Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ عَامَ الفَتْحِ وَهُوَ بِمَكَّةَ: «إِنَّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ حَرَّمَ بَيْعَ الخَمْرِ، وَالمَيْتَةِ وَالخِنْزِيرِ وَالأَصْنَامِ»، فَقِيلَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَرَأَيْتَ شُحُومَ المَيْتَةِ، فَإِنَّهَا يُطْلَى بِهَا السُّفُنُ، وَيُدْهَنُ بِهَا الجُلُودُ، وَيَسْتَصْبِحُ بِهَا النَّاسُ؟ فَقَالَ: «لاَ، هُوَ حَرَامٌ»، ثُمَّ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عِنْدَ ذَلِكَ: «قَاتَلَ اللَّهُ اليَهُودَ إِنَّ اللَّهَ لَمَّا حَرَّمَ شُحُومَهَا جَمَلُوهُ، ثُمَّ بَاعُوهُ، فَأَكَلُوا ثَمَنَهُ».
Fassara
Daga Jabir ɗan Abdullah - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, yana faɗa a shekarar buɗe Makka alhali shi yana Makkah: "Lallai Allah da manzonSa - sun haramta saida giya, da mushe da alade da gumaka", sai aka ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin kitsen mushe, cewa su ana shafe jiragen ruwa da su, kuma ana shafe fatu da su, kuma mutane suna fitila da su? sai ya ce: "A'a, shi haramun ne", sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce a wannan lokacin: "Allah Ya la'anci Yahudawa lallai Allah yayin da Ya haramta kitsensu sai suka gyara shi, sannan suka saida shi, sai suka ci kuɗinsa".
Sharhi
Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda ad shi - ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa a shekarar da aka buɗe Makka, alhali shi yana Makka: Lallai Allah da ManzonSa sun haramta saida giya da mushe da alade da gumaka, sai aka ce : Ya Manzon Allah, shin ya halatta mu saida kitsen mushe? domin su ana shafe jiragen ruwa da su, kuma shafe fatu da su, kuma mutane suna kunna fitilunsu da su, sai ya ce: A'a, saida su haramun ne, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce a wannan lokacin: Allah Ya halakar da Yahudawa kuma Ya la'ancesu; lallai Allah yayin da Ya haramta musu kitsen dabbobi sai suka narkasu, sannan suka saida mansu suka ci kuɗinsa.
Fa'idoji
- AlNawawi ya ce: Mushe da giya da alade: Musulmai sun haɗu akan haramcin saida kowanne ɗaya daga cikinsu.
- Alƙali ya ce: Wannan Hadisin ya ƙunshi cewa abinda cinsa da anfani da shi ba ya halatta to saida shi ba ya halatta, kuma cin kuɗinsa ba ya halatta, kamar yadda yake a cikin kitsen da aka anbata a cikin Hadisin.
- Ibnu Hajar ya ce: Siyaƙin mai alamtarwa ne da ƙarfin dalili akan abinda mafi yawa suka yi tawilinsa cewa abin nufi da faɗinsa: "Shi haramun ne'’, siyarwa ba anfani ba.
- Dukkan dabarar da za'a kai ga halatta haram da ita to ita ɓatacciya ce.
- Nawawi ya ce: Malamai su ce: A cikin gamewar haramcin saida mushe cewa saida jikin kafiri yana haramta idan mun kashe shi, kuma kafirai suka nemi siyansa, ko bada canjinsa daga gare shi, haƙiƙa ya zo a cikin Hadisi: Cewa Naufal ɗan Abdulahi AlMakhzumi musulmai sun kashe shi ranar Khandaƙ, sai kafirai suka bada dirhami dubu goma ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga jikinsa bai karɓa ba, ya ba su shi.
Sharhi: العربية
سَمِعَ جابرُ بن عبدِ الله رضي الله عنهما النبيَّ صلى الله عليه وسلم يقول عامَ الفَتْح، وهو بمكة: إن الله ورسوله حَرَّم بيعَ الخمر والميتة والخنزير والأصنام، فقيل: يا رسول الله، هل يَحِلُّ أنْ نبيعَ شحومَ الميتة؟ لأنها يُطْلَى بها السُّفُن، ويُدهَن بها الجلود، ويُوقِد بها الناسُ سُرُجَهم، فقال: لا، بيعُها حرام، ثم قال صلى الله عليه وسلم عند ذلك: أَهْلَكَ اللهُ اليهودَ ولعنَهم؛ إن الله لمّا حرّم عليهم شحوم البهائم أذابوها، ثم باعوا دُهنَها فأكلوا ثَمَنَه.
- قال النووي: الميتة والخمر والخنزير: أجمع المسلمون على تحريم بيع كلِّ واحدٍ منها.
- قال القاضي: تَضَمَّنَ هذا الحديث أن ما لا يَحِلُّ أكلُه والانتفاع به لا يجوز بيعه، ولا يحل أكل ثمنه، كما في الشحوم المذكورة في الحديث.
- قال ابن حجر: وسياقُه مُشْعِرٌ بِقُوَّة ما أوّله الأكثر أن المراد بقوله: "هو حرام" البيع لا الانتفاع.
- كلُّ حِيْلةٍ يُتَوَصَّل بها إلى تحليل مُحَرَّمٍ فهي باطلة.
- قال النووي: قال العلماء: وفي عموم تحريم بيع الميتة أنه يحرم بيع جُثَّة الكافر إذا قتلناه وطَلَبَ الكفّارُ شراءَه، أو دَفْع عِوَضٍ عنه، وقد جاء في الحديث: أنّ نوفل بن عبد الله المخزومي قتله المسلمون يوم الخندق، فبذل الكفار في جسده عشرة آلاف درهم للنبي صلى الله عليه وسلم فلم يأخذْها، ودَفَعَه إليهم.