Hadisai

Wanda ya ɗaga makami a kammu, to, ba ya tare da mu

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ حَمَلَ عَلَيْنَا السِّلَاحَ فَلَيْسَ مِنَّا».

Fassara

Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya ɗaga makami a kammu, to, ba ya tare da mu"

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana gargaɗarwa daga ɗaukar makami a kan musulmai, don tsorata su ko yi musu ƙwace, wanda ya aikata hakan ba tare da wani haƙƙi ba, to, haƙiƙa ya aikata babban laifi daga manyan laifuka, kuma ya cancanci wannan narkon mai tsanani.

Fa'idoji

  • Gargaɗi mai tsanani game da yaƙar musulmi ga 'yan uwansa musulmai.
  • Daga mafi girman laifuka da ɓarna mai girma a ban ƙasa ɗaga makami a kan musulmai, da kuma ɓarna ta hanyar kisa.
  • Narkon da aka ambata ba ya shafar yaƙin (da aka yi) da haƙƙi, kamar yaƙar 'yan tawaye da maɓarnata da wasunsu.
  • Haramcin tsoratar da musulmai da makami ko waninsa - ko da ta fuskar wasa ne ne -.
Sharhi: العربية

نهى النبي صلى الله عليه وسلم وحذر من حمل السلاح على المسلمين بغير حق لإخافتهم أو نهبهم، وأن من فعل ذلك فليس منا.

  • هذا الوعيد في الحديث يدل على أن هذا العمل من كبائر الذنوب.
  • التحذير الشديد من قتال المسلم لإخوانه المسلمين.
  • من أعظم المنكرات والفساد العظيم في الأرض إِشْهَارُ السلاحِ على المسلمين، والإفسادِ بالقتل.
  • الوعيد المذكور لا يتناول القتال بحقٍّ، كقتال البُغَاة والمفسدين وغيرِهم.
  • تحريم إِخَافَةِ المسلمين بالسلاح أو غيره -ولو على وجه المزاح-.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari