Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَقَدَّمُوا رَمَضَانَ بِصَوْمِ يَوْمٍ وَلَا يَوْمَيْنِ إِلَّا رَجُلٌ كَانَ يَصُومُ صَوْمًا فَلْيَصُمْهُ».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku gabaci Ramadan da azimin yini ko yini biyu sai dai mutumin da ya kasance yana yin wani azimi to ya azimce shi".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya yi azimi kafin Ramadan da yini ɗaya ko yini biyu akan niyyar lissafa shi a (watan) Ramadan; domin wajabacin azimin Ramadan an rataya shi ne da ganin jinjirin wata, babu buƙatuwa ga ɗorawa kai, sai dai wani wanda ya kasance yana yin wani azimin da ya sabayi kamar azimin yini da fashin yini (irin na annabi Dawud), ko ranar litinin ko alhamis sai ya yi daidai da shi to ya azimce shi; wannan bai zamo daga tarbar Ramadan a wani abu ba, an riskar da hakan abinda ya kasance azimi ne na wajibi kamar ramuwa da bakance.
Fa'idoji
- Hani daga ɗorawa kai (wahala), da wajabcin kiyayewa akan ibada kamar yadda aka shara'antata ba tare da ƙari ko ragi ba.
- Daga hikimar hakan - Allah ne Mafi sani - banbance farillan ibadu daga nafilfilinsu, da yi wa Ramadan tanadi da nishaɗi da kwaɗayi, kuma dan azimi ya zama alamar wannan watan mai falala abin banbancewa da shi.
Sharhi: العربية
نَهَى النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنْ يصوم المسلم قبل رمضان بيوم أو يومين على نية الاحتياط لرمضان؛ لأنّ وجوبَ صيام رمضان عُلِّق برؤية الهلال، ولا حاجة للتكلُّف، إلا أحد كان يصوم صومًا اعتاد عليه كصوم يوم وفطر يوم، أو يوم الاثنين أو الخميس فصادفه فليصمْه؛ وليس ذلك من استقبال رمضان في شيء، ويلحق بذلك ما كان صيامًا واجبًا كالقضاء والنَّذْر.
- النهي عن التكلف، ووجوب المحافظة على العبادة كما شُرعت بدون زيادة أو نقص.
- من حكمة ذلك -والله أعلم- تمييز فرائض العبادات من نوافلها، والاستعداد لرمضان بنشاط ورغبة، وليكون الصيام شعار ذلك الشهر الفاضل المميز به.