Hadisai

Ki ɗauki abin da zai ishe ki ke da 'ya'yanki daga cikin dukiyarsa ba tare da barna ba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها قَالَت: دَخَلَتْ هِنْدٌ بِنْتُ عُتْبَةَ امْرَأَةُ أَبِي سُفْيَانَ عَلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَتْ: يَا رَسُولَ اللهِ، إِنَّ أَبَا سُفْيَانَ رَجُلٌ شَحِيحٌ، لَا يُعْطِينِي مِنَ النَّفَقَةِ مَا يَكْفِينِي وَيَكْفِي بَنِيَّ إِلَّا مَا أَخَذْتُ مِنْ مَالِهِ بِغَيْرِ عِلْمِهِ، فَهَلْ عَلَيَّ فِي ذَلِكَ مِنْ جُنَاحٍ؟ فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «خُذِي مِنْ مَالِهِ بِالْمَعْرُوفِ مَا يَكْفِيكِ وَيَكْفِي بَنِيكِ».

Fassara

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Hindu 'yar Utbatah - matar Abu Sufyan- ta shigo wajen Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai ta ce: Ya Manzon Allah, Abu Sufyan ya kasance mutum ne mai ƙwauro, ba ya bamu abin da zai ishe mu ni da 'ya'ya na sai abinda na ɗauka daga cikin dukiyarsa ba tare da saninsa ba, shin ba laifi akaina a yin hakan? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ki ɗauki abin da zai ishe ki ke da 'ya'yanki daga cikin dukiyarsa ba tare da barna ba".

Sharhi

Hindu 'yar Utbah - Allah Ya yarda da ita - ta nemi fatawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mijinta Abu Sufyan - Allah Ya yarda da shi -, kuma shi mutum ne marowaci mai kwaɗayin dukiyarsa, ba ya bata abinda zai isheta ya ishi 'ya'yanta na ciyarwa, sai dai in ta ɗauka a ɓoye cikin dukiyarsa alhali shi bai sani ba, shin akwai wani laifi akanta a hakan? Sai (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ki ɗauki gwargwadan abinda aka sani a al'ada cewa shi zai isa cikin dukiyarsa koda ba tare da saninsa ba.

Fa'idoji

  • Wajabcin ciyar da mata da kuma 'ya'ya.
  • Ibnu Hajar ya ce: Abin nufi a faɗinsa: "Ki ɗauki abinda zai isheki cikin dukiyarsa ta yadda al'ada take gudana da shi", sai ya mayar da ita zuwa ga al'ada a cikin abinda babu iyakancewar shari'a a cikinsa.
  • Ibnu Hajar ya ce: An kafa hujja da wanna hadisin akan halaccin ambatan mutum da abinda ba ya ƙayatar da shi idan ya kasance ta fuskar neman fatawa ne da kai ƙara da makamancin haka, kuma shi ne ɗaya daga cikin guraren da aka halatta giba (yi da mutum) a cikinsu.
  • AlƘurɗubi ya ce: Hindu bata nufin siffanta Abu Sufyan da ƙwauro a dukkanin halayensa, kawai ta siffanta halinta ne tare da shi kuma cewa shi yana yi mata ƙwauro ita da 'ya'yanta, wannan ba ya lazimtar rowa kai tsaye, domin cewa mafi yawancin shugabanni sunayin haka tare da iyalansu suna fifita na waje dan jawo zukatansu.
Sharhi: العربية

استفتتْ هند بنت عتبة رضي الله عنها النبيَّ صلى الله عليه وسلم عن زوجها أبي سفيان رضي الله عنه، وأنه رجل بخيل حريص على ماله، لا يعطيها من النفقة ما يكفيها ويكفي بنيها، إلا أن تأخذ من ماله سرًّا وهو لا يعلم، فهل عليها في ذلك من إثم؟ فقال صلى الله عليه وسلم: خذي لك ولبنيه من ماله القَدْرَ الذي عُرِف بالعادة أنه الكفاية ولو بغير علمه.

  • وجوب النفقةِ على الزَّوجة والأولاد.
  • قال ابن حجر: والمراد من قوله: "خذي من ماله ما يكفيك بالمعروف"، فأحالها على العرف فيما ليس فيه تحديد شرعي.
  • قال ابن حجر: واستدل بهذا الحديث على جواز ذكر الإنسان بما لا يعجبه إذا كان على وجه الاستفتاء والاشتكاء ونحو ذلك، وهو أحد المواضع التي تباح فيها الغيبة.
  • قال القرطبي: لم تُرد هند وصف أبي سفيان بالشُّحّ في جميع أحواله، وإنما وصفت حالها معه وأنه كان يُقَتِّر عليها وعلى أولادها، وهذا لا يستلزم البخل مطلقًا، فإن كثيرًا من الرؤساء يفعل ذلك مع أهله ويؤثِر الأجانب استئلافًا لهم.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari