Hadisai

Mai sakayya bai zama mai sadarwa ba (sada zumunci), saidai mai asadarwa shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «لَيْسَ الْوَاصِلُ بِالْمُكَافِئِ، وَلَكِنِ الْوَاصِلُ الَّذِي إِذَا قُطِعَتْ رَحِمُهُ وَصَلَهَا».

Fassara

Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mai sakayya bai zama mai sadarwa ba (sada zumunci), saidai mai asadarwa shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari, Cewa cikakken mutum a sada zumunci da kuma kyautatawa 'yan uwa shi ne mutumin da yake fuskantar kyakkyawa da kyakkywa, Kai mai sadarwa a hakika a sada zumunci shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi, idan sun munana masa to sai shi ya fuskantarsu da kyautatawa zuwa garesu.

Fa'idoji

  • Sada zumunci abin la'akari a shari'a shi ne ka sadarwa wanda ya yanke maka daga gare su, ka yi afuwa ga wanda ya zalinceka, ka bawa wanda ya haramta maka, bawai sadarwar fuskanta da sakayya ba.
  • Sada zumunci yana kasancewane ta hanyar sadar da abinda zai yiwu na alheri na dukiya da addu'a, da horo da aikin alheri, da kuma hani daga abin ki da makamantansu, da kuma tunkude abinda zai yiwu na sharri daga gare su.
Sharhi: العربية

يُخبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم بأنَّ الإنسانَ الكامِلَ في صِلَةِ الرَّحِم والإحسانِ إلى الأقاربِ ليس هو الشخصُ الذي يُقابِلُ الإحسانَ بالإحسان، بل الواصِلُ حقيقةً الكامِلُ في صلة الرحم هو الذي إذا قُطِعَتْ رَحِمُه وَصَلَها، وإن أساؤوا إليه فإنه يُقابِلُهم بالإحسان إليهم.

  • صِلَةُ الرَّحِم الكاملة شَرْعًا أنْ تَصِلَ مَن قَطَعَك منهم، وتَعفوَ عمَّن ظَلمك، وتعطي من حرمك، وليست صِلَة المقابلة والمجازاة.
  • صلة الرَّحم تكون بالزيارة واللقاء والتواصل، وإيصال ما أمكن من الخير من المال والدعاء والأمر بالعروف والنهي عن المنكر ونحوِها، ودفع ما أمكن من الشر عنهم.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari