Hadisai

Allah Ya yi wa mutum rahama mai saukakawa idan zai siyar, kuma idan zai siya, kuma idan zai nemi biyan bashi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن جابر رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «رَحِمَ اللهُ رَجُلًا سَمْحًا إِذَا بَاعَ، وَإِذَا اشْتَرَى، وَإِذَا اقْتَضَى».

Fassara

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah Ya yi wa mutum rahama mai saukakawa idan zai siyar, kuma idan zai siya, kuma idan zai nemi biyan bashi".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da rahama ga dukkanin wanda ya kasance mai sauki mai kyauta a cinikinsa; Ba ya tsanantawa mai saye a farashinta kuma yana mu'amalantarsa da kyakkyawan halaye, Mai sauki mai kyauta idan zai siya, baya tauye mudu kuma ba ya karanta daga kimar haja. Mai sauki mai kyauta idan ya nemi biyan basukansa; ba ya tsanantawa akan talaka da mabukaci, kai yana nemansa da sauki, kuma yana jinkirtawa wanda ke cikin mawuyacin hali.

Fa'idoji

  • Daga manufofin shari'a akwai kiyaye wa akan abinda yake gyara alakoki tsakanin mutane.
  • Kwadaitarwa a aiki da kyawawan halaye a ciki da mu'amaloli tsakanin mutane na siye da siyarwa da makamancin hakan.
Sharhi: العربية

دعا النبي صلى الله عليه وسلم بالرحمة لكل من كان: سهلًا جَوَادًا سَخِيًّا في بيعِه، فلا يُشدِّد على المشتري في سعرها ويعامله بخُلُقٍ حَسَن. سهلًا جوادًا سَخِيًّا إذا اشترى، فلا يَبْخَس ويُقَلِّل من قيمة البِضَاعَة. سهلًا جوادًا سخيًا إذا طَالَبَ بقضاءِ الدُّيون التي له، فلا يُشدِّد على الفقير والمُحتاج، بل يُطالِبه برفق ولُطف، ويُنْظِر المُعسر.

  • مِن مَقاصد الشريعة الحِفاظ على ما يُصلِحُ العلاقاتِ بين الناس.
  • الترغيب في استعمال معالي الأخلاق في المعاملات بين الناس من البيع والشراء ونحو ذلك.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari