Hadisai

Kada ku maida gidajanku kaburbura, kuma kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gareni; domin cewa salatinku a gareni yana isomin a duk inda kuke

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Hasan neAbu Dawud ne Ya Rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «لَا تَجْعَلُوا بُيُوتَكُمْ قُبُورًا، وَلَا تَجْعَلُوا قَبْرِي عِيدًا، وَصَلُّوا عَلَيَّ؛ فَإِنَّ صَلَاتَكُمْ تَبْلُغُنِي حَيْثُ كُنْتُمْ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku maida gidajanku kaburbura, kuma kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gareni; domin cewa salatinku a gareni yana isomin a duk inda kuke".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin hani daga wofintar da gidaje daga sallah sai su zama kamar makabartu, da ba'a sallah a cikin su. Kuma ya yi hani daga maimaita ziyarar wani kabari da taruwa a wurinsa ta fuskar al'ada; domin hakan hanya ce zuwa ga shirka, Ya yi umarni da yin salati da sallama a gare shi a kowane wuri anan doron kasa; domin cewa hakan yana isa gare shi daga na kusa da na nesa duk daya ne, babu bukatuwa zuwa kaikawo a kabarinsa.

Fa'idoji

  • Hani daga wofintar da gidaje daga bautar Allah - Madaukakin sarki -a cikinsu.
  • Hani daga tafiya dan ziyarar kabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; domin cewa shi ya yi umarni da yin salati a gare shi kuma ya sanar da cewa shi yana isowa zuwa gare shi, kadai ana daure sirdi ne dan nufin masallaci da kuma sallah a cikinsa.
  • Haramcin sanya ziyarar kabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idi, ta hanyar maimaita ziyararsa ta kebantacciyar fuska a wani zamani kebantacce, hakanan ziyar kowanne kabari.
  • Girman Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa, ta hanyar shara'anta yin salati da sallama a gare shi a kowanne zamani da kuma kowanne wuri.
  • Yayin da cewa hanin game da sallah a wurin kaburbura hakika ya tabbata a wurin sahabbai; saboda haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana maida gidaje tamkar makabartun da ba'a sallah a cikin su.
Sharhi: العربية

يَنهى النبيُّ صلى الله عليه وسلم عن تعطيل البيوت من الصلاة فتكون كالمقابر التي لا يصلى فيها. ونهى عن تَكرار زيارة قبره والاجتماع عنده على وجهٍ معتاد؛ لأن ذلك وسيلةٌ إلى الشرك. وأمر بالصلاة والسلام عليه في أي مكان من الأرض؛ لأن ذلك يبلغه من القريب والبعيد على حدٍّ سواء، فلا حاجة إلى التردد إلى قبره.

  • النهي عن تعطيل البيوت من عبادة الله تعالى.
  • المنع من السفر لزيارة قبر النبي عليه الصلاة والسلام؛ لأنه أمر بالصلاة عليه وأخبر أنها تبلغه، وإنما تُشَدُّ الرحال لقصد المسجد والصلاة فيه.
  • تحريم جعل زيارة قبر النبي صلى الله عليه وسلم عيدًا، بتكرير زيارته على وجه مخصوص في زمن مخصوص، وكذلك زيارة كل قبر.
  • كرامة النبي صلى الله عليه وسلم على ربه، بمشروعية الصلاة والسلام عليه في كل زمان ومكان.
  • حيث أن النهي عن الصلاة عند القبور قد تقرر عند الصحابة؛ لذا نهى النبي صلى الله عليه وسلم أن تجعل البيوت مثل المقابر لا يُصلى فيها.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari