Hadisai

Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «مَنْ صَامَ يَوْمًا فِي سَبِيلِ اللهِ بَاعَدَ اللهُ وَجْهَهُ عَنِ النَّارِ سَبْعِينَ خَرِيفًا».

Fassara

Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya azumci wani yini a yaƙi, an ce a yaƙi da waninsa yana mai ikhlasi ga Allah dan neman sakamako da lada daga Allah; to lallai Allah da falalarsa Zai nisantar da tsakaninsa da tsakanin wuta (tsawon) shekara saba'in.

Fa'idoji

  • AlNawawi ya ce: Falalar azimi a tafarkin Allah, shi abin ɗauka ne akan wanda ba ya cutuwa da yin azumin, kuma ba zai salwantar da wani haƙƙi idan ya yi azumin, kuma yaƙinsa ko waninsa ba zai bata muhimman yaƙi da shi ba.
  • Zaburarwa da kwaɗaitarwa akan azimin nafila.
  • Wajabcin ikhlasi da neman yardar Allah, kuma kada ya yi azimi dan riya ko jiyarwa ko dan wasu manufofin daban.
  • Sindi ya ce: Faɗinsa (A tafarkin Allah), za'a iya ɗaukar cewa abin nufi mujarradin gyara niyya, kuma za'a iya ɗaukar cewa abin nufi da shi cewa shi ya yi azimi a halin kasancewarsa mai yaƙi, na biyun shi ne abin gaggawar (manufa).
  • Ibnu Hajar ya ce: Faɗinsa: (Kharif saba'in) Kharif wani lokaci ne sananne a shekara, abin nufi da shi a nan shekarar (gaba ɗayanta), kuma keɓance Kharif (Kaka) da ambato banda ragowar lokutan - zafi da sanyi da damina -; domin cewa Kharif (Kaka) ya fi ragowar lokutan kyau domin kasancewarsa ana tsinkar 'ya'yan itatuwa a cikinsa.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلّم أنَّ مَن صام يومًا في الجهاد، وقيل في الجهاد وغيره مُخلِصًا لله ابتغاء الثواب والأجر من الله؛ فإنّ الله بفضله يُبَاعِد بينه وبين النار سبعين سنة.

  • قال النووي: فضيلة الصيام في سبيل الله، وهو محمول على مَن لا يَتضرر به، ولا يُفوِّت به حقًّا، ولا يَختلُّ به قتالُه ولا غيره من مُهِمَّات غزوِه.
  • الحث والترغيب على صيام التطوع.
  • وجوب الإخلاص وابتغاء مرضاة الله، ولا يصوم رياء ولا سمعة ولا لمقاصد أخرى.
  • قال السندي: قوله (في سبيل الله)، يحتمل أن المراد مجرد إصلاح النية، ويحتمل أن المراد به أنه صام حال كونه غازيًا، والثاني هو المتبادر.
  • قال ابن حجر: قوله: (سبعين خريفًا) الخريف زمان معلوم من السَّنَة، والمراد به هنا العام، وتخصيص الخريف بالذكر دون بقية الفصول -الصيف والشتاء والربيع-؛ لأن الخريف أزكى الفصول لكونه يُجْنَى فيه الثمار.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari