّسِّ وَثَمُودُ

    Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, [1]da Samũdãwa.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Rassi sunan wata rijĩya ce. Mutãnenta na zaune a gefenta da dabbõbinsu, sunã bauta wa gumãka, aka aika musu wani Annabi, anã ce da shi Hanzala bn safwan kõ kuma waninsa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 12 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  13. 13

    وَعَادٌ وَفِرْعَوْنُ وَإِخْوَٰنُ لُوطٍ

    Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 13 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  14. 14

    وَأَصْحَـٰبُ ٱلْأَيْكَةِ وَقَوْمُ تُبَّعٍ ۚ كُلٌّ كَذَّبَ ٱلرُّسُلَ فَحَقَّ وَعِيدِ

    Da ma'abũta ƙunci [1]da mutãnen Tubba'u,[2] kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Ma'abũta ƙunci, mutãnen shu'aibu ne na farko. Bãyan an halaka su, sa'an nan ya tafi Madayana. [2] Tubba'u, sarkin Himyar ne,a Yemen, yã musulunta amma mutãnensa suka ƙi bin sa ga addini, aka halaka su, shi kuma ya tsĩra. Shĩ ne sarki wanda ya sãɓãwa ƙã'ida; ya musulunta amma mabiyansa ba su musulunta ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 14 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  15. 15

    أَفَعَيِينَا بِٱلْخَلْقِ ٱلْأَوَّلِ ۚ بَلْ هُمْ فِى لَبْسٍ مِّنْ خَلْقٍ جَدِيدٍ

    Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 15 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  16. 16

    وَلَقَدْ خَلَقْنَا ٱلْإِنسَـٰنَ وَنَعْلَمُ مَا تُوَسْوِسُ بِهِۦ نَفْسُهُۥ ۖ وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنْ حَبْلِ ٱلْوَرِيدِ

    Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar hannayẽnsa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 16 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  17. 17

    إِذْ يَتَلَقَّى ٱلْمُتَلَقِّيَانِ عَنِ ٱلْيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ قَعِيدٌ

    A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 17 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  18. 18

    مَّا يَلْفِظُ مِن قَوْلٍ إِلَّا لَدَيْهِ رَقِيبٌ عَتِيدٌ

    Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 18 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  19. 19

    وَجَآءَتْ سَكْرَةُ ٱلْمَوْتِ بِٱلْحَقِّ ۖ ذَٰلِكَ مَا كُنتَ مِنْهُ تَحِيدُ

    Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 19 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  20. 20

    وَنُفِخَ فِى ٱلصُّورِ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمُ ٱلْوَعِيدِ

    Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 20 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  21. 21

    وَجَآءَتْ كُلُّ نَفْسٍ مَّعَهَا سَآئِقٌ وَشَهِيدٌ

    Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 21 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  22. 22

    لَّقَدْ كُنتَ فِى غَفْلَةٍ مِّنْ هَـٰذَا فَكَشَفْنَا عَنكَ غِطَآءَكَ فَبَصَرُكَ ٱلْيَوْمَ حَدِيدٌ

    (Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 22 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  23. 23

    وَقَالَ قَرِينُهُۥ هَـٰذَا مَا لَدَىَّ عَتِيدٌ

    Kuma abõkin haɗinsa[1] ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Malã'ika mai rubũtun aikinsa. Bã ya rabuwa da shi sai a hãlãye uku, wurin jimã'i da salga da wanka. Malã'ikan da aka haɗa shi da shi dõmin ya rubũta ayyukansa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 23 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  24. 24

    أَلْقِيَا فِى جَهَنَّمَ كُلَّ كَفَّارٍ عَنِيدٍ

    (A ce wa Malã'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 24 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  25. 25

    مَّنَّاعٍ لِّلْخَيْرِ مُعْتَدٍ مُّرِيبٍ

    "Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 25 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  26. 26

    ٱلَّذِى جَعَلَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ فَأَلْقِيَاهُ فِى ٱلْعَذَابِ ٱلشَّدِيدِ

    "Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 26 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  27. 27

    ۞ قَالَ قَرِينُهُۥ رَبَّنَا مَآ أَطْغَيْتُهُۥ وَلَـٰكِن كَانَ فِى ضَلَـٰلٍۭ بَعِيدٍ

    Abõkin haɗinsa[1] ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Shaiɗanin da ke tãre dashi. A cikin hadĩsi an ruwaito cewa kõwa yana da Shaiɗani tãre da shi, sai dai idan ya rinjãye shi, da abin da Allah Ya aza masa, ko kuma shi sai shaiɗãnin ya rinjãye shi da bin son zũciyarsa.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 27 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  28. 28

    قَالَ لَا تَخْتَصِمُوا۟ لَدَىَّ وَقَدْ قَدَّمْتُ إِلَيْكُم بِٱلْوَعِيدِ

    Ya ce: "Kada ku yi husũma a wur Nalhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 28 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  29. 29

    مَا يُبَدَّلُ ٱلْقَوْلُ لَدَىَّ وَمَآ أَنَا۠ بِظَلَّـٰمٍ لِّلْعَبِيدِ

    "Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyi Na."

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 29 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  30. 30

    يَوْمَ نَقُولُ لِجَهَنَّمَ هَلِ ٱمْتَلَأْتِ وَتَقُولُ هَلْ مِن مَّزِيدٍ

    Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe,[1] akwai wani ƙãri?"

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Wannan jawãbi na Jahannama yanã ɗaukar ma'anõni biyu. Ta farko tanã nũna ta cika ƙwarai, amma tanã kũkan a ƙara mata wani abu a cikinta. Wannan fassara ta yi daidai da ayãr da ta ce, "Lalle na cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya." Sura ta 32, ãyã ta 13. Fassara ta biyu, ita ce Jahannama nã neman ƙãri tanã hushi sabõda mãsu sãɓawa umurnin Allah. Sũra ta 67 ãyõyi 6, 7 da 8.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 30 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  31. 31

    وَأُزْلِفَتِ ٱلْجَنَّةُ لِلْمُتَّقِينَ غَيْرَ بَعِيدٍ

    Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 31 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  32. 32

    هَـٰذَا مَا تُوعَدُونَ لِكُلِّ أَوَّابٍ حَفِيظٍ

    "Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa).

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 32 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  33. 33

    مَّنْ خَشِىَ ٱلرَّحْمَـٰنَ بِٱلْغَيْبِ وَجَآءَ بِقَلْبٍ مُّنِيبٍ

    "Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, [1]kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Tsoron Allah a fake, shĩ ne a bauta masa, bã da riya ba, ɓayyane da ɓõye duka ɗaya.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 33 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  34. 34

    ٱدْخُلُوهَا بِسَلَـٰمٍ ۖ ذَٰلِكَ يَوْمُ ٱلْخُلُودِ

    (A ce musu) "Ku shige ta da aminci, [1]waccan ita ce rãnar dawwama."

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Kõ kuma ku shiga da sallama.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 34 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  35. 35

    لَهُم مَّا يَشَآءُونَ فِيهَا وَلَدَيْنَا مَزِيدٌ

    Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima,

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 35 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  36. 36

    وَكَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّن قَرْنٍ هُمْ أَشَدُّ مِنْهُم بَطْشًا فَنَقَّبُوا۟ فِى ٱلْبِلَـٰدِ هَلْ مِن مَّحِيصٍ

    Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'?[1] (Babu).

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Sun nħmi wurin tsĩra, ba su sãmu ba, sabõda haka kãfiran yanzu ma ba su iya samun wurin tsĩra, sai dai idan sunkõma ga Allah ta hanyar Manzon Sa kawai, watau taƙawa ga Allah ke nan. Anã kãre azãbar Sa da ibãdar Sa kamar yadda Yake so.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 36 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  37. 37

    إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَذِكْرَىٰ لِمَن كَانَ لَهُۥ قَلْبٌ أَوْ أَلْقَى ٱلسَّمْعَ وَهُوَ شَهِيدٌ

    Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 37 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  38. 38

    وَلَقَدْ خَلَقْنَا ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِى سِتَّةِ أَيَّامٍ وَمَا مَسَّنَا مِن لُّغُوبٍ

    Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 38 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  39. 39

    فَٱصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ قَبْلَ طُلُوعِ ٱلشَّمْسِ وَقَبْلَ ٱلْغُرُوبِ

    Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi[1] game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Tasbĩhi game da gõdewa Allah a gabãnin fitar rãnã, shi ne sallar asuba, na gabãnin ɓacewarta, shi ne sallar Azahar da La'asar. Daga dare kuwa, shĩ ne sallar Magariba da Isha'i. Bãyan sujada, shĩ ne sallõli na nafila kuma ma'anarsa a nan tasbĩhi da tahmĩdi da kabbarõri a bãyan sallõli farillai talãtin da uku kõwace, sa'annan a cika ɗari da addu'ar da aka ruwaito a nan.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 39 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  40. 40

    وَمِنَ ٱلَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَأَدْبَـٰرَ ٱلسُّجُودِ

    Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 40 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  41. 41

    وَٱسْتَمِعْ يَوْمَ يُنَادِ ٱلْمُنَادِ مِن مَّكَانٍ قَرِيبٍ

    Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri [1]makusanci.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Mai kira shĩ ne Isrãfĩlu a cikin ƙaho a Baitil Maƙadis dõmin a nan ƙasa ta fi zama kusa da samã.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 41 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  42. 42

    يَوْمَ يَسْمَعُونَ ٱلصَّيْحَةَ بِٱلْحَقِّ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمُ ٱلْخُرُوجِ

    Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 42 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  43. 43

    إِنَّا نَحْنُ نُحْىِۦ وَنُمِيتُ وَإِلَيْنَا ٱلْمَصِيرُ

    Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 43 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  44. 44

    يَوْمَ تَشَقَّقُ ٱلْأَرْضُ عَنْهُمْ سِرَاعًا ۚ ذَٰلِكَ حَشْرٌ عَلَيْنَا يَسِيرٌ

    Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 44 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
  45. 45

    نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَقُولُونَ ۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيْهِم بِجَبَّارٍ ۖ فَذَكِّرْ بِٱلْقُرْءَانِ مَن يَخَافُ وَعِيدِ

    Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani,[1] ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Wannan ya nũna ba a wa'azi da ilmin da bã daga Alƙur'ãni aka fitar da shi ba, sai fa idan bai sãɓawa abin da ke cikin Alƙur'ani ba.

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 45 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri
Rufewar sura: Tafsirin As-Sa'di (Larabci)

آخر تفسير سورة ق. والحمد لله أولاً وآخراً وظاهراً وباطناً.

Tafsirin As-Sa'di, Larabci v1.0.0, QuranEnc.com

Tafsiri

Sura ta gabaAz-Zariyatالذاريات

Rubutun Alƙur'ani: Tanzil

Ba da rahoton kuskure

Ƙari