Hadisai

Wanda yake son Allah Ya tseratar da shi daga baƙin cikin ranar Alƙiyama, to, ya yaye wa wanda yake cikin wani mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (wani haƙƙi ko nauyin da ya ke kansa)

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبَي قَتَادَةَ رضي الله عنه أنَّهُ طَلَبَ غَرِيمًا لَهُ، فَتَوَارَى عَنْهُ ثُمَّ وَجَدَهُ، فَقَالَ: إِنِّي مُعْسِرٌ، فَقَالَ: آللَّهِ؟ قَالَ: آللَّهِ؟ قَالَ: فَإِنِّي سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «مَنْ سَرَّهُ أَنْ يُنْجِيَهُ اللهُ مِنْ كُرَبِ يَوْمِ الْقِيَامَةِ فَلْيُنَفِّسْ عَنْ مُعْسِرٍ أَوْ يَضَعْ عَنْهُ».

Fassara

Daga Abu Katada - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya nemi wani wanda yake bin sa bashi, sai ya ɓuya daga gare shi, sai ya ce: Lallai ni bani da kuɗi, sai ya ce: (tskaninka da) Allah? ya ce: (tsakanina da) Allah? ya ce: Lallai ni naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wanda yake son Allah Ya tseratar da shi daga baƙin cikin ranar Alƙiyama, to, ya yaye wa wanda yake cikin wani mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (wani haƙƙi ko nauyin da ya ke kansa)".

Sharhi

Abu Katadah alAnsari - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana binciken wani wanda yake binsa bashi wanda yake ɓoye masa, sai ya same shi, sai wanda ake bi bashi ya ce: Lallai ni bani da kuɗi, kuma bani da dukiyar da zan biya bashinka. Sai Abu Katadah - Allah Ya yarda da shi - ya sa ya rantse da Allah cewa shi bashi da dukiya? Sai ya rantse da Allah cewa shi mai gaskiya a abinda yake faɗa. Sai Abu Katadah - Allah Ya yarda da shi - ya ce lallai shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Wanda yake so kuma yake farin ciki Allah Ya tseratar da shi daga baƙin cikin ranar alƙiyama da tsanace-tsanancanta da tsorace-tsoracenta, to ya yayewa wanda yake cikin ƙunci, shi ne cewa ya ƙara (lokaci) ya jinkirta neman bashin, ko ya sarayar da sashin bashin ko ma dukkansa.

Fa'idoji

  • An so saurarawa wanda ke cikin ƙunci zuwa lokacin samun walwala, ko sarayar da bashin daga gare shi gaba ɗayansa ko sashinsa.
  • wanda ya yayewa mumini baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa baƙin cikin ranar alƙiyama, sakamako yana daga jinsin aiki.
  • Ka'ida (ita ce): Lallai cewa farillai sun fi nafilfili, sai dai a wasu lokuta nafila tana zama ta fi farilla, sarayar da bashi daga wanda ke cikin ƙunci nafila ne, kuma yi masa haƙuri da saurare da rashin neman to wannan farilla ne, nafila ta fi farilla a nan.
  • Hadisin yana (bayani) a cikin haƙƙin wanda ke cikin ƙunci, to wannan an yi masa uzuri, amma mai taurin bashi wanda yana da dukiya, to haƙiƙa ya zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce: "Taurin bashin mawadaci zalinci ne".
Sharhi: العربية

كان أبو قتادة الأنصاري رضي الله عنه يبحث عن مَدِيْنٍ له يَخْتَبِئ عنه، فوجده، فقال الغَريم: إني مُعسر، وليس عندي مال لأقضي دينك. فاستحلفه أبو قتادة رضي الله عنه بالله أنه لا مال عنده؟ فحلف بالله أنه صادق فيما يقول. فقال أبو قتادة رضي الله عنه إنه سمع النبي صلى الله عليه وسلم يقول: مَن سرّه وأفرحه أن ينجيَه الله من كُرب يوم القيامة وشدائدها وأهوالها، فلينفِّس عن معسر، بأن يَمُدَّ ويؤخّر المطالبة بالدَّيْن، أو يُسقط بعض الدين أو كله.

  • استحباب إنظار المُعْسر إلى مَيْسرة، أو وضع الدَّين عنه، كله أو بعضه.
  • من نَفَّس عن مؤمن من كُرب الدنيا نَفَّس الله عليه من كُرَب يوم القيامة، والجزاء من جِنس العمل.
  • القاعدة: أن الفرائض أفضل من النوافل، لكن في بعض الأحيان تكون النافلة أفضل من الفريضة، وإسقاط الدين عن المعسر نافلة، والصبر عليه والانتظار وعدم المطالبة هذا فريضة، والنافلة أفضل من الفريضة هنا.
  • الحديث في حق من كان معسرًا، فهذا معذور، أما المُماطِل الذي عنده مال، فقد جاء عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال: "مَطْلُ الغني ظُلْم".

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari