Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَن أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيَّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا وُضِعَتِ الجِنَازَةُ وَاحْتَمَلَهَا الرِّجَالُ عَلَى أَعْنَاقِهِمْ فَإِنْ كَانَتْ صَالِحَةً قَالَتْ: قَدِّمُونِي، وَإِنْ كَانَتْ غَيْرَ صَالِحَةٍ قَالَتْ: يَا وَيْلَهَا أَيْنَ يَذْهَبُونَ بِهَا؟ يَسْمَعُ صَوْتَهَا كُلُّ شَيْءٍ إِلَّا الإِنْسَانَ، وَلَوْ سَمِعَهُ صَعِقَ».
Fassara
Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Idan aka ajiye jana'iza (gawa) maza suka ɗauketa akan kafadinsu idan ta kasance ta gari ce zata ce: Ku kaini, idan ba ta gari ba ce kuwa zata ce: Ya kaicanta ina zasu tafi da ita? kowane abu yana jin sautinta sai mutum kawai, da ace ya ji shi (sautin) da ya suma».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa idan aka ajiye jana'aiza (gawa) akan gado (makara), maza suka ɗauketa akan wuyansu, idan ta kasance ta gari ce zata ce: Ku gabato da ni dan abinda ta gan shi a gabanta na ni'ima, idan ba tagari ba ce zata yi ƙara da sauti abin ƙi: Ya halakarta ina zasu tafi da ita?! dan abinta ta gan shi a gabanta na azaba, kowane abu yana jin sautinta sai mutum kawai, da a ce ya ji shi da ya suma saboda tsananin abinda ya jishi.
Fa'idoji
- Mamaci na gari yana ganin abubuwan bushara kafin rufe shi, kafiri kuwa yana kasa haƙuri, kuma yana ganin akasin hakan.
- Wasu sautukan wanda ba mutum ba zai ji su, amma mutum ba zai iya jinsu ba.
- Sunna ita ce ɗaukar jana'iza (gawa) akan kafadun maza banda mata; saboda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana mata binta (jana'iza).
Sharhi: العربية
أخبر النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنه إذا وضعت الجنازة على السرير، واحتملها الرجال على أعناقهم، فإن كانت صالحة قالت: قدموني لما تراه أمامها من النعيم، وإن كانت غير صالحة صاحت بصوت منكر: يا هلاكها أين يذهبون بها؟! لما تراه أمامها من العذاب، يسمع صوتها كل شيء إلا الإنسان، ولو سمعه لغشي عليه من شدة ما يسمعه.
- الميت الصالح يرى المُبَشِّرات قبل دفنه، ويجزع الكافر، ويرى عكس ذلك.
- بعض الأصوات يسمعها غير الإنسان، ولا يستطيع الإنسان سماعها.
- السنة حمل الجنازة على أعناق الرجال دون النساء؛ لنهي النبي صلى الله عليه وسلم النساء عن اتباعها.