Hadisai

Addini nasiha ne

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن تميم الداري رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «الدِّينُ النَّصِيحَةُ» قُلْنَا: لِمَنْ؟ قَالَ: «لِلهِ وَلِكِتَابِهِ وَلِرَسُولِهِ وَلِأَئِمَّةِ الْمُسْلِمِينَ وَعَامَّتِهِمْ».

Fassara

Daga Tamim al-Dari - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Addini nasiha ne" Muka ce; ga wa? Ya ce; "Ga Allah da littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin musulmai da dukkaninsu".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa addini a tsaye yake a kan ikhlasi da gaskiya, har a yi kamar yadda Allah Ya wajabta, cikakke ba tare da tawaya ko algus ba. Sai aka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Ga wa nasihar za ta kasance? sai ya ce: Na farko: Nasiha ga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya daukaka -: ta hanyar tsarkake aiki gare shi, da rashin haɗa wani da Shi, kuma mu yi imani da Rububiyyarsa da Uluhiyyarsa da sunayensa da siffofinsa, da girmama al'amarinsa, da kira zuwa imani da Shi. Na biyu: Nasiha ga littafinsa shi ne Alƙur'ani mai girma: Shi ne cewa mu ƙudirce cewa shi zancensa ne, kuma ƙarshen littattafansa, kuma cewa shi mai shafewa ne ga dukkanin shari'o'i kafinsa, mu girmamashi, mu karantashi haƙiƙanin karantashi, mu yi aiki da muhkam ɗinsa, mu miƙa wuya ga abubuwa masu kamanceceniya a cikinsa, kuma mu kore tawilin masu karkacewa gareshi, mu wa'azantu da wa'azozinsa, da yaɗa ilimummukansa, da kira zuwa gareshi. Na uku: Nasiha ga manzonsa (Annabi) muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Shi ne mu kudire cewa shi ne karshen manzanni, mu gasgatashi a cikin abin da ya zo da shi, mu kamanta umarninsa, mu nisanci haninsa, kuma kada mu bautawa Allah da komai sai abin da ya zo da shi, mu girmama haƙƙinsa, mu girmamashi, mu yaɗa da'awarsa, mu yaɗa shari'arsa, kuma mu kore tuhuma daga gareshi. Na hudu: Nasiha ga shugabannin musulmai: Ta hanyar taimakonsu a kan gaskiya, da rashin jayayya da su a al'amari, da ji da biyayya garesu a cikin biyayya ga Allah. Na biyar: Nasiha ga musulami: Ta hanyar kyautatawa zuwa garesu da kiransu, da kame cuta daga garesu, da son alheri garesu, da taimakekeniya tare da su a kan biyayya da tsoron Allah.

Fa'idoji

  • Umarni da nasiha ga kowa da kowa.
  • Girman matsayin nasiha a addini.
  • Addini ya ƙunshi ƙudirce-ƙudirce da maganganu da kuma ayyuka.
  • Yana daga cikin nasiha tsarkake zuciya daga algus ga wanda aka yi wa nasihar da kuma nufin alheri gareshi.
  • Kyakkyawar koyarwar Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da yake ambaton abu a dunkule sannan ya yi shi dalla-dalla.
  • Farawa da mafi muhimmanci sannan mai bi masa, yayin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fara da nasiha ga Allah, sannan littafinsa, sannan manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sannan ga shugabannin musulmai, sannan kowa da kowansu.
Sharhi: العربية

أَخبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم بأنَّ الدين قائمٌ على الإخلاص والصدق، حتى يؤدَّى كما أوجب الله، كاملًا دون تقصير أو غش. فقيل للنبي صلى الله عليه وسلم: لمن تكون النصيحة؟ فقال: أولًا: النصيحة لله سبحانه وتعالى: بإخلاص العمل له، وعدم الإشراك به، وأن نؤمن بربوبيته وألوهيته وأسمائه وصفاته، وتعظيم أمره، والدعوة إلى الإيمان به. ثانيًا: النصيحة لكتابه وهو القرآن الكريم: بأن نعتقد أنه كلامُه، وآخِرُ كتبِه، وأنه ناسخ لجميع الشرائع قبله، ونعظِّمه، ونتلوه حق تلاوته، ونعمل بمُحْكَمِه، والتسليم بمتشابهه، ونَذُبُّ عن تأويل المُحرِّفين له، ونعتبر بمواعظه، ونشر علومه، والدعوة إليه. ثالثًا: النصيحة لرسوله محمد صلى الله عليه وسلم: بأن نعتقدَ أنه آخِرُ الرسل، ونصدِّقَه فيما جاء به، ونَمتَثِلَ أمرَه، ونجتنبَ نهيَه، وأن لا نتعبدَ لله إلا بما جاء به، ونُعظِّمَ حقَّه، ونوقرَه، ونَبُثَّ دعوته، ونَنشُرَ شريعتَه، ونَنفيَ التُّهَمَ عنه. رابعًا: النصيحة لأئمة المسلمين: بمعاونتهم على الحق، وعدم منازعتهم الأمر، والسمع والطاعة لهم في طاعة الله. خامسًا: النصيحة للمسلمين: بالإحسان إليهم ودعوتهم، وكَفِّ الأذى عنهم، ومحبة الخير لهم، والتعاون معهم على البر والتقوى.

  • الأمر بالنصيحة للجميع.
  • عِظَم منزلة النصيحة من الدين.
  • اشتمال الدين على الاعتقادات والأقوال والأعمال.
  • من النصيحة تصفية النفس من الغش للمنصوح له وإرادة الخير له.
  • حسن تعليم الرسول صلى الله عليه وسلم حيث يذكر الشيء مُجملًا ثم يُفصّله.
  • البداءة بالأهم فالأهم، حيث بدأ النبي صلى الله عليه وسلم بالنصيحة لله، ثم لكتابه، ثم لرسوله صلى الله عليه وسلم ثم لأئمة المسلمين، ثم عامتهم.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari