Hadisai

Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad manzon Allah ne

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ البَرَاءِ بْنِ عَازِبٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «المُسْلِمُ إِذَا سُئِلَ فِي القَبْرِ: يَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ»، فَذَلِكَ قَوْلُهُ: {يُثَبِّتُ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا بِالقَوْلِ الثَّابِتِ فِي الحَيَاةِ الدُّنْيَا وَفِي الآخِرَةِ} [إبراهيم: 27].

Fassara

Daga Bara'u ɗan Azib - Allah Ya yarda da shi - manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad manzon Allah ne". to wannan shi ne faɗinSa: {Allah Yana tabbatar wa waɗanda suka yi imani da faɗa tabbatacciya a cikin rayuwar duniya da kuma lahira} [Ibrahim: 27].

Sharhi

Za'a tambayi mumini a cikin ƙabari, sai mala'iku biyu waɗanda aka wakilta da hakan su tambaye shi su ne Munkar da Nakir, kamar yadda ambatansu ya zo a Hadisai masu yawa, sai ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: wannan shi ne tabbatacciyar magana wacce Allah Ya faɗa a cikinta: {Allah Yana tabbatar da wadanda su ka yi imani da magana matabbaciya a rayuwar duniya da kuma a lahira} [Ibrahim: 27].

Fa'idoji

  • Lallai cewa tambayar ƙabari gaskiya ne.
  • Falalar Allah ga bayinSa muminai a duniya da lahira ta hanyar tabbatar da su akan tabbatacciyar magana.
  • Falalar shaidawa da Tauhidi da mutuwa akan hakan.
  • Tabbatar war Allah ga mumini a duniya da tabbata akan imani, da shiga hanya madaidaiciya, a lokacin mutuwa kuma da mutuwa akan Tauhidi, a ƙabari a lokacin tambayar mala'iku biyu.
Sharhi: العربية

يُسألُ المؤمنُ في القبر، فيسأله الملكان الموكَّلان بذلك وهما منكر ونكير، كما جاء تسميتهما في عدة أحاديث، فيشهد أن لا إله إلا الله وأن محمدًا رسول الله، قال النبي صلى الله عليه وسلم هذا هو القول الثابت الذي قال الله فيه: {يُثَبِّتُ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا بِالْقَوْلِ الثَّابِتِ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَفِي الْآخِرَةِ} [إبراهيم: 27].

  • أنَّ سؤال القبر حق.
  • فضل الله على عباده المؤمنين في الدنيا والآخرة بتثبيتهم على القول الثابت.
  • فضل شهادة التوحيد والموت عليها.
  • تثبيت الله للمؤمن في الدنيا بالثبات على الإيمان، وسلوك الصراط المستقيم، وعند الموت بالموت على التوحيد، وفي القبر عند سؤال الملكين.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari