Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ ابنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهما عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنِ اقْتَنَى كَلْبًا إِلَّا كَلْبَ ضَارٍ أَوْ مَاشِيَةٍ نَقَصَ مِنْ عَمَلِهِ كُلَّ يَوْمٍ قِيرَاطَانِ»، قَالَ سَالِمٌ: وَكَانَ أَبُو هُرَيْرَةَ يَقُولُ: «أَوْ كَلْبَ حَرْثٍ»، وَكَانَ صَاحِبَ حَرْثٍ.
Fassara
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya riƙi wani kare saidai karen farauta ko kiwo ƙiradi biyu zai ragu daga aikinsa kowace rana", Salim ya ce: Abu Huraira ya kasance yana cewa: "Ko karen noma", kuma ya kasance manomi ne.
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga riƙon karnuka, saidai dan buƙatar farauta, ko gadin dabbobi da shuka, wanda ya riƙe kare ga wanin haka kowace rana ƙiraɗi biyu zai ragu daga ladan aikinsa; kuma shi wani gwargwado ne sananne a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
Fa'idoji
- Ba ya halatta ga musulmi ya riƙi kare, sai dai abinda aka togance.
- Hana riƙon karnuka; dan abinda ke cikinsu na ɓarnace-ɓarnace da cutukka masu yawa, haƙiƙa ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa mala'iku ba sa shiga gidan da a cikinsa akwai kare; dan kuma abinda ke cikinsa na najasa mai kauri wacce babu abinda ke gusar da ita sai maimaita wankewar da ruwa da kuma turɓaya.
Sharhi: العربية
حذّر النبيُّ صلى الله عليه وسلم من اقتناء الكلاب، إلا لحاجة الصيد، أو حراسة الماشية والزروع، ومن اقتناه لغير ذلك نقص من ثواب عمله كل يوم قيراطان؛ وهو مقدار معلوم عند الله تعالى.
- لا يجوز للمسلم أن يقتني الكلب، إلا فيما استثني.
- منع اقتناء الكلاب؛ لما فيه من المفاسد والمضار الكثيرة، فقد ثبت عن النبي صلى الله عليه وسلم أن الملائكة لا تدخل بيتًا فيه كلب؛ ولما فيه من النجاسة الغليظة التي لا يزيلها إلا تكرار الغسل بالماء والتراب.