Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَسْعُودٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ لِي النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «اقْرَأْ عَلَيَّ»، قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَأَقْرَأُ عَلَيْكَ، وَعَلَيْكَ أُنْزِلَ؟ قَالَ: «نَعَمْ» فَقَرَأْتُ سُورَةَ النِّسَاءِ حَتَّى أَتَيْتُ إِلَى هَذِهِ الآيَةِ: {فَكَيْفَ إِذَا جِئْنَا مِنْ كُلِّ أُمَّةٍ بِشَهِيدٍ، وَجِئْنَا بِكَ عَلَى هَؤُلاَءِ شَهِيدًا} [النساء: 41]، قَالَ: «حَسْبُكَ الآنَ» فَالْتَفَتُّ إِلَيْهِ، فَإِذَا عَيْنَاهُ تَذْرِفَانِ.
Fassara
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mini: «Ka yi mini karatu» Na ce: Ya Manzon Allah, shin na yi maka karatu, alhali kai aka saukarwa? Ya ce: «Eh» sai na karanta Surat al-Nisa'i har sai da na zo wannan ayar: {To yaya al'amarin zai kasance idan muka zo da kowace al'umma tare da mai yi mata shaida, kai kuma Muka zo da kai a matsayin mai shaida kan waɗannan al'ummar?”. {al-Nisa'i 41]. ya ce: «Ya isa haka» sai na juya gurinsa, sai ga idanuwansa suna zubar da hawaye.
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya karanta masa wani abu na Alƙur'ani, sai ya ce; Ya Manzon Allah, ta yaya zan karanta maka alhali kai aka saukarwa?! sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni ina son in ji shi daga wanina, sai ya karanta masa Suratu al-Nisa'i yayin da ya kai ga faɗinSa Allah - Maɗaukakin sarki -:{To yaya al'amarin zai kasance idan Muka zo da kowace al'umma tare da mai yi mata shaida, kai kuma Muka zo da kai a matsayin mai shaida akan waɗannan al'ummar?} Wato yaya halinka da halin al'ummarka zasu kasance idan Muka zo da kai kana mai shaida ga al'ummarka cewa kai ka isar musu da saƙo, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka tsaya da karatun a yanzu, Ibnu Mas'uda - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Sai na juya wajensa sai ga idanuwansa suna zubar da hawaye dan tsoron mauƙifin (alƙiyama), da kuma tausayin al'ummarsa.
Fa'idoji
- Nawawi ya ce: An so sauraren Alƙur'ani da karkata zuwa gare shi da kuka a wurin karatun, da kuma la’akari da ma'anoninsa, kuma an so neman karantawa daga waninsa dan ya saurare shi, kuma hakan ya fi kai matuƙa a fahimta da kuma la’akari da ma'anoni akan ya karanta da kansa.
- Akwai lada a cikin sauraren karatun Alƙur'ani kamar yadda yake akwai a cikin karanta shi.
- Falalar Abdullahi bin Mas'ud - Allah Ya yarda da shi -, inda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya so ya ji karatun daga bakinsa, wannan yana nuni akan kwaɗayin Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda ad shi - akan neman Alƙur'ani da haddace shi da kuma kyautata shi.
- Falalar yin kuka dan tsoron Allah - Mai girma da ɗaukaka - a lokacin jin ayoyinSa, tare da lazimtar nutsuwa, da kyakkyawan yin shuru, da kuma rashin kururuwa.
Sharhi: العربية
طلب النبي صلى الله عليه وسلم من عبدالله بن مسعود رضي الله عنه أن يقرأ عليه شيئًا من القرآن، فقال: يا رسول الله، كيف أقرؤه عليك وعليك أنزل؟! فقال صلى الله عليه وسلم: إني أحب أن أسمعه من غيري، فقرأ عليه من سورة النساء، فلما بلغ قوله تعالى: {فَكَيْفَ إِذَا جِئْنَا مِنْ كُلِّ أُمَّةٍ بِشَهِيدٍ، وَجِئْنَا بِكَ عَلَى هَؤُلاَءِ شَهِيدًا}. أي ماذا يكون حالك وحال أمتك إذا أتينا بك شهيدًا على أمتك أنك بلغتهم رسالة ربك، فقال النبي صلى الله عليه وسلم: توقف الآن عن القراءة، قال ابن مسعود رضي الله عنه: فالتفتُّ إليه فإذا عيناه تجري دموعهما رهبة من الموقف، ورحمة بأمته.
- قال النووي: استحباب استماع القراءة والإصغاء لها والبكاء عندها وتدبرها، واستحباب طلب القراءة من غيره ليستمع له، وهو أبلغ في التفهم والتدبر من قراءته بنفسه.
- سماع القرآن فيه ثواب كما في تلاوته.
- فضيلة عبد الله بن مسعود رضي الله عنه، حيث أحب الرسول صلى الله عليه وسلم أن يسمعه من فِيه، وهذا يدل على حرص ابن مسعود رضي الله عنه على تطلُّب القرآن وحفظه وإتقانه.
- فضيلة البكاء خشية من الله عز وجل عند سماع آياته، مع التزام السكون، وحسن الصمت، وعدم الصراخ.