Hadisai

Ɗayanku ya ɗauki igiyarsa, ya zo da curin itatuwa a gadan bayansa, ya saida su, Allah Ya kame fuskarsa da su, shi ne yafi alheri gare shi daga ya roƙi mutane sun ba shi ko sun hana shi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ الزُّبَيْرِ بْنِ العَوَّامِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَأَنْ يَأْخُذَ أَحَدُكُمْ حَبْلَهُ، فَيَأْتِيَ بِحُزْمَةِ الحَطَبِ عَلَى ظَهْرِهِ، فَيَبِيعَهَا، فَيَكُفَّ اللَّهُ بِهَا وَجْهَهُ خَيْرٌ لَهُ مِنْ أَنْ يَسْأَلَ النَّاسَ أَعْطَوْهُ أَوْ مَنَعُوهُ».

Fassara

Daga Zubair ɗan Awwam - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ɗayanku ya ɗauki igiyarsa, ya zo da curin itatuwa a gadan bayansa, ya saida su, Allah Ya kame fuskarsa da su, shi ne yafi alheri gare shi daga ya roƙi mutane sun ba shi ko sun hana shi».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum ɗaya daga cikin mutane ya yi aiki kowane irin aiki ne koda zai ɗauki igiya ne, ya tattara itatuwa a gadan bayansa sai ya saida shi ya ci daga gare shi, ko ya yi sadaka da shi ya wadata daga mutane da shi kuma ya kare fuskarsa daga ƙasƙancin roƙo; shi ne ya fiye masa alheri daga ya tambayi mutane su ba shi ko su hanashi, roƙon mutane ƙasƙanci ne, mumini kuwa maɗaukaki ne ba ƙasƙantacce ba ne.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa akan kamewa daga roƙo da kuma tsarkaka daga gare shi.
  • Kwaɗaitarwa akan aiki dan samun arziƙi, koda an jarrabi baligi da ƙaramar sana'a wulaƙantacciya a idanuwan mutane.
  • Yaƙar da Musulunci yake yi wa roƙo; saboda haka ya wajabta yin aiki, ko da mai wahala ne; kamar saran ita ce misali.
  • Roƙo ba ya halatta tare da iko akan aiki da kuma neman arziƙi.
  • Roƙon sarki (shugaba) idan akwai buƙata ya halatta, Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: {Haka kuma babu (laifi) a kan waɗanda idan sun zo maka don ka basu abin hawa sai ka ce: "Bani da abin hawan da zan baku," sai suka juya idanuwansu suna kwararar da hawaye don baƙin cikin ba su sami abinda zasu ciyar ba}. [Al-Taubah: 92].
  • Wanda yake da larurar roƙo da kuma rauni akan neman kuɗi to ya halatta gare shi ya yi roƙo, amma kada ya yi naci, Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: {Basa nacin roƙon mutane} [Al-Baƙara: 273].
  • Nawawi ya ce: A cikinsa akwai: Kwaɗaitarwa akan sadaka, da kuma ci daga aikin hannunsa, da neman halal.
Sharhi: العربية

بيّن النبي صلى الله عليه وسلم أن الواحد من الناس يعمل أي عمل ولو أن يأخذ حبلًا، فيجمع به الحطب على ظهره فيبيعه ويأكل منه، أو يتصدق به ويستغني به عن الناس ويقي وجهه ذلة المسألة؛ خير له من أن يسأل الناس فيعطونه أو يمنعونه، فسؤال الناس مذلة، والمؤمن عزيز غير ذليل.

  • الحَضُّ على التعفف عن المسألة والتنزُّه عنها.
  • الحث على العمل لتحصيل الرزق، ولو امتهن المُكَلَّفُ حِرَفَة بسيطة وحقيرة في نظر الناس.
  • محاربة الإسلام للتَسَوُّل والبطالة؛ ولذلك أوجب السعي والعمل، ولو كان شاقًّا؛ كالاحتطاب مثلًا.
  • لا تحل المسألة مع القُدْرة على العمل وكسب الرزق.
  • سؤال السلطان مع الحاجة جائز، قال الله عز وجل: {وَلَا عَلَى الَّذِينَ إِذَا مَا أَتَوْكَ ‌لِتَحْمِلَهُمْ قُلْتَ لَا أَجِدُ مَا أَحْمِلُكُمْ عَلَيْهِ تَوَلَّوْا وَأَعْيُنُهُمْ تَفِيضُ مِنَ الدَّمْعِ حَزَنًا أَلَّا يَجِدُوا مَا يُنْفِقُونَ} [التوبة: 92].
  • من اضطر إلى السؤال وضعف عن التكسب والاحتطاب فجائز له أن يسأل ولا يُلْحِف ويُلِحّ، قال الله عز وجل: {لَا يَسْأَلُونَ النَّاسَ ‌إِلْحَافًا} [البقرة: 273].
  • قال النووي: فيه: الحث على الصدقة، والأكل من عمل يده، والاكتساب بالمباحات.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari