Hadisai

Mun kasance ba ma daukar kalar hanta-hanta da fatsi-fatsi a bakin komai bayan tsarki

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAbu Dawud ne ya ruwaito shi da wannan lafazin, kuma Bukhari ya ruwaito shi ba tare da ƙarin (bayan tsarki) ba

Rubutun Larabci

عن أُمِّ عَطِيَّةَ رَضي الله عنها، وكَانَتْ بايَعَت النبيَّ صلى الله عليه وسلم، قالت: كُنَّا لا نَعُدّ الكُدرَةَ والصُّفْرَةَ بعدَ الطُّهرِ شيئًا.

Fassara

Daga Ummu Adiyya - Allah Ya yarda da ita -, ta kasance ta yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - caffa, ta ce: Mun kasance ba ma daukar kalar hanta-hanta da fatsi-fatsi a bakin komai bayan tsarki.

Sharhi

Sahabiyya Ummu Adiyya - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa mata a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba sa daukar ruwan da yake fita daga farji - wanda launinsa yake karkata zuwa baƙi, ko fatsi-fatsi - bayan ganin tsarki cewa yana daga al’ada, saboda haka ba sa barin sallah ko azimi saboda shi.

Fa'idoji

  • Ruwan da yake zuba daga farjin mace - bayan tsarkaka daga al’ada - ba'a izina da shi koda a tare da shi akwai launin hanta-hanta da fatsi-fatsi wanda ya samu ta hanyar jini.
  • Zubar hanta-hanta da fatsi-fatsi a lokacin al’ada da al'ada ana daukarsa a matsayin al’ada; Domin cewa shi jini ne a lokacinsa, sai dai mai cakuduwa ne da ruwa.
  • Mace ba ta barin sallah ko azimi saboda hanta-hanta da fatsi-fatsi wanda yake a bayan tsarki, kawai ta yi alwala ta yi sallah.
Sharhi: العربية

أَخْبَرتْ الصحابيّةُ أُمُّ عَطية رضي الله عنها أنَّ النساء في عَهد النبيِّ صلى الله عليه وسلم لا يَعْتَبِرْنَ الماءَ الذي يَخرُج من الفَرْج -والذي يَميل لونُه إلى السواد، أو إلى الاصفرار- بعدَ رؤية الطُّهرِ مِن الحيض: حيضًا، فلا يَتْرُكْنَ الصَّلاة ولا الصوم لأجله.

  • الماء الذي ينزل من فرج المرأة -بعد الطهر من الحيض- لا يُعتبر ولو كان فيه الكدرة والصفرة المكتسبة من الدم.
  • نزول الكدرة والصفرة زمن الحيض والعادة يعتبر حيضًا؛ لأنه دم في وقته، إلا أنه ممتزج بماء.
  • لا تترك المرأة الصلاة ولا الصوم لأجل الكدرة والصفرة التي بعد الطهر، بل تتوضأ وتصلي.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari