Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ لِي عَنْ أُمَّتِي الخَطَأَ وَالنِّسْيَانَ وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ».
Fassara
Daga ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Lallai Allah Ya yi wa al'ummarsa rangwame akan halaye uku: Na farko: Kuskure, shi ne abin da ya bijiro daga garesu ba tare da ganganci ba, kuma shi ne musulmi ya nufi wani abu da aikinsa sai aikin na sa ya dace da abin da bai yi nufi ba. Na biyu: Mantuwa, shi ne musulmi ya zama mai tina wani abu, saidai a lokacin aikata shi sai ya manta shi, to babu zunubi a kan hakan. Na uku: Tilastawa, za’a iya tilastawa bawa yin wani aikin da bai yi nufinsa ba tare da rashin ikonsa akan tunkuɗe tilastawar, a wannan lokacin zunubi ko ƙunci ba zai faɗa kansa ba. Tare da lura da cewa matashiyar hadisin a abin da ke tsakanin bawa da Ubangijinsa ne, a kan aikata abinda aka haramta, amma barin abin da aka yi umarni akan mantuwa to ba zai saraya ba, amma da ace wani laifi zai faru akan aikinsa to ba zai sarayar da wani haƙƙi na abin halitta ba, kamar yadda da ace zai yi kisa akan kuskure, ko ya lalata wata mota akan kuskure to wajibi ne ya biya.
Fa'idoji
- Yalwar rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - da tausasawarSa ga bayinSa inda ya ɗauke musu zunubi, idan saɓo ya bijiro daga garesu akan waɗan nan halayen uku.
- Falalar Allah ga Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma al'ummarsa.
- Ɗauke zunubi ba ya nufin ɗauke hukunci ko biya, misali wanda ya manta alwala, sai ya yi sallah yana mai zatan cewa shi yana da tsarki, to babu laifi a kansa da hakan, sai dai wajibi ne akansa ya yi alwala kuma ya sake sallar.
- Babu makawa a cikin ɗauke laifi da tilastawa daga samuwar sharuɗɗa, misali mai tilastawar ya zama mai iko akan zartar da abin da ya yi barazana da shi.
Sharhi: العربية
يخبر النبي صلى الله عليه وسلم : أن الله عفا عن أمته في ثلاثة أحوال: الأولى: الخطأ، وهو ما صدر منهم دون تعمد، وهو أن يقصد المسلم بفعله شيئًا، فيصادف فعله غير ما قصده. والثانية: النسيان، وهو أن يكون المسلم متذكرًا لشيء، ولكن ينساه عند الفعل، فلا إثم في ذلك أيضًا. والثالثة: الإكراه ، فقد يُكره العبد على فعل شيء لا يريده مع عدم قدرته على دفع الإكراه، وحينئذٍ لا يقع عليه الإثم أو الحرج. مع ملاحظة أن موضوع الحديث فيما بين العبد وربه في فعل المحظور، فأما ترك المأمور نسيانًا فلا يسقط، وأما لو ترتب على فعله ذلك جناية فلا يسقط حق المخلوق، كما لو قتل خطًأ، فعليه الدية، أو أتلف سيارة خطأ فعليه الضمان.
- سعة رحمة الله -عزّ وجل- ولطفه بعباده حيث رفع عنهم الإثم إذا صدرت منهم المعصية على هذه الأحوال الثلاثة.
- فضل الله على النبي محمد صلى الله عليه وسلم وأمته.
- رفعُ الإثم لا يعني رفع الحكم أو الضمان، فمثلًا من نسي الوضوء، وصلى ظانًّا أنه متطهر، فلا إثم عليه بذلك، ولكن عليه الوضوء وإعادة الصلاة.
- لا بد في رفع الإثم بالإكراه من توفر الشروط، مثل أن يكون المكِره قادرًا على تنفيذ ما هدد به.