Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي ذَرٍّ، جُنْدُبِ بْنِ جُنَادَةَ، وَأَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ، مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «اتَّقِ اللَّهَ حَيْثُمَا كُنْت، وَأَتْبِعْ السَّيِّئَةَ الْحَسَنَةَ تَمْحُهَا، وَخَالِقْ النَّاسَ بِخُلُقٍ حَسَنٍ».
Fassara
Daga Abu Zarr, Jundubu Ibnu Junadata, da Abu Abdurrahman, Mu'azu Ibnu Jabal - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ka ji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka bi munanan (ayyuka) da kyakkyawa zai shafe shi, ka ɗabi'anci mutane da kyawawan ɗabi'u».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da al'anura uku: Na farko: Tsoron Allah hakan ta hanyar aikata wajibai, da barin abubuwan da aka haramta, a kowane guri da zamani da kuma hali, a ɓoye da bayyane, haka a lokacin lafiya da bala'i da wanin haka. Na biyu: Idan ka afka cikin mummunan (laifi), to ka aikata kyakkawan (aiki) a bayan shi, kamar sallah da azimi da sadaka da aikin alheri da sada zumunci da wanin haka, domin cewa hakan zai shafe mummuna. Na uku: Ka yi wa mutane mu'amala da kyawawan ɗabi'u, na murmushi a fuskokinsu, da tausasawa da aikata alheri da kamewa daga cutarwa.
Fa'idoji
- Falalar Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga bayi a kan rahamarSa da gafararSa da kuma rangwaminSa.
- Hadisin ya ƙunshi haƙƙoƙi uku: Haƙƙin Allah da taƙawa, da haƙƙin rai ta hanyar aikata kyawawan halaye bayan munanan (halaye), da kuma haƙƙin mu'amala ta hanyar aikata kyawawan ɗabi'u.
- Kwaɗaitarwa akan aikata kyawawan (halaye) bayan munanan (halaye), da kyawawan ɗabi'u, na ɗabi'un tsoron Allah, kawai an ambace su da ambato ne dan buƙatuwa zuwa ga bayaninsu.
Sharhi: العربية
يأمر النبي صلى الله عليه وسلم بثلاثة أمور: الأول: تقوى الله وذلك بفعل الواجبات، وترك المحرمات، في كل مكان وزمان وحال، في السر والعلانية، وفي العافية والبلاء وغير ذلك. الثاني: إذا وقعت في سيئة، فافعل بعدها حسنة من صلاة وصدقة وبر وصلة وتوبة وغير ذلك، فإن ذلك يمحو السيئة. الثالث: عامل الناس بأخلاق حسنة، مِنْ تبسم في وجوههم، ورفق ولين وبذل معروف وكف أذى.
- فضل الله عزّ وجل على العباد في رحمته ومغفرته وعفوه.
- اشتمل الحديث على الحقوق الثالثة: حق الله بالتقوى، وحق النفس بفعل الحسنات بعد السيئات، وحق الناس بالمعاملة بالأخلاق الحسنة.
- الترغيب في فعل الحسنات بعد السيئات، وحسن الخلق من خصال التقوى، وإنما أفرد بالذكر للحاجة إلى بيانها.