Hadisai

Ubangijimmu maɗaukaki Yana sauka a kowanne dare, zuwa sama makusanciya, lokacin da ɗaya bisa uku na dare ya saura

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي هريرة رضي الله عنه: أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «يَنْزِلُ رَبُّنَا تَبَارَكَ وَتَعَالَى كُلَّ لَيْلَةٍ إِلَى السَّمَاءِ الدُّنْيَا حِينَ يَبْقَى ثُلُثُ اللَّيْلِ الْآخِرُ، يَقُولُ: «مَنْ يَدْعُونِي فَأَسْتَجِيبَ لَهُ؟ مَنْ يَسْأَلُنِي فَأُعْطِيَهُ؟ مَنْ يَسْتَغْفِرُنِي فَأَغْفِرَ لَهُ؟».

Fassara

Daga Abu Hurairah Allah Ya yarda da shi, Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ubangijimmu maɗaukaki Yana sauka a kowanne dare, zuwa sama makusanciya, lokacin da ɗaya bisa uku na dare ya saura yana cewa: Wa zai roƙeni in amsa masa,?? wa zai tambaye ni in ba shi, ?? wa zai nemi gafarata in gafarta masa ??

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin Allah maɗaukaki Yana sakkowa a kowanne dare zuwa sama makusanciya lokacin da ɗaya bisa uku na dare ya saura, yana kwaɗaitar da bayinSa a kan su roƙe shi, shi kuma zai amsawa wanda ya roƙe Shi, yana zaburar da su a kan su tambaye Shi abin da suke so, Shi kuma zai ba wanda ya tambaye Shi, yana kiransu da su roƙi gafararSa daga zunubansu Shi kuma yana gafartawa bayinSa muminai.

Fa'idoji

  • Falalar ɗaya bisa ukun ƙarshe na dare da Sallah da Addu’a da neman gafara a lokacin.
  • Ya kamata ga mutum a lokacin da ya ji wannan Hadisi ya kasance yana da tsananin kwaɗayin ribatar lokutan amsar Addu’a.
Sharhi: العربية

بيَّن النبيُّ صلَّى اللهُ عليه وسلَّمَ أنَّ اللهَ تَبارَك وتعالَى يَنزِلُ كلَّ لَيلةٍ إلى السماء الدنيا حِينَ يَبْقى الثُّلثُ الأخيرُ مِن اللَّيل، ويُرَغِّبُ عبادَه أن يَدْعُوْهُ، فهو يَستجيب لمَن دَعاه، ويَحُثُّهم أن يَسألوه ما يُريدون، فهو يُعطي مَن سأله، ويَنْدُبُهم أنْ يَستغفروه مِن ذنوبِهم فهو يَغفِرُ لعبادِه المؤمنين.

  • فضل الثلث الأخير من الليل والصلاة والدعاء والاستغفار فيه.
  • ينبغي للإنسان عند سماع هذا الحديث أن يكون شديد الحرص على اغتنام أوقات الإجابة للدعاء.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari