Hadisai

Wannan dinnan jijiya ce, saidai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina haila a cikinsu, sannan ki yi wanka ki yi Sallah

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤمنين رضي الله عنها أَنَّ فَاطِمَةَ بِنْتَ أَبِي حُبَيْشٍ سَأَلَتِ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَتْ: إِنِّي أُسْتَحَاضُ فَلاَ أَطْهُرُ، أَفَأَدَعُ الصَّلاَةَ؟ فَقَالَ: «لَا، إِنَّ ذَلِكِ عِرْقٌ، وَلَكِنْ دَعِي الصَّلاَةَ قَدْرَ الأَيَّامِ الَّتِي كُنْتِ تَحِيضِينَ فِيهَا، ثُمَّ اغْتَسِلِي وَصَلِّي».

Fassara

Daga A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa Fatima 'yar Abu Hubaishi ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce : Ni ina yin jinin cuta bana tsarkaka, shin zan bar sallah ne? sai ya ce: "A'a, Wannan dinnan jijiya ce, saidai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina haila a cikinsu, sannan ki yi wanka ki yi Sallah.

Sharhi

Fadima 'yar Hubaishin ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Lallai ni jini ba ya yanke mini, yana zarcewa har a lokacin da ba na al’ada ba, shin hukuncin hakan zai zama hukuncin al’ada sai inbar sallah? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mata: Lallai shi jinin cuta ne, shi jinin rashin lafiya ne yana faruwa daga yankewar jijiya a mahaifa, ba jinin haila ba ne, Idan lokacin haila ya zo wanda kika kasance kina haila a cikinsa akan al'adarki ta wata kafin ki yi rashin lafiya da jinin cuta, to ki bar sallah da azimi da wasunsu , na abinda haila take hanawa a lokacin al’ada . Idan gwargwadan lokacin ya kare sai ki zama kin yi tsrki, to sai ki wanke gurin jinin, sannan ki wanke jikinki cikakken wankewa dan dauke hadasi, sannan ki yi sallah.

Fa'idoji

  • Wajabcin wanka akan mace a yayin karewar kwanukan al’adarta.
  • Wajabcin sallah akan mai jinin cuta.
  • Haila: Jini ne na dabi'a da mahaifa take turo shi ta gaban mace baliga, da yake samunta a wasu kwanuka sanannu.
  • Jinin cuta: Zubar jini ba'a lokacinsa ba daga kasan mahaifa ba daga can cikin mahaifa ba.
  • Banbanci tsakanin jinin haila da jinin cuta: Cewa jinin haila baki ne mai kauri mai wari, amma jinin cuta to shi jane siriri ba shi da wari.
Sharhi: العربية

سَألتْ فاطمةُ بنت حبيش النبيَّ صلى الله عليه وسلم فقالت: إني لا ينقطع عني الدم ويستمر حتى في غير زمن الحيض، فهل يكون حكم ذلك حكم الحيض فأترك الصلاة؟ فقال لها النبي صلى الله عليه وسلم: إنه دم استحاضة، وهو دم مَرَضِيٌّ ينشأ عن انقطاع عرق في الرحم، وليس بدم حيض، فإذا جاء وقت الحيض الذي كنت تحيضين فيه على عادتك الشهرية قبل أن تمرضين بالاستحاضة، فاتركي الصلاة والصوم وغيرَهما مما تُمنَع منه الحائض وقت الحيض. فإذا انتهى مقدار تلك المدة، فتكوني قد طهرتي من الحيض، فاغسلي موضع الدم، ثم اغسلي بدنك اغتسالًا كاملًا لرفع الحدث، ثم صلي.

  • وجوب الغسل على المرأة عند انتهاء أيام حيضها.
  • وجوب الصلاة على المستحاضة.
  • الحيض: دمُ طبيعةٍ يُرْخِيْه الرَّحِمُ عَبْرَ فَرْجِ المرأةِ البالغة، يصيبها في أيام معلومة.
  • الاستحاضة: سَيَلانُ الدمِ في غير وقته من أدنى الرحم دون قَعْرِه.
  • الفرق بين دم الحيض ودم الاستحاضة: أنَّ دمَ الحيضِ أسود ثخين مُنْتِن الرائحة، أما دم الاستحاضة فأحمر رقيق ليس له رائحة منتنة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari