Hadisai

Dabi'a (ta addinin Musulunci ) guda biyar ce: Kaciya da aske gashin mara, da rage gashin baki, da yanke farata, da tsige gashin hammata

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبِي هريرة رضي اللَّه عنه: سمعتُ النبِيّ صلى الله عليه وسلم يقول: «الفِطْرَةُ خمسٌ: الخِتَانُ والاستحدادُ وقصُّ الشَّارِبِ وتقليمُ الأظفارِ وَنَتْفُ الآبَاطِ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Dabi'a (ta addinin Musulunci ) guda biyar ce: Kaciya da aske gashin mara, da rage gashin baki, da yanke farata, da tsige gashin hammata".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana ɗabi'u biyar daga addinin Musulunci da kuma sunnonin manzanni: Na farkonsu: Kaciya, ita ce yanke fatar da ta ƙaru a kan azzakari wajen kan kaciya, da kuma yanke kan fata a farjin mace a saman bigiren mashigar azzakari. Na biyunsu: Aske gashin mara, shi ne aske gashin mara wanda ke gefen gaba. Na ukunsu: Rage gashin baki, shi ne rage abin da ya tsiro a kan leɓen sama na namiji inda leɓe yake bayyana. Na huɗunsu: Yanke farata. Na biyar ɗinsu: Aske gashin hammata.

Fa'idoji

  • Sunnonin manzanni waɗanda Allah Yake sonsu kuma Ya yarda da su, Yake umarni da su, suna kira zuwa ga cika da tsafta da kyau.
  • Halaccin lazimtar waɗannan abubuwan, da kuma rashin rafkana daga garesu.
  • Akwai fa'idoji na addini da rayuwa cikin waɗannan ɗabi'un: Daga cikinsu akwai: Kyautata yanayin mutum, da tsaftace jiki, da tabbatar da tsarki, da saɓawa kafirai, da riko (aiwatar da) umarnin Allah.
  • Awasu hadisan daban an ambaci ƙarin wasu ɗabi'un banda waɗannan biyar ɗin, kamar: Cika gemu, da asuwaki, da wasunsu.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم خمسَ خصالٍ من دينِ الإسلام وسنن المرسلين: أولها: الختان، وهو قطع جِلْدَةٍ زائدةٍ على الذَّكَرِ فوق الحَشَفَة، وقطعُ رأسِ جِلدةٍ في فرج الأنثى فوق مَحَلِّ الإيلاج. وثانيها: الاستحداد، وهو حَلْقُ شَعَرِ العَانَة الذي حول القُبُل. وثالثها: قص الشارب، وهو قصُّ ما نبت على شفة الرجل العليا بحيث تظهر الشفة. ورابعها: قص الأظفار. وخامسها: نتف الإبط.

  • سُنَنُ المرسلين التي يُحِبُّها الله ويرتضيها ويأمر بها تدعو إلى الكمال والنزاهة والجمال.
  • مشروعية تَعَاهُدِ هذه الأشياء، وعدم الغفلة عنها.
  • لهذه الخصال فوائد دينية ودنيوية، منها: تحسين الهيئة، وتنظيف البدن، والاحتياط للطهارة، ومخالفة الكفار، وامتثال أمر الله.
  • ذُكِرَ في أحاديث أخرى زيادةُ خصالٍ للفطرةِ غيرِ هذه الخمس، مثل: إعفاء اللحية، والسواك، وغيرها.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari