Hadisai

Asiwaki mai tsarkake baki ne, mai sa yardar Ubangiji ne

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neNasa'i ne ya ruwaito shi da Ahmad

Rubutun Larabci

عن عائشة رضي الله عنها قالت: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «السِّوَاكُ مَطْهَرَةٌ لِلْفَمِ، مَرْضَاةٌ لِلرَّبِّ».

Fassara

Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yace: "Asiwaki mai tsarkake baki ne, mai sa yardar Ubangiji ne".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sanar damu cewa tsaftace hakora da itaciyar urak da makamancinta yana tsaftace baki daga datti da wari wadanda suke abin ki. Kuma cewa shi yana daga sabubban yardar Allah ga bawa; domin cewa a cikinsa akwai biyayya ga Allah da amsa umarninSa, da kuma abinda ke cikinsa na tsaftar da Allah - Madaukakin sarki - yake son ta.

Fa'idoji

  • Falalar asiwaki, da kwadaitarwar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi ga al'ummarsa da yawaitawa hakan.
  • Abinda yafi ga asiwaki shi ne yin amfani da itacan urak (kirya), yin amfani da makilin da burush yana tsayawa a madadinta.
Sharhi: العربية

يُخبرنا النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ تنظيفَ الأسنانِ بِعُوْدِ شجرةِ الأَرَاك ونحوِه يُطَهِّر الفَمَ من الأوساخ والروائح الكريهة، وأنه مِن أسباب رضا الله عن العبد؛ لأن فيه طاعة لله واستجابة لأمره، ولما فيه من النظافة التي يحبها الله تعالى.

  • فضيلة التَّسَوُّك، وترغيب النبي صلى الله عليه وسلم أمَّته الإكثار منه.
  • الأفضل في التسوُّك استعمال عُوْد شجر الأراك، واستعمل الفرشاة والمعجون يقومُ مقامَه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari