Hadisai

Na tambayi Nana A'isha, sai na ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah?

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ مُعَاذَةَ قَالَتْ: سَأَلْتُ عَائِشَةَ، فَقُلْتُ: مَا بَالُ الْحَائِضِ تَقْضِي الصَّوْمَ، وَلَا تَقْضِي الصَّلَاةَ؟ فَقَالَتْ: أَحَرُورِيَّةٌ أَنْتِ؟ قُلْتُ: لَسْتُ بِحَرُورِيَّةٍ، وَلَكِنِّي أَسْأَلُ. قَالَتْ: كَانَ يُصِيبُنَا ذَلِكَ، فَنُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّوْمِ، وَلَا نُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّلَاةِ.

Fassara

Daga Mu'azah ta ce : Na tambayi Nana A'isha, sai na ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah? Sai ta ce: Shin ke baharuriyyace? na ce: Ni ba baharuriyya ba ce, sai dai tambaya nake. Ta ce: Hakan yana samunmu, sai a umarcemu da rama azimi, ba'a umartarmu da rama sallah.

Sharhi

Mu'azah al'adawiyya - ta tambayi uwar muminai Nana A'isha - Allah Yarda da ita -, sai ta ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah? Sai ta ce mata: Shin ke daga Khawarijawa Hirarura’a kike ne ? waɗanda suke yawaita tambaya dan ta'annuti da kuma tsanantawa? Na ce: Ni ba baharuriyyababa ce, sai dai tambaya nake yi, ta ce: al’ada tana samunmu tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai a umarcemu da rama azimi, ba'a umartarmu da rama sallah.

Fa'idoji

  • Yin inkari akan dukkan wanda ya yi tambaya irin ta ta'annitanci da kuma jayayya.
  • Haruriyya an dangantasu ga wani gari kusa da Kufa, sunansa "Hiraura’a'; wasu jama'a ne daga Khwarijawa, ta kamantata da su ne saboda tsanantawarsu a cikin al'amarinsu da kuma yawan tayambayarsu da ta'annitancinsu da ita.
  • Malami ya bayyanawa wanda ya neme shi dan neman sani da kuma neman shiriya.
  • Bada amsa da nassi ya fi; domin cewa Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - bata bijiro da ma'anar da mai tambayar ta tambayeta ba; hakan domin cewa amsa da nassi ya fi yanke musu.
  • Sallamawa hukuncin Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - koda bawa bai san hikimar ba.
  • Nawawi ya ce: Ma'anar faɗin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - cewa wasu jama'a daga Khwarij suna wajabtawa mai al’ada rama sallar da ta wuce a lokacin al’ada, wannan kuwa saɓanin Ijma'in musulmai ne, wannan tambayar da Nana A'isha ta tambayeta tambaya ce ta inkari wato: Wannan hanyar Haruriyya ce tir da wannan hanyar.
Sharhi: العربية

سألت معاذة العدوية أم المؤمنين عائشة رضي الله عنها، فقالت: ما بال الحائض تقضي الصوم، ولا تقضي الصلاة؟ فقالت لها: أأنت من الخوارج الحرورية الذين يكثرون الأسئلة للتَّعَنُّت والتشدد؟ قلت: لست بحرورية، ولكني أسأل، قالت: كان يصيبنا الحيض مع النبي صلى الله عليه وسلم، فنؤمر بقضاء الصوم، ولا نؤمر بقضاء الصلاة.

  • الإنكار على كل من سأل سؤال تعنُّت ومجادلة.
  • الحرورية نسبة إلى بلدة قرب الكوفة، اسمها "حروراء": طائفة من الخوارج، شبهتها بهم لتشددهم في أمرهم وكثرة مسائلهم وتعنتهم بها.
  • تبيين المعلم لمن طلبه للتعلم والاسترشاد.
  • الإجابة بالنص أولى؛ لأن عائشة رضي الله عنها لم تتعرض للمعنى الذي سألت عنه السائلة؛ وذلك لأن الإجابة بالنص أقطع للمعارضة.
  • التسليم لحكم الله ورسوله صلى الله عليه وسلم وإن لم يعرف العبد الحكمة.
  • قال النووي: معنى قول عائشة رضي الله عنها أن طائفة من الخوارج يوجبون على الحائض قضاء الصلاة الفائتة في زمن الحيض وهو خلاف إجماع المسلمين، وهذا الاستفهام الذي استفهمته عائشة هو استفهام إنكار أي: هذه طريقة الحرورية وبئست الطريقة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari