Hadisai

Ku barni a abinda na bar muku, kaɗai waɗanda ke gabaninku sun halaka ne da tambayarsu da kuma saɓawarsu ga annabawansu

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «دَعُونِي مَا تَرَكْتُكُمْ، إِنَّمَا هَلَكَ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ بِسُؤَالِهِمْ وَاخْتِلَافِهِمْ عَلَى أَنْبِيَائِهِمْ، فَإِذَا نَهَيْتُكُمْ عَنْ شَيْءٍ فَاجْتَنِبُوهُ، وَإِذَا أَمَرْتُكُمْ بِأَمْرٍ فَأْتُوا مِنْهُ مَا اسْتَطَعْتُمْ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku barni a abinda na bar muku, kaɗai waɗanda ke gabaninku sun halaka ne da tambayarsu da kuma saɓawarsu ga annabawansu, idan na haneku daga wani abu to ku nuisance shi, idan na umarceku da wani abu to ku zo da shi daidai ikonku".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa hukunce-hukuncen shari'a sun rabu gida uku: Abinda aka yi shiru akan sa, da abubuwan da aka hana, da abubuwan da aka yi umarni. Amma na farko: Shi ne wanda shari'a ta yi shiru akansa, ta yadda babu wani hukunci, sai kuma cewa asali a abubuwa rashin wajabci; amma a zamaninsa - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - to barin tambaya ga wani abu da bai afku ba yana wajaba dan tsoron kada a wajabta ko haramci ya sauka a kan shi, domin Allah Ya bar su ne dan rahama ga bayi. Amma bayan rasuwarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan tambayar ta kasance ta fuskar neman fatawa ce ko koyarwa ga abinda ake buƙatuwa a gare shi na al'amarin addini to ya halatta, kai an yi umarni da shi ma, idan kuma ta fuskar ta'annututi ce da ɗorawa kai to shi ne abinda ake nufi da barin tambaya daga gare shi a cikin wannan Hadisin; hakan domin cewa shi zai iya kaiwa zuwa kwatankwacin abinda ya afku ga Banu Isra'ila, dan an umarce su su yanka saniya da sun yanka kowacce irin saniya da sun aikata umarni, sai dai su sun tsananta sai aka tsananta musu. Na biyu: Abubuwan da aka hana; su ne: Abinda ake bawa wanda ya bar shi lada, kuma ana yi wa wanda ya aikata shi uƙuba, to nisantarsu yana wajaba. Na uku: Abubuwan da aka umarta; shi ne abinda ake bawa wanda ya aikata shi lada, kuma ana yi wa wanda ya bar shi uƙuba, to yana wajaba ya aikata shi gwargwadan iko.

Fa'idoji

  • Abinda ya kamata a shagalta da mafi muhimmancin abinda ake buƙatuwa zuwa gare shi, da barin abin da ba'a buƙatuwa zuwa gare shi a wannan lokaci, da barin shagaltuwa da tambaya daga abinda bai afku ba.
  • Haramcin tambayar da wataƙila ta kai zuwa ƙulle mas'aloli, da buɗe ƙofar shubuhohi masu kaiwa zuwa yawan saɓani.
  • Umarni da barin dukkan abinda aka hana; domin babu wata wahala a barinsu, saboda haka hanin da aka ya yi zama gamamme.
  • Umarni da aikata abinda aka yi umarni da shi gwargwadan iko; domin zai iya lizimtar da wahala ko a gajiya a aikata shi; saboda haka umarni da shi ya zama akan gwargwadan iko.
  • Hani akan yawan tambaya, haƙiƙa malamai sun raba tambaya gida biyu: Ta ɗayansu: Wadda take kasancewa ta fuskar koyarwa ga abinda ake buƙatuwa zuwa gare shi na al'amarin addini, to wannan an yi umarni da ita, daga wannan nau'in tambayoyin sahabbai suke. Na biyu: Wadda ta kasance ta fuskar ta'annuti da ɗorawa kai to wannan ita ce wacce aka hana.
  • Gargaɗin wannan al'ummar daga saɓawa annabinta, kamar yadda ya afku a cikin al’ummun da suka gabata.
  • Yawan tambaya yana daga abinda ba'a buƙatuwa zuwa gare shi, kuma saɓawa annabawa sababi ne na halaka, musamman ma a cikin al'amuran da kaiwa gare su ba zai yi wu ba, misalin: Mas'alolin gaibun da babu wanda ya sansu sai Allah, da halayen ranar Alkiyama.
  • Hana yin tambaya a mas'aloli masu tsanani, Auza'i ya ce: Lallai Allah idan Ya yi nufin haramtawa bawanSa albarkar ilimi sai Ya jefawa harshensa galaɗi mai yawa, haƙiƙa na gansu (sune) mafi ƙarancin mutane a ilimi. Ibnu Wahab ya ce: Na ji Malik yana cewa: Gaddama a cikin ilimi tana tafiyar da hasken ilimi daga zuciyar mutum.
Sharhi: العربية

ذَكَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنّ الأحكام الشرعية على أقسام ثلاثة: ما سُكت عنه، ونواهي، وأوامر. فأما الأول: وهو ما سَكَتَ الشرعُ عنه: حيث لا حُكْم، وأنّ الأصل في الأشياء عدم الوجوب؛ فأما في عهده صلى الله عليه وسلم فيجب تركُ السؤال عن شيء لم يقع خشية أن ينزل به وجوب أو تحريم، فإن الله تركَها رحمة بالعباد، وأما بعد موته صلى الله عليه وسلم فإن كان السؤال على وجه الاستفتاء أو التعليم لما يحتاج إليه من أمر الدين فهو جائز بل مأمور به، وإن كان على وجه التَّعَنُّت والتكلُّف فهو المراد بترك السؤال عنه في هذا الحديث؛ وذلك لأنه قد يُفضي إلى مثل ما وقع لبني إسرائيل، إذ أُمروا أن يذبحوا بقرة فلو ذبحوا أيَّ بقرة لامتثلوا، ولكنهم شددوا فشُدِّد عليهم. الثاني: النواهي؛ وهي: ما يثاب تاركه، ويعاقب فاعله، فيجب اجتنابُها كلها. الثالث: الأوامر؛ وهو ما يثاب فاعله، ويعاقب تاركه، فيجب أن يفعل منه قدر الاستطاعة.

  • ينبغي الانشغال بالأهم المُحتاج إليه، وترك ما لا يحتاج إليه في الحال، وعدم الاشتغال بالسؤال عما لم يقع.
  • حرمة السؤال الذي ربما أوصل إلى تعقيد المسائل، وفتح باب الشبهات المفضية إلى كثرة الاختلاف.
  • الأمر بترك كل المنهيات؛ لأنه لا مشقة في تركها، ولذلك كان النهي عنه عامًّا.
  • الأمر بفعل المأمور به على قدر الاستطاعة؛ لأنه قد يلزم منه مشقة أو يعجز عنه؛ ولذا كان الأمر به على قدر الاستطاعة.
  • النهي عن كثرة السؤال، قد قسم العلماء السؤال إلى قسمين: أحدهما: ما كان على وجه التعليم لما يحتاج إليه من أمر الدين، فهذا مأمور به ومن هذا النوع أسئلة الصحابة، والثاني: ما كان على وجه التعنت والتكلف وهذا هو المنهي عنه.
  • تحذير هذه الأمة من مخالفة نبيها، كما وقع في الأمم التي قبلها.
  • كثرة السؤال مما لا يُحتاج إليه والاختلاف على الأنبياء سببٌ للهلاك، ولا سيّما في الأمور التي لا يمكن الوصول إليها، مثل: مسائل الغيب التي لا يعلمها إلا الله، وأحوال يوم القيامة.
  • النهي عن السؤال في شِداد المسائل، قال الأوزاعي: إن الله إذا أراد أن يحرم عبده بركة العلم ألقى على لسانه المغاليط، فلقد رأيتهم أقلَّ الناس علمًا، وقال ابن وهب: سمعت مالكًا يقول: المِراء في العلم يذهب بنور العلم من قلب الرجل.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari