Hadisai

Cewa ita ta zo da wani ɗanta ƙarami bai fara cin abinci ba zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zaunar da shi a ƙirjinsa, sai ya yi fitsari akan tufafinsa, sai ya sa a kawo masa ruwa, sai ya yayyafa ruwan bai wanke shi ba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أُمِّ قَيْسٍ بِنْتِ مِحْصَنٍ رَضيَ اللهُ عنها: أَنَّهَا أَتَتْ بِابْنٍ لَهَا صَغِيرٍ لَمْ يَأْكُلِ الطَّعَامَ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَجْلَسَهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي حَجْرِهِ، فَبَالَ عَلَى ثَوْبِهِ، فَدَعَا بِمَاءٍ، فَنَضَحَهُ وَلَمْ يَغْسِلْهُ.

Fassara

Daga Ummu Kais Bint Mihsan -Allah Ya yarda da ita -: Cewa ita ta zo da wani ɗanta ƙarami bai fara cin abinci ba zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zaunar da shi a ƙirjinsa, sai ya yi fitsari akan tufafinsa, sai ya sa a kawo masa ruwa, sai ya yayyafa ruwan bai wanke shi ba.

Sharhi

Ummu Kais bintu Mihsan - Allah Ya yarda da shi - ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani ɗanta wanda bai fara cin abinci ba saboda ƙanƙantar shekarunsa, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya zaunar da shi a ƙirjinsa, sai yaron ya yi fitsari akan tufafinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya sa a kawo masa ruwa, sai ya yayyafa ruwan akan tufafinsa bai wanke tufafin ba.

Fa'idoji

  • Kyawawan Ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabata agare shi - mai girma, da kuma tawali'unsa mai yawa.
  • An so kyautata kyakkyawar mu'amala da tawali'u da tausasawa ga ƙananan yara, da gyara zukatan manya ta hanyar girmama ƙananan yaransu da kuma zaunar da su a ƙirji, da makamancin haka.
  • Najasar fitsarin yaro ko da bai fara cin abinci daomin sha'awa ba.
  • Aikin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ana kiransa yayyafi, kuma ya keɓanci ƙaramin yaro ne wanda bai fara cin abinci ba, amma mace to babu makawa sai an wanke fitsarinta koda ta kasance ƙarama ce.
  • Bahayar yaro wanda yake cin abinci ta hanyar tsotson nonon mahaifiyarsa to babu makawa a cikin hakan sai an wanke kamar sauran najasa.
  • Babu makawa a wankewar daga wani al'amari na ƙari akan sanya ruwan.
  • Abin da ya fi yin gaggawa da tsaftace bigiren najasar; dan gaggawa a tsarkaka daga kabasin, kuma dan kada a manta.
Sharhi: العربية

أتتْ أمُّ قيس بنت محصن رضي الله عنها إلى النبي صلى الله عليه وسلم بابن لها لم يبدأ بأكل الطعام من صغر سنه، فأجلسه صلى الله عليه وسلم في حجره، فبال الصبي على ثوبه صلى الله عليه وسلم، فطلب ماء، ورشه على ثوبه ولم يغسله.

  • أخلاق النبي صلى الله عليه وسلم الكريمة، وتواضعه الجم.
  • الندب إلى حسن المعاشرة والتواضع والرفق بالصغار، وجبر قلوب الكبار بإكرام أطفالهم وإجلاسهم في الحجر، ونحو ذلك.
  • نجاسة بول الغلام وإن لم يأكل الطعام لشهوة.
  • فعل النبي صلى الله عليه وسلم يسمى نَضْحًا، وهو خاص بالطفل الصغير الذكر الذي لم يبدأ بأكل الطعام، أما الأنثى فلا بد من غسل بولها حتى ولو كانت صغيرة.
  • عَذِرَةُ الغلام الذي يتقوَّت من لبن أمه لا بُدَّ فيها من الغسل كسائر النجاسات.
  • الغسل لا بد فيه من أمر زائد على إيصال الماء.
  • الأولى المبادرة بتطهير محل النجاسة؛ للمسارعة في التطهر من الخبث؛ ولئلَّا ينسى.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari