Hadisai

Da yawa mutum daƙal-daƙal abin tunkuɗewa a ƙofofi, da a ce zai yi rantsuwa ga Allah da (Allah) Ya kuɓutar da shi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «رُبَّ أَشْعَثَ مَدْفُوعٍ بِالْأَبْوَابِ لَوْ أَقْسَمَ عَلَى اللهِ لَأَبَرَّهُ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Da yawa mutum daƙal-daƙal abin tunkuɗewa a ƙofofi, da a ce zai yi rantsuwa ga Allah da (Allah) Ya kuɓutar da shi".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai daga cikin mutane wanda gashin kansa a cukurkuɗe yake, ya yi ƙura, ba ya shafa masa mai, kuma ba ya yawan wanke shi, ba shi da wata daraja a wurin mutane dan haka suke ture shi a bakin ƙofofinsu, suna korarsa dan wulaƙanta shi; saidai cewa shi da ace zai yi rantsuwa akan faruwar wani abu da Allah Ya farar da abun, dan girmama shi da amsa roƙonsa, da kuma kiyaye shi daga warware rantsuwarsa, hakan saboda falalarsa da matsayinsa a wurin Allah.

Fa'idoji

  • Allah ba Ya duba zuwa surorin bawa saidai Yana duba zuwa zukata ne da ayyuka.
  • Ya wajaba akan mutum ya kula da aikinsa da tsarkin zuciyarsa sama da kulawarsa ga jiinsa da tufafinsa.
  • Kanƙar dakai ga Allah da miƙa wuya gare shi to hakan sababi ne na amsa addu'a, saboda haka; Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Yana kuɓutar da rantsuwar masu tsoronSa ɓoyayyu.
  • Bayanin tarbiyyar Annabi ga mutane; dan kada sashinsu su wulaƙanta sashi.
Sharhi: العربية

أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أن من الناس مُتَلَبِّد الشَّعَر مُغْبَرَّه، لا يَدهنه ولا يُكثر غسله، لا قدْر له عند الناس فهم يدفعونه عن أبوابهم، ويطردونه عنهم احتقارًا له؛ إلا أنه لو حلف على وقوع شيء أوقعه الله إكرامًا له بإجابة سؤاله، وصيانته من الحنث في يمينه، وذلك لفضله ومنزلته عند الله.

  • الله لا ينظر إلى صورة العبد ولكن ينظر إلى القلوب والأعمال.
  • على الإنسان أن يعتني بعمله وطهارة قلبه أكثر من عنايته بجسمه وملبسه.
  • التواضع لله والتذلل له سبب في إجابة الدعاء، ولذلك؛ فالله سبحانه يَبُرُّ قَسَمَ الأتقياء الأخفياء.
  • بيان التربية النبوية للناس؛ حتى لا يَحتقر بعضهم بعضًا.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari