Hadisai

‌Allah Ya fi tausayin bayinSa fiye da wannan matar ga ɗanta

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: قَدِمَ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سَبْيٌ، فَإِذَا امْرَأَةٌ مِنَ السَّبْيِ قَدْ تَحْلُبُ ثَدْيَهَا تَسْقِي، إِذَا وَجَدَتْ صَبِيًّا فِي السَّبْيِ أَخَذَتْهُ، فَأَلْصَقَتْهُ بِبَطْنِهَا وَأَرْضَعَتْهُ، فَقَالَ لَنَا النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَتُرَوْنَ هَذِهِ طَارِحَةً وَلَدَهَا فِي النَّارِ؟» قُلْنَا: لاَ، وَهِيَ تَقْدِرُ عَلَى أَلَّا تَطْرَحَهُ، فَقَالَ: «لَلَّهُ أَرْحَمُ بِعِبَادِهِ مِنْ هَذِهِ بِوَلَدِهَا».

Fassara

Daga Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -: Wasu ribatattu sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ga wata mace daga cikin ribatattun nonanta yana zuba tana shayar da ɗanta, sai ga shi ta samu wani yaro a cikin ribatattun sai ta ɗauke shi, sai ta ɗanfara shi a cikinta ta shayar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mana: «‌Shin yanzu kuna zatan cewa wannan matar zata jefa ɗanta a cikin wuta?» muka ce: A'a, alhali ita tana da ikon ƙin jefa shi, sai ya ce:«‌Allah Ya fi tausayin bayinSa fiye da wannan matar ga ɗanta».

Sharhi

An zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wasu ribatattu daga (ƙabilar) Hawazin, sai ga shi a cikinsu akwai wata mace tana neman ɗanta, sai ga shi ta samu wani yaron da ta ɗauke shi sai ta shayar da shi saboda cutuwa da tayi ta hanyar taruwar nono a cikin hantsarta, sai ta samu ɗanta a cikin ribatattu sai ta ɗauke shi, sai ta ɗanfara shi a cikinta ta shayar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa sahabbansa: Shin yanzu kuna zatan cewa wannan matar zata jefa ɗanta a cikin wuta? Muka ce: Ba zata jefa shi da yardarta ba har abada. Sai ya ce: Allah Ya fi jin tausayin bayinSa daga wannan matar da ɗanta.

Fa'idoji

  • Rahamar Allah mai yalwa ce ga bayinSa, kuma Shi Yana nufin alheri da aljanna garesu, da kuma tsira daga wuta.
  • Fa'idantuwa daga abubuwan dake faruwa da kuma alaƙanta su a kan fadakarwa da kuma koyarwa.
  • Yana kamata ga mumini ya zama mai kyakkyawan zato ga Allah, kuma kada ya yanke ƙauna tare da tsoron Allah da kuma tabbata akan AddininSa, domin Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Ma'abocin rahama ne mayalwaciya.
Sharhi: العربية

جيء للنبي صلى الله عليه وسلم بأسرى من هَوَازِن، فإذا منهم امرأة تبحث عن صبيها، فإذا وجدت صبيًّا أخذته فأرضعته لتضررها باجتماع اللبن في ثديها، فوجدت ولدها في الأسرى فأخذته، فألصقته ببطنها وأرضعته، فقال النبي صلى الله عليه وسلم لأصحابه: أتظنون هذه طارحة ولدها في النار؟ قلنا: لا تطرحه طائعة أبدًا. فقال: فالله أرحم بعباده المسلمين من هذه بولدها.

  • رحمة الله الواسعة بعباده، وأنه يريد لهم الخير والجنة، والنجاة من النار.
  • الاستفادة من الحوادث وربطها في التوجيه والتعليم.
  • ينبغي للمؤمن أن يكون حسنَ الظن بالله، ولا ييأس مع تقوى الله والاستقامة على دينه، فإنه سبحانه ذو الرحمة الواسعة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari