Hadisai

Mutum yana kan Addinin abokinsa, saboda haka dayanku ya duba wanda zai yi abokantaka (da shi)

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Hasan neAbu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad

Rubutun Larabci

عن أبي هريرة رضي الله عنه أَن النبيَّ صَلّى اللهُ عَلَيْهِ وسَلَّم قَالَ: «الرَّجُلُ عَلَى دِينِ خَلِيلِهِ، فَلْيَنْظُر أَحَدُكُم مَنْ يُخَالِل».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutum yana kan Addinin abokinsa, saboda haka dayanku ya duba wanda zai yi abokantaka (da shi)".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum yana kamanceceniya da abokinsa amintacce a rayuwarsa da kuma al'adarsa, kuma abokantaka tana tasiri a ɗabi'u da yanayi da tasarrufi, saboda haka ne ya nunar zuwa kyakkyawan zabin aboki; domin aboki yana shiryar da abokinsa akan imani da shiriya da alheri, kuma yana kasancewa taimako ga abokinsa.

Fa'idoji

  • Umarni da abokantaka da zababbu da kuma tsabosu, da hani daga abokantaka da mutanen banza.
  • An kebanci aboki banda ɗan'uwa; domin aboki kai ne wanda ka zabe shi, amma ɗan'uwa da makusanci to kai baka da zabi a cikinsa.
  • Zabin aboki babu makawa dole sai an yi tunani.
  • Mutum yana karfafar addininsa ta hanyar abokantakar muminai, kuma yana raunana shi ta hanyar abokantaka da fasikai.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ الإنسانَ يُشابه صديقَه وصاحبَه الخالصَ في سيرته وعادته، وتؤثر الصداقة في الأخلاق والسلوك والتصرفات، ولهذا أرشد إلى حسن اختيار الصديق؛ لأنه يَدلُّ صديقَه على الإيمان والهدى والخير، ويكون عونًا لصاحبه.

  • الأمر بصحبة الأخيار وانتقائهم والنهي عن صحبة الأشرار.
  • خص الصديق دون القريب؛ لأن الصاحب أنت مَن يختاره، أما الأخ والقريب فليس لك فيه اختيار.
  • اتِّخاذ الصحبة لا بد أن يصدر عن تفكُّر.
  • المرء يُقوِّي دينه بِصُحبة المؤمنين ويُضعفه بِصُحبَة الفاسقين.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari